Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kare sauran zakunan daji da suka rage a Afirka
Mai daukar hoto na Burtaniya George Logan ya tattaro hotuna masu kyaun asali da nuna rayuwar yau da kullum na zakunan Afrika.
Logan ya shafe shekaru 10 yana daukar hotunan zakuna a kasashen Kenya da Ethiopia, Zambia, da Malawi, da Botswana, da Namibia da kuma Afirka ta Kudu.
Daya daga cikin hotunan da ya fi so cikin wadanda ya dauka shi ne na wannan zakin da kuke gani a sama, da ake kira Scarface.
"Jarumi ne na kwarai da ya rage, kuma ya gudanar da rayuwarsa kamar yadda ya kamata a ce zakin dawa ya yi, ba a tsare a gidan ajiyar namun daji ba, ko kuma a hannun masu wasa da dabbobi, ko kuma mutuwa a hannun mafarauta,'' a cewarsa.
Littafin mai daukar hoton na, ''Lion: Pride Before The Fall'', ya kunshi zakuna a muhallinsu na ainihi, hade da kayatattun hotunan da ke nuna yadda rayuwar zakunan dawa ke tafiya a yanzu.
"Zaki wata alama ce ta nuna namun dajin Afirka, amma duk da haka kasa da 20,000 suka rage a nahiyar, daga kiyasin da aka yin na adadin 100,000 a shekaru 50 da suka gabata," in ji Logan.
"A kiyasin koma bayan da aka samu a yanzu, zakuna za su bace daga doron kasa nan da tsakiyar wannan karnin."
Ribar da aka samu daga littafin za ta tafi ne wajen ayyukan raya namun dajin da kungiyar bayar da tallafi ta Born Free.
'Yar wasan kwaikwayo kuma mai fafutikar kare gandun daji Virginia McKenna, kuma daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar ta bayyana a yabon littafin cewa: "Babu wani, a ra'ayina da ya iya samu da kuma gano bangarori na halayyar zakuna kamar George Logan."
Logan ya harhada hotunan da ne ta hanyar hada kai da wasu kungiyoyin fasaha da suka ba shi shawarwari kan yadda nuna hadurran da zakoki ke fuskanta a cikin daji.
Ga kadan daga cikin hotunan, dauke da bayanai daga Logan:
Zaki zai yi barci da dare
"Akasarin mutane na mamakin ganin zaki cikin daji.
"Danna hancin bindiga kadan, cikin lokaci daya maharbi mai neman suna ya kawar da wannan abin mamaki da kuma kyau.
"A kan me?"
Kwana nawa ya rage su zama tarihi?
"Raguwar yawan adadin zakunan ya ta'alakka ne da mummunar al'adarmu ta lalatawa da gallazawa da kuma rashin adalci ga namun daji.
"Baya ga bukatar farfadon da tunaninmu , yana da kyau yin la'akari da duk abinda muka iya rasawa.
"Wane irin kallo za a yi mana a matsayin halittu, idan muka gaza kare duka muhimman halittun?"
Bai kamata yawon bude ido ya kasance na harbin neman suna ba
"A Burtaniya, mun saba da girmama zakuna.
"Ba su kasance a cikin daji na yankunan Birtaniya kamar su Ireland ta Arewa, da Ingila, da Scotland da kuma Wales ba, tun zamanin kaka da kakanni tsakanin shekaru dari da shekaru miliyan daya da dubu dari takwas da suka gabata, amma duk da haka muna da dangantaka da su.
"Akwai hoton zakuna a jikin tutocinmu, da tufafin wasanninmu har ma da kudinmu.
"A duk inda ka duba za ka ka zakuna…baya ga a inda aka saba ganinsu. A cikin daji.''
Gagarumin wasa
"Duka wadannan barazana da zakuna ke fuskanta, kisan da ke yi musu don nuna bajinta da neman suna shi ne mafi muni.
"Na fahimci dalilan da suka sa ake rasa muhallan, kana dalilan da suka sa makiyaye ke son kare dabbobinsu, amma kuma dabi'ar biyan har dala dubu hamsin $50,000 a harbe zaki, ta hanyar amfani da bindiga mai karfi a kuma rufaffen wurin da babu hanyar tserewa abin takaici ne.
"Dabbobin da aka saba amfani da su wajen neman suna, galibi mutane ne suka rene su, don haka ba sa tsoron mutane, da hakan ya zamana da sauki wajen hallaka su.
Farautar namun daji a shekarar 2050?
"Kasashen Afirka da dama sun dogara ne kan yawon bude ido a gandun dazuka.
"Baki nawa ne za su daura damarar bulaguron yawon bude idon, bayan sanin cewa ba za su ga manyan dawa ba?"
Farautar neman suna
"Farautar neman suna ta zakuna babban kasuwanci ne.
"Duk da haka mazauna yankin ba sa amfana - kudi kadan ne cikin makudan kudaden mafarautan ke biya a madadin kashe zakin, ke shiga aljihunsu.''
Babu sauran kasaita
"Zakuna basu dace da tsarewa ba."
"A cikin daji suna da muhallinsu kama daga daruruwan mil."
"Dubban zakuna ne aka kulle a gidajen ajiyar namun daji, da wasu cibiyoyin killace dabbobi don wasu bukatu a fadin duniya.
"Duk da cewa a kan tsara musu muhallansu, rayuwa a killace daban ta ke da rayuwar cikin daji."
Duniya babu zakuna?
Raguwar yawan adadin zakunan ya ta'alaka ne da mummunar al'adarmu ta lalatawa da gallazawa da kuma rashin adalci ga namun daji.
"Baya ga bukatar farfado da tunaninmu, akwai dalilai masu muhimmanci na bukatar ceto zakunan.
"A matsayinsu na dabbobi masu farautar nama, zakuna na taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa bunkasar dabbobi masu cin ciyayi da tsirrai.
"Zakuna kan yi farautar dabbobi ne, galibi sukan kama mafiya rauni.
"Hakan ya kan sa garken dabbobi su kasance cikin juriya da koshin lafita.''
Hotuna daga George Logan.