Africa internet: Gwamnatocin Afrika da ke toshe hanyoyin intanet

A girl in the Democratic of Congo on a computer

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A karon farko, wannan na iya kasancewa toshe shafukan sada zumunta da aka fi amfani da su
    • Marubuci, Daga Christopher Giles da Peter Mwai
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check
  • An wallafa

Babu Facebook ko Twitter ko Whatsapp.

Wannan na kara zama ruwan dare a wasu kasashen Afrika, inda gwamnatoci ke toshe intanet ko shafukan sada zumunta lokaci zuwa lokaci.

Uganda ce kasa ta baya bayan nan da ta takaita intanet daf da fara zaben shugaban kasar ran 14 ga watan Janairu.

Masu fafutukar kare hakkin amfani da intanet sun ce wannan tauye hakkin bayyana ra'ayi ne, amma gwamnati ta ce hakan na taimakawa wajen tabbatar da tsaro.

Ya ake toshe intanet?

Gwamnati na iya takaita amfani da intanet ta hanyar bai wa kamfanonin da ke samar da shi umarnin hana masu amfani da itanet dama.

A karon farko, wannan na iya kasancewa toshe shafukan sada zumunta da aka fi amfani da su.

Idan ta yi tsanani, ana iya ba kamfanonin umarnin toshe hanyoyin intanet din ma gaba daya.

Woman voting at polling station in Zanzibar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zimbabwe da Togo da Burundi da Chadi da Mali da Guinea duk sun toshe intanet a bara

Wadanne kasashe ne ke toshe intanet?

Batun toshe intanet na karuwa sosai a Afrika.

Uganda ta bai wa kamfanonin da ke samar da intanet umarnin toshe duka shafukan sada zumunta da manhajojin aika sakonni.

Dama dai masu amfani da intanet da shafukan sada zumunta a kasar na ta korafin rashin iya shiga wasu shafukan.

Tanzania ta takaita damar amfani da intanet da shafukan sada zumunta a lokacin zabenta a watan Oktobar bara.

A watan Yunin bara, ita ma Habasha ta rufe gaba daya intanet din kasar tsawon kusan wata guda a wani martani na tashin hankali da ya biyo bayan kashe shahararren mawaki kuma mai fafutuka Hachalu Hundessa.

Zimbabwe da Togo da Burundi da Chadi da Mali da Guinea duk sun toshe intanet a bara.

A shekarar 2019, an toshe wani bangare ko duka intanet a kalla sau 25 idan aka hada da sau 20 a shekarar 2018 da sau 12 a 2017 a cewar Access Now wata kungiya mai sa ido mai zaman kanta.

Kuma kungiyar ta ce a 2019, bakwai daga cikin kasashen 14 da suka toshe intanet sun taba toshewa a shekaru biyu na baya da suka wuce.

Sabbin kasashen su ne Benin da Gabon da Eritrea da Liberia da Malawi da Mauritania da Zimbabwe.

Wannan wani salo ne da ya karade duniya, inda kasashe da dama ke rufe intanet.

Kungiyar ta ce a shekarar 2019, sau 21 cikin sau 25 da aka toshe intanet ya shafi duka kasashe ko mafi yawan kasashen.

A Sudan da Habasha ne kawai aka toshe intanet din a wasu sassan kasar.

"Wannan ya nuna cewa rufe intanet na karuwa kuma suna shafar Karin mutane a Afrika," a cewar kungiyar.

A ko wace kasa, ya danganta da ko wane kamfanin samar da intanet ya bi umarnin hukumomi.

Wani tsari da ake amfani da shi shi ne toshe wasu shafukan intanet.

A Kenyan girl using a smartphone

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Amma kuma ana iya sa kamfanonin su kasha intanet din gaba daya a kasa bude shafukan intanet

Mai amfani da shafin na iya ganin sakon "server not found" ko kuma "this site has been blocked by the network administrator".

Wani salon kuma shi ne wanda ake kira 'throttling' ko kuma rage karfi ko gudun intanet din.

Wannan zai nuna wa mai amfani da shafin kamar babu network ne, har ya gaji da gwadawa ya hakura.

Amma kuma ana iya sa kamfanonin su kasha intanet din gaba daya a kasa bude shafukan intanet.

Kamfanonin samar da intanet na iya ce wa gwamnati a'a?

Ya danganta da idan gwamnati za ta iya nuna iko kan kamfanonin.

Gwamnati c eke bai wa kamfanonin lasisi, wanda ke nufin za a iya cin tararsu ko a ƙwace lasisinsu.

Kamfanonin na iya kai batun kotu, amma a zahiri ba su cika yi ba.

Amma a shekarar 2019 kotuna a Zimbabwe sun yanke hukuncin sake bude intanet bayan da gwamnati ta bayar da umarnin rufe shi.

Gwamnatin ta mayar da martani ta hanyar sanya sabbin dokoki da za su ba ta damar ikon kan intanet a kasar.

Protests in Zimbabwe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Idan dai ba an toshe intanet din gaba daya ba, akwai hanyoyin da mutane za su iya bi su shiga intanet din

Ministar sadarwar Zimbabwe Monica Mutsvangwa ta ce wannan "zai tabbatar intanet da sauran lamurran fasaha sun amfani al'uma maimakon saba wa tsaron kasa."

Idan dai ba an toshe intanet din gaba daya ba, akwai hanyoyin da mutane za su iya bi su shiga intanet din.

Hanya mafi shahara ita ce ta hanyar amfani da VPN. Wannan wasu hanyoyi ne na intanet masu tsaro, wanda kuma zai yi wuya kamfanonin su iya tsohe su.

Gwamnati na iya toshe VPN amma ba su fiye yi ba saboda suna tsoron shiga hakkin manyan jakadai na kasashen waje da manyan kamfanoni da ke amfani da su.

Wasu gwamnatocin Afrika sun bayyana cewa "labaran karya" a shafukan intanet ne ke sa wa a taikaita amfani da intanet.

Amma wasu masana da masu adawa na cewa wannan kawai wata dama ce ta hana mutane sukar gwamnati, wanda sau da yawa ake yi a Faceboo da WhatsApp.

"Kafin da yayin da kuma bayan zabe, gwamnati na toshe intanet saboda 'yan adawa," a cewar Mista Bekele.

A man in Kinshasa holding a phone

Asalin hoton, Getty Images

Presentational grey line
Reality Check branding
Presentational grey line