Likitan da ya yi shekara biyar bai yi wanka ba a matsayin gwaji

Asalin hoton, James Hamblin
- Marubuci, Daga Margarita Rodriguez
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
- An wallafa
''Ina ji na garau.''
Ga yadda Dr James Hamblin ya rika amsa tambayoyi kan matakin da ya dauka na shafe shekara biyar bai yi wanka ba.
"Za ka ji kawai ka saba da hakan,'' Kana jin ka daidai,'' ya shaida wa BBC.
Hamblin, mai shekaru 37, farfesa ne a sashen nazarin kula da lafiyar al'umma na Jami'ar Yale kuma likitan da ya ƙware a fannin magungunan hana kamuwa da ƙwayoyin cuta.
Ya kuma yi rubutu a mujallar Amurka 'The Atlantic', inda ya wallafa maƙala ta shekarar 2016 mai taken:"I Quit Showering, and Life Continued" wato ''Na daina wanka, kuma rayuwa na tafiya daidai''.
"Mun shafe shekara biyu cur a rayuwarmu muna wanka. Barnar kudi da kuma ruwa nawa muka yi?'' ya rubuta.
A shekarar 2020, Hamblin ya dada yin karin bayan ikan wannan matakin bincike da ya dauka a wani littafi 'Clean: New Science of Skin and the Beauty of Doing Less.'

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa Hamblin ya ƙi amince cewa bai kamata mu daina wanke hannayenmu da sabulu da goge haƙoranmu ba, ya yi amanna cewa ba ma bukatar tsaurarawa wajen tsaftace sauran sassan jikinmu
Gwaji kan 'kaucewa-amfani da sabulu'
Matakin daina yin wankan ya fara ne da wannan gwaji.
"Ina so in gano ko shin me zai faru,'' ya bayyana.
"Na san mutane da yawa da ba sa wanka sosai. Na san hakan na faruwa, amma ina son in gwada a kaina in ga abin da hakan ke haifarwa.''
Don haka, bayan da ya daina wanka a shekarar 2015, shin mene ne hakan ya haifar?
"Bayan wani lokaci jikinka na ƙara amincewa da sabawa da rashin wankan, don haka baka yin wari sosai idan baka yi amfani da sabulu ko man shafawa mai ƙamshi ba,'' ya ce.
"Kuma fatar jikinka ba ta yin maiƙo.''
"Mutane da dama kan yi amfani da sabulun wanke gashi ''shampoo'' su wanke maiƙon mai daga gashinsu, kana su shafa man da yake saka gashin ya yi laushi ''condtioner' suka ƙara masa maski.

Asalin hoton, Getty Images
Idan ka duba yadda abubuwan ke juyawa, gashinka zai koma kamar lokacin da ka fara amfani da wadannan kayayyaki,'' ya ƙara fada.
Amma likitan ya bayyana cewa ya fara gwajin ne sannu a hankali.
Ya fara amfani da sabulu kadan, da kuma man wanke gashi da na man ƙamshin jiki, da kuma yawan yin wanka - a maimakon yi a kullum, ya kan yi fashin kwana uku, kafin daga bisani ya daina wanka gabaki daya.
"Akwai lokutan da na kan so yin wankan saboda ina kewar yin hakan. Na kan ji ina wari da kuma maiko,'' in ji Hamblin.
"Amma hakan ya rika faruwa da ni ne sannu a hankali.''
Tunanin Hambli shi ne a yayin da yake amfani da ruwa da sabulun ''da kadan-kadan'', a lokacin ne ya fara daina jin yana da bukatar'' da kadan-kadan''.
Warin jiki da kwayoyin cutar bacteria
Dan bokon Ba Amurke ya bayyana cewa warin jikinmu na faruwa ne saboda kwayoyin cutar bacteria da ke makale a fatar jikin namu suna samun abinci daga zufa da kuma maikon da ke fita daga jikinmu.
A lokacin da muke shafa wadannan mayuka ko sabulai a fatar jikinmu a kullum, Hamblin ke cewa, ana samun daidaito tsakanin mayukan a kan fatar jikinmu da kuma ƙwayoyin cutar na bakteriya.

Asalin hoton, Getty Images
"Idan ka yi wanka sosai, kana lalata yanayin tsarin halittun,'' ya rubuta a wallafar da ya yi a mujallar ''The Atlantic'' a shekarar 2016.
"Sukan yaɗu cikin sauri, amma su kan fi daidaituwa da nau'ukan ƙwayoyin cutar da ke fitar da wari.''
Haka kuma, likitan ya ce rashin yin wankan zai ƙara ƙarfin ayyukan halittun da tsarinsu ya daidaita, kuma sai mu daina yin wari.
"Ba za ka riƙa ƙamshin ruwan wardi ba ko turaren fesawa a jiki, kamar yadda kuma ba za ka rika warin jiki ba," Hamblin ya ce.
Batun yin warin jiki
A wata hira da wata mujallar kimiyya ta BBC ''Science Focus'' cikin watan Agustan shekarar 2020 , an tambayi Hamblin kan ko me yiwuwa zai damu idan ''yana warin jiki'' kana mutane sun kasa fada masa don ya sani.
Hamblin ya bayyana cewa ya tambayi abokan aikinsa, abokai da wadanda ya saba hulɗa da su kada su damu su fada masa gaskiya a duk lokacin da suka ji jikinsa na wari.
A lokacin ne ya yi ikirarin cewa jikinsa ya kai matakin da ya daina warin da muka saba ji.

Asalin hoton, Getty Images
Gakiyar magana, Hamblin ya ce matarsa na jin dadin sabon warin jikinsa kuma ya ce ''babu rashin dadi'' a wurin sauran mutane.
"Ga yawancin tarihinmu, muna da wani ƙashin jiki da ke wani bangare na yadda muke isar da sako da sauran mutane,'' ya bayyana.
Don haka, likitan ya ce irin wannan ƙamshi ko wari, an riga an kawar da shi daga ilmin halittunmu na zamantakewa.
"Don haka muna fatan mutane kada su yi ƙamshin wani abu da ya wuce na turare ko abubuwan ƙamshi na wanka da na jiki.''
"In ba haka ba, ana nufin suna wari. Idan dai aka ji wani ƙamshi na mutum, to ba abu ne mai kyau ba,'' ya ƙara cewa.
Amma kuma ko shikenan Hamblin ya daina yin wanka kenan?
Ya ce har yanzu ya kan wanke jikinsa a duk lokacin da ''ya yi datti'' ko kuma bayan motsa jiki.
Amma yana ikirarin cewa zamu iya goge jikinmu mu goge maiƙo ta hanyar ''gogewa kawai da hannayenmu da taje gashinmu akai-akai''.
Yanayin fatar jiki yanayin tafiyar da rayuwa ne
Matakin Hamblin na daina yin wanka ba wai don gwaji ne kadai ba.

Asalin hoton, James Hamblin
A matsayin wani ɓangare na ayyukan bincike ga littafin, ya tattauna da mutane da dama da suka hada da ƙwararru kamar likitocin cututtukan fata, da na garkuwar jiki, da na borin jini, da kuma na tauhidi.
Littafin na da matukar muhimmanci ga masana'antar sarrafa kayayyakin gyara fatar jiki.
"Masana'antar da ke sayar da kayyakin gyaran fata da sabulai na mayar da hankali sosai kan manyan abubuwan kawo gyara,'' ya yi amanna.
Yayin da wasu ka iya taimakawa, y ace, yana da muhimmanci a yi tunanin yanayin tunkarar ''ciki-da-waje'' a fannin kula da lafiyar fatar jiki - da hakan ke nufin lafiyar fatar jikinmu ita ma wani bangare ne da ke nuna yadda muke kula da tafiyar da rayuwarmu, da kuma abin da ke faruwa a cikin jikinmu.
Kimiyya da kuma kasuwanci
Ya yi la'akari da cewa babban muhimmin abu ne a banbance tsakanin mece ce kimiyya da kuma mene ne kasuwanci.
Hamblin ya yi ikirarin cewa muna amfani da kayayyaki fiye da yadda muke bukata saboda imanin da muka yi cewa yin hakan zai kara mana lafiya..
Likitan ya kuma yi kuma ce yadda muke kalali da tsaftace kanmu duk irin na hanyoyin zamani ya zo da shi ne.
"Mutane da dama a shekaru 100 da suka gabata, ba su samu cin gajiyar ruwan famfo ba ," Hamblin ya ce.
"Abu ne da sai masu hannu da shuni ke samu a lokacin, amma mutane ba sa samun wannan moriya sosai.''
" Zai iya kasancewa su je kogi ko kuma tafki, amma abu ne da ba za a bukaci yi a kullum ba,'' ya kara da cewa.
"Haka kuma, ba mu da halin irin bin irin wadannan matakai. Saboda haka, mutane da dama kan yi amfani da sabulan da aka sarrafa a cikin gida, kuma ba sa amfani da su a kullum saboda suna da zafi a fatar jiki.''

Asalin hoton, Luis Diaz Devesa
Hamblin ya ƙarƙare a cikin littafinsa cewa zai kasancewa muna yawan yin wanka, kana zai iya kasancewa idan muka daina ya yi amfani.
Daya daga cikin dalilan da suka haifar da wannan tunani shi ne cewa har yanzu bamu fahimci me zai faru idan muka sauya yawan adadin halittun da ba a gani a fatar jikinmu ba.
"Kwayoyin cutar bakteriya da ke cikin fatarmu na da amfani kamar yadda suka fito ga lafiya kamar yadda ƙwayoyin cuta na bakteriya da ke da amfani a cikin hanyoyin sarrafa abinci na kayan cikinmu suke,'' ya ce.
Duk da haka, wadannan kananan halittu na da tarihi na suna maras kyau.
"Amma a cikin shekaru goma da suka gabata, saboda muna da fasahar gwajin kwayoyin halittu, mun san cewa, kananan halittun na nan a ko ina, kuma yawanci ba sa haddasa cututtuka. Kadan daga cikinsu ne ke da hakan,'' Hamblin ya bayyana.
"Hakan zai sa mutane sake tunani kan abin da suke kokarin yi a duk lokacin da suke kokarin yin tsafta saboda, ko shakka babu, muna son mu kawar da cututtukan da kananan kwayoyin cutar ke haddasawa.''
"Amma ba ma son mu kawar da dukkaninsu.''
Shin ko an zuguguta batun yin wanka ne?
Baya ga wadannan, likitan na tunanin cewa ba kowa ba ne ke da wannan tunani kan ko me ake nufi da ka kasance mai tsafta.
Ya kuma yi amanna cewa ana ƙara zuzuta batun yin wanka ne.
"Zan iya cewa ra'ayi ne, amma a likitance ba dole ba ne."

Asalin hoton, Getty Images
"(Amma) Ba ina cewa mutane su daina yin wanka ba ne,'' in ji' Hamblin.
Ta yaya za mu gwada wannan hanya?
Likitan ya yi nuni da cewa ba shi da sha'awar bayar da shawarar abin da ya dace ko abin da bai dace ba, ko kuma nuna cewa matakin da ya dauka shi ne ya fi daidai ga kowa.
Abu ne da shi dai zai ce ya yi masa aiki.
"Amma ga mutanen da suke da matsalolin fatar jiki ko kuma suna son su gwada, zan iya cewa su bi a sannu-sannu, su duba irin hanyar da tafi dace musu.
Kamar misali, amfani da man awnke gashi kadan ne a matakin farko, yayin da wasu kuma sun fi son su fara da man kamshin jiki maras karfi.
"Za ka iya farawa da wanka gajartacce, mai ruwan sanyi sannan kadan-kadan, ta hanyar amfani da sabulu kadan,'' ya ce.
"Ba sai ya zama wani abin kuzo ku gani ba,'' ya ce.











