Wasika daga Afirka: Abubuwan da ka iya faruwa a shekarar 2021 a nahiyar Afirka

Master KG performing

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Master KG yana waƙar Jerusalema a gaban jama'a a Malawi
An wallafa

A jerin wasiƙunmu daga 'yan jaridun Afirka, mai horarwa a fannin aikin jarida da sadarwa Joseph Warungu, ya yi magana da ƙwararru a fannonin harkokin kuɗi, da siyasa, da kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe, don yin nazari kan ci gaban da za a iya samu a nahiyar cikin shekarar 2021.

Short presentational grey line

"Wakar Jerusalema alama ce da ke nuna gagarumar nasara da samun bunkasa ga wakokin Afirka a shekarar 2021,'' in ji wata babbar mai tsara wakoki a kasar Tanzania Christine Mosha.

Yayin da wasu ke gaggawar mantawa da abubuwan da suka faru cikin watanni 12 da suka gabata, mai shirya wakoki Master KG, ya bayar da tabbacin cewa za a tuna da ita a matsayin muhimmiyar shekara a fannin fasaha ta hanyar fitattun wakokin yabo na addini masu ƙarfafa gwiwa.

Wakar Jerusalema, wacce shaharren mawakin Afirka Ta Kudu Nomcebo Zikode ya jagoranta, ta ja hankulan mutane wajen taka rawa salo daban-daban a sassan duniya.

Ms Mosha, wacce a watan da ya gabata ne aka bai wa muƙami na jagorantar kasuwancin wakokin shahararren kamfanin 'Sony Music na Afirka' da kuma bunkasar cigaban mawaka a gabashin Afirka, ta ce nahiyar ta daya ce a fannin waƙoƙi.

Beyoncé da Burna Boy

"Abubuwa da dama sun faru a cikin shekaru biyu da suka gabata da suka ba ni ƙwarin guiwa. ''Da farko shi ne tagomashin da Afirka ta samu a fannin al'adu da wakoki a fim din nan na 'Black Panther'.

Na biyu, shi ne wakar nan ta Beyoncé a fim din 'The Lion King': Da ta hada da mawaka daga kasashe daban-daban kamar Ghana, da Kamaru da kuma Afirka Ta Kudu.

"Kuma a shekarar bara, mun ga P Diddy wanda ya fito da kundin wakokin dan Najeriya Burna Boy 'Twice As Tall'."

Amma kuma za a samu karin wasu wakoki mafiya kyau ga Afirka a cikin shekarar 2021.

Wasu shugabannin sun dauki munanan dabi'u a shekarar 2020, inda suka mayar da yaki da annobar cutar korona wata dama ta keta hakkin jama'arsu.

An bayar da rahotanni kan yadda jami'an tsaro suka rika gallaza wa mutane a kasashe da dama.

Bayanan bidiyo, Yadda wani yanki a Kenya suka yi wa 'yan sanda bore

Mai sharhi kan al'amuran yau da kullum kuma lauya, Abdul Tejan-Cole, wanda ya taba jagorantar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar Saliyo, na ganin an shiga shekarar 2021 da sauran alamun ɓurɓushin damuwa.

Ya yi nuni da tarin abubuwan da suka faru na al'amuran da suka shafi take hakkin bil adama a wasu kasashen, da suka hada da hana 'yancin fadin albarkacin baki da kafa kungiyoyi, har ma da fadace-fadace a yankuna daban-daban na nahiyar.

"Ci gaba da tashe-tashen hankula a kasashen Ethiopia, da Mali, da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, kana da koma baya a fannin tsarin dimokaradiyya zai haifar da babban kalubale ga nahiyar a cikin shekarar 2021 da ma shekaru masu zuwa,'' ya ce.

'Babu sauran ja-da-baya'

Mr Tejan-Cole ya bayyana cewa, kungiyoyin yankin marasa karsashi kamar su Ecowas a Afirka ta Yamma, da ta saba taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ɗorewar doka da oda a can, ita ce kadai babbar abin damuwa.

"Amsar ba ta ƙara ja-da-baya ba a fannin mulkin kama-karya da tsarin jam'iya daya. Mun manta cikin sauri irin mummunan tasirin da tsarin jam'iya daya ya yi a cikin shekarar 1970 da 1980."

Ya ce, nahiyar na bukatar farkawa daga barci wajen ''dakatar da koma-bayan tare da komawa tafarkin dimokaradiyya ta gaskiya - wacce ke cike da bin doka da oda, da gudanar da sahihin zabe, da bayar da 'yancin fadin albarkacin baki, da shugabanci na gari, da kuma tafiyar da tsarin mulki da za a mutunta ba sauyawa ba don kawai shugaban kasa ya so ya dauwama a kan karagar mulki.

"Dimokaradiyyar gaskiya ta hada da ginawa da samun cancantar amincewar mutane tare da inganta rayuwarsu."

2px presentational grey line

Za ku so ku karanta waɗannan labaran:

2px presentational grey line

Ta bangaren harkar kudi, 'yan Afirka na bukatar ɗaura babbar ɗamara a harkokin rayuwarsu.

Julians Amboko, masani a fannin tattalin arziki kuma editan harkokin kasuwanci a gidan talabijin na wajen kasar Kenya NTV, ya yi hasashe mai tsauri a wannan shekarar.

"Babban abin damuwa zai kasance batun basussukan jama'a. Hakan ya kara ta'azzara saboda bukatun samun kudade masu yawa da kuma koma baya a bangaren tara kudaden haraji da gwamnatoci ke bukata don yaki da annobar korona.

"Za kuma mu fuskanci tafiyar hawainiya a farfadowar da bata taka kara ta karya ba saboda tattalin arzkin kasashen da suka dogara da samu daga man fetur, da noman gahawa, da ganyen shayi, da hakar zinari zai gamu da koma baya saboda faduwar farashinsu a kasuwar duniya saboda karancin bukatarsu.''

Mr Amboko ya ce su ma masu sayen kayan za su gamu da cikas bayan da ake sa ran kudaden haraji za su karu.

Christine Mosha
Christine Mosha
Coronavirus has taught us that you have to diversify and have multiple revenue streams beyond just selling music"
Christine Mosha
Music industry executive
1px transparent line

Amma akwai wani abu da za mu iya koya daga cikin watanni 12 da suka gabata, wanda zai taimaka mana wajen tafiyar da lamurranmu a sabuwar shekarar?

Babbar mai shirya wakokin Ms Mosha ta ce amsar wannan tambaya ta dogara ne ga raba kafa.

"Annobar cutar korona ta shafi mawakan Afirka da dama saboda sun dogara ne kacokan kan irin abinda su kan samu daga wakokin da suke yi,'' ta ce, tana mai bayar da shawara ga mawakan da su zage damtse.

"Cutar korona ta koya mana cewa dole mu raba kafa wajen hanyoyin samun kudaden shiga da suka wuce na wakoki kawai." A Afirka idan ka daina waka da rawa, shikenan.'' Za ka zama ba komai ba. Ya kamata su yi tunanin saka jari a wasu fannonin kasuwancin''.

Nasarorin Afirka

Ta ɓangaren manufofi, Mr Tejan-Cole ya ce cutar korona ta nuna cewa Afirka na buƙatar mayar da hankali wajen sabbin hanyoyin fasahar samun kudin shiga.

"Akwai manyan nasarori. A kasar Senegal, masu bincike a cibiyar Pasteur sun samar da wurin gwajin gano cutar korona a kan dalar Amurka daya.

A lokaci guda, dalibai masu koyin aikin injiniya sun gina wani mutum-mutumi mai gudanar da ayyuka da yawa don rage wa ma'aikatan kiwon lafiya nauyi.

Ita ma kasar Ghana ta samar da wurin gwajin na cutar korona mai saukin kudi da a yanzu haka ake kan tantancewa.''

Joseph Warungu in front of Nairobi's famous fig tree
Geofrey Angote
Our industries have potential but those in public service must now be selfless and make plans to help the ordinary citizen"
Joseph Warungu
Media and communication trainer
1px transparent line

A ganin Mr Amboko, cutar korona ta tuna wa da shugabannin kasashen Afirka matsalolin kasancewar akasarin wadanda ke aikin ma'aikatan basu da tsarin kariya game da shari'a a hukumance.

"Ko da tsara manufofin shigowa cikin lamari a lokacin annoba ko wata matsala sun zama da cikas saboda babu takamaimen mutanen da za ka dosa wajen neman taimako.

"Abin da ya sa kullen korona ya fi yin mummunan tasiri a kasashe masu tasowa fiye da kasashen da suka ci gaba ta fannin tattalin arziki shi ne, saboda iyalai a irin wadannan kasashe ka iya zama lami lafiya ba tare da gudanar da wani aikin na samun kudaden shiga ba."

Nasarorin wakar Jerusalema da ta mamaye kafofin yanar gizo a fadin duniya da kuma tsara raye-rayen da 'yan majalisunmu da shugabanni da sauransu suka gudanar, yan una hanyoyin samun nasara a nahiyar.

Masana'antunmu na da basira, amma wanda ke aikin gwamnati dole su zage damtse wajen tsara yadda za su taimaka wa masu kananan karfi, kada su yi nesa da juna sosai tsakaninsu da kudi s shekarar 2021.

Presentational grey line