COVID-19: Shin shekarar 2020 ce mafi muni a tarihin duniya?

Asalin hoton, Getty Images
Ga yawancinmu, shekarar 2020 shekara ce mai tsanani, ƙunci da yawan amfani da manjahar zoom, yayin da wasu kuma ke ganin cewa annobar korona ta mayar da shekarar mafi muni a tsawon shekaru.
Amma duba da abubuwan da suka faru a baya na iya nuna cewa wataƙila abubuwa za su iya fin tsanani a nan gaba.
Duban baya da sauri kan tarihi yana nuna mana cewa abubuwa na iya yin muni sosai, amma ya kamata mu duba nasarorin da muka samu. Bari mu duba abubuwan baƙin ciki da na alheri da suka faru a 2020 domin kwatanta su da baya.
A cikin 2020, cutar korona ta kashe dubban mutane
Ya zuwa ranar 17 ga watan Disamba, cutar korona ta kama mutane sama da miliyan 74.5 kuma ta kashe sama da miliyan 1.6 a duniya, bisa ga bayanan da Jami'ar Johns Hopkins ta tattara.
Amma ko kaɗan tasirinta bai kama ƙafar annobobin da suka fi ta yin tasiri a duniya ba.
Annobar da ta fi kowacce kashe mutane a duniya ita ce Black Death, wadda ta hallaka mutum miliyan 25 a Turai sannan ta kashe mutum miliyan 200 a duniya a shekarar 1346.

Asalin hoton, Getty Images
Cutar Spanish Flu ta mamaye ko'ina cikin duniya a 1918, inda sojoji suka yaɗa ta bayan dawowa daga yaƙin Duniya na Ɗaya, sannan ta kashe mutane miliyan 50.
Wannan ya yi daidai da kashi 3-5 na yawan mutanenn duniya baki ɗaya.
HIV da AIDs sun kashe fiye da mutane miliyan 32 tun lokacin da cutar ta ɓarke a shekarun 1980.
A shekarar 2020, mutane da yawa sun rasa ayyukansu
Ta yi matuƙar shafar 'tattalin arzikin duniya, kuma ta yi illa ga rayuwar mutane a faɗin duniya.
Sai dai har yanzu, adadin waɗanda suka rasa rayukansu bai kai na waɗanda suka rasa ba a yayin matsalar tattalin arziki da duniya ta yi fama da ita a 1929 zuwa da 33.

Asalin hoton, Getty Images
A 2020, ban iya ganin abokaina ba
Gaskiya ne cewa yawancin kwanakin wannan shekarar an ƙare su ne a cikin gida, nesa da yan uwa.
Amma a shekarar 536, yawancin al'ummar duniya ba ma sa iya ganin sararin samaniya.
Wani hazo mai ban mamaki ne ya baibaye Turai, Gabas ta Tsakiya da wasu sassan Asiya, abin da ya janyo baƙin duhu ba dare ba rana har tsawon watanni 18, a cewar masanin tarihi na Harvard Medieval kuma masanin kimiyyar kayan tarihi Michael McCormick.
Wannan lokaci ya kasance mafi muni, a cewar masanin.

Asalin hoton, Getty Images
A shekarar 2020, fashewar abubuwa ta lalata tashar jirgin ruwan Beirut
Fashewar ba-zata ta kimanin tan 2,750 na sinadarin ammonium nitrate ranar 4 ga watan Agusta ta yi sanadin mutuwar kimanin mutum 190, tare da jikkata sama da 6,000.
Ta kasance ɗaya daga cikin fashewa mafi girma da ba ta nukuliya ba a tarihi, masana sun ce yawan sinadaran da suka janyo fashewar sun kai kilotan na TNT, kusan ninki 20 na bom ɗin da Aaka jefawa yankin Hiroshima.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Amma a cikin watan Disambar 1984, dubun dubatar mutane a garin Bhopal na Indiya sun mutu sanadiyyar malalewar sinadarai daga wata masana'anta, wanda shi ma na ɗaya daga cikin mafi munin bala'o'in masana'antu a tarihin zamani.
Gwamnatin Indiya ta ce kimanin mutane 3,500 suka mutu a cikin 'yan kwanaki, tare da kashe fiye da 15,000 a cikin shekarun da lamarin ya faru, sakamakon cututtukan da suka shafi huhu.
Tun a wancan lokaci ne aka bayyana cewa yankin zai shafe tsawon shekaru cikin mummunan hazo mai yaɗa ɓurɓushin cututtuka, sai dai har yanzu akwai mutane tsilli-tsilli da ke rayuwa a cikinsa.
Layin azurfa
Don haka, ta fuskoki da yawa, 2020 shekara ce mai matuƙar wahala. Cutar da ta ɓarke ta sanya mana tsoro da nesanta jama'a da yan uwansu.
Amma maimakon yanke hukunci a kan kafofin watsa labarai, bari mu mai da hankali kan abubuwa masu kyau da shekarar ta zo da su.
Wakilcin mata a siyasa sun ƙaru. A shekarar 2020, yawan ƙasashen da ke da mace a matsayin shugabar ƙasa ya kai 20, daga 12 a 1995.
Hakanan, wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya gano cewa wakilcin mata a majalisun dokoki ya ninka sau biyu a shekarar 2020, wanda ya kai kashi 25% na dukkan kujerun.

Asalin hoton, Getty Images
Kuma ita ce shekarar da Kamala Harris ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko baƙar fata ta farko da aka zaɓa mataimakiyar shugaban Amurka.
Mutane a duk duniya sun shiga fafutukar adawa da bambancin launin fata, tare da neman sauya al'amura a nan gaba.
Akwai labari mai dadi ga muhalli ma, inda yawan kamfanoni dake alƙawarin rage hayaƙin da suke fitarwa sun ninka a cikin 2020.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce cikin wadanda suka shiga akwai Facebook, da Ford da Mercedes-Benz.











