Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan abubuwan da suka faru a duniya a shekarar 2020
- Marubuci, Buhari Muhammad Fagge
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
- An wallafa
A yayin da muka yi bankwana da shekarar 2020, lokaci ya yi da za mu yi waiwaye kan wasu muhimman abubuwa da suka faru a duniya cikin shekarar.
Kisan Qassem Soleimani
Bari mu fara daga watan Janairu, wanda aka shiga da wani gagarumin rikici tsakanin Amurka da Iran, da yawa sun zaci zai zama yaƙin duniya na uku.
Tun ana faɗan cacar baki da sanya takunkumi tsakani har ta kai ga Amurka ta kai wani mummunan hari kan dakarun Iran a Iraƙi.
Wannan hari ya yi sanadiyyar mutuwar babban janar ɗin sojan Iran Janar Qasem Soleimani ranar 3 ga watan Janairu.
A lokacin jana'izarsa kuwa, akalla mutum 50 ne suka mutu a wani turmutsutsu a Iran yayin da 'yan kasar ke tururuwa zuwa wajen jana'izar babban kwamandan kasar.
Lamarin ya ta'azzara. Iran ta sha alwashin ramuwa inda ta kai hari kan sojin Amurka a Iraƙi ranar 8 ga Janairu kuma da dama suka ji raunuka.
Daga baya dai rikicin ya kwanta.
Ficewar Yarima Harry daga fadar Buckingham
A Burtaniya a ranar 19 ga watan Janairun ne aka tashi da labarin Yarima Harry da matarsa Meghan Markel sun sanar da ajiye muƙamunsu na sarauta, suna cewa suna son su dogara da kansu wajen neman kudi.
Cikin wata sanarwa da suka bayar, ma'auratan sun ce suna son ci gaba da rayuwarsu ne tsakanin Burtaniya da Arewacin Amurka.
Wannan mataki ya ɓata wa Fadar Buckingham rai, saboda babu wanda aka tuntuɓa kan a fitar da sanarwar, wasu ma suka riƙa zargin Meghan da sauya tunanin Yarima Harry.
Annobar cutar korona
Gabanin duk waɗannan abubuwa na sama duniya na ta fama da cutar korona, sai dai ba ta yi ƙamari ba sosai sai a China inda ta samo asali.
A ƙarshen watan Janairun ne, Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta sanya dokar ta ɓaci kan wannan cuta a ɓangaren lafiya, ko da yake ba a fara sanar da ɗaukar matakan kariya ba.
Cutar dai ta ci gaba da yaɗuwa a wasu ƙasashe da dama, kwatsam har ta shiga nahiyar Afrika, inda aka fara samunta a kasashen Masar da Aljeriya.
Bayyana Covid-19 a matsayin annobar duniya - WHO
Duka abubuwan da suke faruwa a rayuwar al'ummar duniya na tafiya ne a karkace, saboda a lokacin kowa ya kwana da sanin annobar korona na ci gaba da yaduwa a duniyar.
A ranar 11 ga watan Maris, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana coronavirus a matsayin annoba ta duniya.
Shugaban hukumar Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce yawan wadanda suka kamu da cutar a wajen China a wannan lokacin ya ninka har sau 13 cikin mako biyu da suka gabata.
Ya kuma ce ya "kadu sosai" da "yanayin yadda aka gaza" dakile cutar.
Annoba ta duniya, ita ce cutar da ta karade duniya a lokaci guda - ana kiranta world pandemic da Ingilishi.
Bayan ta'azzarar cutar a nahiyoyin duniya musamman a Italiya da Iran da Brazil, sai da takai likitocin da ke gaba-gaba wajen yaki da coronavirus sun ce suna fuskantar wani mummunann hali na zabar wanda zai rayu ta hanyar yi musu magani da wanda za su kyale ya mutu ga masu fama da cutar.
An rufe Masallacin Ka'aba da na Annabi Muhammad na Madina
Hukumomi a Saudiyya sun bayar da umarnin rufe Masallacin Annabi (SAW) da ke Madina da kuma na Harami da ke Makkah saboda fargabar ci gaba da yaduwar coronavirus a ranar Alhamis 19 ga watan Maris.
Sanarwar da hukumomin kasar suka fitar ta ce za a rufe dukkan hanyoyin da ke kai wa ga masallatan biyu.
Kazalika hotunan da gwamnati ta wallafa a shafukan sada zumunta ranar Alhamis da Juma'a sun nuna yadda ake rufe kofofin masallatan da kuma wadanda ke nuna su fayau babu kowa.
Da yawa a tsawon rayuwarsu ba su taba ganin wadannan masallatai ba a kulle ko kuma a ce babu kowa cikinsu sai ta dalilin wannan annoba.
Zanga-zangar Black Lives Matter
Zanga-zangar fafutukar Black Lives Matter wato rayuwar baƙaƙen fata na da muhimmanci ta karaɗe wasu ƙasashen duniya a watan Yuni.
Hakan ya samo asali ne bayan kisan da wasu ƴan sanda fararen fata suka yi wa wani baƙar fata ɗan Amurka George Floyd ranar 25 ga watan Mayu.
Kisan Mista Floyd ya kawo sauye-sauye da dama a duniya inda a Amurka Majalisar Wakilan ƙasar wadda 'yan jam'iyyar Democrat ke da rinjaye a cikinta, ta fitar da wani daftarin doka da za ta yi wa ayyukan 'yan sanda garambawul.
Sai dai Shugaba Donald tuni ya bayyana rashin amincewarsa a shafinsa na Twitter inda ya ce: "Yan Democrat na son rusa rundunar 'yan sandanmu kuma suna son a yi watsi da aikinsu. Amma ni ina son a bi DOKA & ODA NE!"
Sabunta alaƙar Isra'ila da ƙasashen Larabawa
Tun bayan yarjejeniyar zaman lafiyar da Masar ta ƙulla da Isra'ila a shekarar 1979, da kuma ta Jordan da ta biyo baya a 1994, ba a sake samun wata ba sai a wanna shekarar.
A 2020 Isra'ila ta fara shirya wa da ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar 13 ga watan Agusta.
A wani biki da Shugaba Trump na Amurka ya jagoranta a Fadar White House, Isra'ila da da Hadaddiyar Daular Larabawa sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.
Wannan sabunta alaƙa ya yi wa Amurka daɗi, wanda hakan ya sanya ta ƙara shigewa gaba wajen ganin kasashen Larabawa da na gabas ta tsakiya sun sake karbar kawancen Isra'ila.
Bayan nan sai kuma Isra'ilan ta shirya da Bahrain ran 18 ga watan Oktoba da Sudan ran 23 ga watan Oktoba da kuma Moroko a farkon watan Disamba.
Amma wannan mataki ya sha suka daga shugabannin Falasdinawa in da suka bayyana shi a matsayin "cin Amana".
Zaɓen Amurka
A watan Nuwamba ne aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Amurka.
Kuma bayan shafe kwanaki ana tattara sakamako, daga baya alƙluma sun nuna ɗan takarar jam'iyyar Democrat Joe Biden ne ya lashe zaɓen, inda ya kayar da shugaba mai ci Donald Trump.
Da farko Mista Trump ya yi watsi da sakamakon yana ta zargin cewa an tafka maguɗi, sai dai bai gabatar da wasu hujjoji da za su nuna hakan ba.
A ƙarshe dai an tabbatar da nasarar Joe Biden a hukumance.
Riga-kafin cutar korona
Bayan an azabtu da yaɗuwar annobar cutar korona a kowane lungu da saƙo na duniya, daga ƙarshe dai wasu manyan kamfanonin haɗa magunguna a wasu ƙasashen duniya sun samu nasarar samar da allurar riga-kafi.
Sannan bayan gwaje-gwaje da aka dinga yi daga baya an amince a yi amfani da ita, kuma tuni ƙasashe fiye da 30 suka fara yi wa al'ummarsu a ƙrshen shekarar 2020.