Duniyoyin Jupiter da Saturn za su haɗu da juna a watan Disamba

The milky way at Durdle Door, Dorset, UK

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani abin ƙawa da watan Disambar 2020 zai zo da shi a cikin dararen wannan lokacin
    • Marubuci, Daga Eva Ontiveros
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa

Ba kowa ne yake ƙaunar shekarar 2020 ba.

Amma a yaren masana ilimin taurari, shekarar na sauya kanta, watan Disamba ya zo da wani yanayi mai kyau ga sararin samaniya da za ka iya kalla daga cikin gidanka, ba tare da amfani da abin hangen nesa ba ko kuma wata na'ura.

Duniyoyi biyu sun narke sun zama ɗaya, wani irin yanayi mai kamar zubar ruwa, da kuma yadda ake samun kusufin rana... babu abin da kake buƙata sai sararin samaniya wanda yake tas, abin da zai samar da kariya ga idanu, tare da wasu abubuwan burgewa da ake gani.

Cikin wani jeri ga yadda samaniya ta sauya wannan wata:

Daga 13 zuwa 14 ga watan Disamba: Wani yanayi da samaniya ta samu kanta mai kama da zubar ruwa a kan iya gani a ko ina cikin duniya

The Geminids meteor shower during its peak, in the night sky over Tokarevsky Lighthouse on Egersheld Cape on Russky Island in the Sea of Japan, December 2017.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kowa zai iya ganin yayyafin matukar samaniyan ba ta da gajimare

Za a iya ganin sauran filin samaniyar a watannin baya, za ka iya kintsa kanka domin ganin yanayin zubar ruwa daga sama.

"A kan samun irin wannan yanayin duniyar ne lokacin da duniya ke tafiya ta cikin datti da ƙura ta kuma bar wasu dunƙulen ƙankara a baya," in ji Patricia Skelton, wata mai ilimin taurari a Birtaniya.

Amma kowacce shekara, da duniyarmu ta gitta ta ɓaraguzan duwatsun da aka bari, don haka mukan ga wani irin dare mai kyan gani: a kan samu taurari 150 cikin awa ɗaya lokacin da yake kan ganiyarsa, daga 13 zuwa 14 ga watan Disamba.

A composite image of the 2017 Geminid meteor shower in Arizona.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Duhun daren da za a iya samu, yanayin damar da ake da ita ta ganin wannan abin birgewa

"Yanayin yayyafin yana shigowa wannan duniyar ne a gudun kilomita 35 a sakan ɗaya... kilomita 130,000 kenan a sa'a ɗaya!" in ji Patricia.

An fi sa ran ganin yanayin ruwan ɗorawa - a wasu lokutan kuma a ga kore ko shuɗi - tsilla-tsillan haske ke mamaye samaniya a daren," wancan dattin na ƙonewa a hankali"

Yanayin da duhu ya yi nisa, lokacin ne ake da damar ganin kyawun yanayin, amma duk da haka za ka iya ganin ƙurar haske a yankunan birnin.

Kuma ga wasu labarai masu dadin ji: ba kamar shekarar da ta gabata ba (lokacin da ya zo daidai da sanannen abokin gabar hangen taurari, cikakken farin-wata), wannan karo akwai cikakken farin-wata (hakan na nufin farin-watan ya ɓoye shi yasa sararin sama ya ƙara duhu.)

Kuma wasu labarai masu ɗadin ji: ba kamar shekarar da ta gabata, (lokacin da aka samu wani akasi na fitowar wata baki ɗayansa)

14 ga watan Disamba: Ana iya ganin husufin ranar a kasashen Chile da Argentina…

Panoramic view of Patagonia: The recently paved road connecting El Calafate to El Chalten is renowned to be one of the most beautiful roads in the world.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Me manyan masana na baya ke tunani lokacin da ta yi duhu a tsakiyar rana?

…amma har ila yau a ko ina a duniya, saboda duk saboda yadawar da aka yi kai tsaye da shafin intanet!

Kafin ɓarkewar annoba, mutane da dama sun yi tururuwar zuwa Patagonia a kudancin Chile da Argentina don ganin wannan kasaitaccen taro.

Amma a shekara ta 2020 muke, kuma wasu abubuwa da dama yawancinmu sai dai mu kalla ta shafin intanet.

Idan kana cikin mutane kalilan da suka taki sa'a su kalle shi a situ, ka san cewar kada ka sake ka kalli rana kai tsaye - a koda yaushe ka nemi kariya.

Lokacin mintoci 24 na wani abu mai kama da rufa-ido, sabon watan zai ketara ta fuskar rana, tare da rufe ta ga baki ɗaya na tsawon mintoci biyu da dakikoki 9.6,'' in ji wata 'yar sama jannati Tania de Sales Marques, daga 'Royal Observatory Greenwich'.

"Girman ranar ya linka na wata har sau 400,'' Tania ta bayyana, amma kamar ya fi girma saboda ya fi kusa da mu, don haka zai iya mamaye duka zagayen fadin ranar.

Hanyar da watan ke bi a gaban ranar zai lullube haske a kan Amurka ta Kudu, a tsakiyar rana.

Low angle view of solar eclipse in sky during foggy weather.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kada ka sake ka rika kallon rana kai tsaye ko da kuwa lokacin da ta yi kusufi ne.

Wadanda za su fi mayar da hankali kan sauye-sauye a sararin sama zai kasance mazauna Patagonia, wato mutanen Mapuche.

"Ranar na nuna 'ƙarfin namiji', yayin da watan ke nuna 'ƙarfin mace' [...], kuma arangamar da ke tsakanin waɗannan ƙarfafa guda biyu yayin da suke haɗuwa kan hanya ɗaya lokaci ne mai matukar wahala a gare mu,'' in ji Marcelo Huequenman, wani mai koyarwa a fannin gamayyar al'adun mutanen Mapuche.

A al'adance, mutanen Mapuche suna da fargaba game da batun husufin rana kuma a harshensu ana daukar wannan taro a matsayin lhan Antü, da ake yi wa fassara da ''mutuwar rana'', in ji Marcelo.

"An shaida husufin rana a fadin duniya da kuma daukacin tarihi har na tsawon shekara 5,000," in ji Tania.

"Yana da sauki a gane me yasa husufin rana mutane da yawa ke daukarsa a matsayin abu marar kyau a tarihi, a yayin da ake hadiye rana a dan lokaci kankane rana ta zama dare,'' dan sama jannatin ya kara fada.

Tania ta ce "za a iya samun husufin rana kamar sau biyar a shekara, amma ana samun cikakken husufin rana ne sau ɗaya a cikin watanni 18, lokacin da wata yake samun cikakken hasken da yake yi wa rana baka-baka."

Dan haka idan ana so a yi masa shiri kamar yadda ya kamata, za a samu cikakken husufin rana na gaba a yankin Antartuca a watan Disambar 2021, A Idonesia da Australia kuma a watan Afrilun 2023, Amurka da Canada za a samu nasu ne a Afrilun 2024, a kudancin Turai da Greenland a watan Agustan 2026, Arewacin Afrika za yankin gabas ta tsakiya za a yi musu na su ne a Agustan 2027.

21 ga watan Disamba: wata kyakkyawar gamuwa tsakanin duniyar Jupiter da Saturn, wadda za a iya gani a duka fadin duniya

The trio of (L to R) Saturn, Mars and Jupiter in conjunction in the dawn twilight, taken from home in Alberta on March 26, 2020. This is a stack of 10 exposures.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Duniyoyin biyu na haskakawa a matsayin daya: lokacin na ƙarshe da suka kusanci juna shi ne shekara 397 baya, jim kadan bayan Galilei ya kirkiro abin hangen nesa.

"Duniyoyin Jupiter da Saturn za su iya zama wadanda za su fi dadin kallo saboda hasken da suke da shi a samaniya" In ji Ed Bloomer kuma mai ilimin taurari a Royal Observatory Greenwich.

Zai zama abin kwallacewa idanu lokacin da duniyoyi biyu suka shiga jikin juna, inda suka zama abu ɗya kuma suke haskakawa a matsayin abu guda.

Wannan ne kuma abin da muke tsammanin gani a ranar 21 ga watan Disamba. "Waɗanda suke mamakin cewa duniyoyin Jupiter da Saturn za su iya kusantar juna, to za su ga yadda za su zo su haɗe da juna," in ji ED.

Da idanu kuru-kuru, duniyoyin za su kusanci juna kasar da 0.1, amma a zahiri har da wani abu mai kama da siddabaru ciki, amma a yanzu haka akwai kimanin kilomita miliyan 800 tsakanin duniyarmu ta Earth da Jupiter, kuma kwatankwacin haka ne tsakanin Saturn da Jupiter.

Amma a yan watannin bayan nan, manyan duniyoyin biyu suka ƙara kusantar juna kamar yadda muke gani a dararen duniyarmu, kafin daga bisani su zo su haɗe da juna.

"Irin wannan gamayyar wani abu ne mai dadin gani, musamman a ranakun da za su kara matse juna, dan ganin yadda za suy iya sauyawa," in ji ED.

Idan ma kana da abin hangen nesa zaka iya ganin yadda manyan watanni hudu na cikin na Jupiter da suka hada da Io, da Europa da Ganymede da kuma Callisto.

JUpiter da girmnata tana da watanni hudu ne kawai.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Idan kasa abin hangen nesanka zai taimaka wajen kallon: watan Io da na Callisto daga hagu, ita kuma duniyar Jupiter ita ce babba a tsakiya watan Ganymede da na Europa daga dama

Irin wannan haɗuwa da waɗannan duniyoyi ke yi na faruwa ne kawai a cikin shekara 19 da wata shida, "amma na wannan shekarar na musamman ne, saboda haɗuwar ta su a 2020, za ta zama mafi kusa da aka taba samu tun farkon ƙarni na 17".

Lokaci na ƙarshe da wadannan duniyoyi biyu suka kusanci juna shi ne shekara 397 da ta gabata, (a 1623 -Mista Galilei).

Babu mamaki shi yasa masana ilimin taurari suka damu da na wannan shekarar "Saboda ba kasafai ake samun a ga irin wannan dama sau ɗaya a rayuwa ba!" in ji Ed.

"Bibiya yadda duniyoyin za su haɗu zai bai wa dan adam wata damar fahimtar yadda tsarin hasken rana yake tun gabanin a fara zuwa sararin samaniya," kamar yadda ya ce.

Idan babu gajimare a samaniya, zai iya ganuwa cikin sauki, sai dai kuma akwai bukatar hanzartawa wajen kama kusancin nasu: ana da tazarar awa daya ne kawai kafin kuma su kara nisantar kansu.

A yi tanadi gabanin haduwarsu na 'yan darare zai taimaka, saboda an san takamaimai inda za a same su: bangaren kudu maso yamma, sa'a daya da rabi bayan rana ta fadi.

Wani ƙarin garabasa shi ne, 21 ga watan Disamba shi ne daidai ranar da hakan zai faru: ranar farko ta yananyin zafi a kudancin duniya, kuma ranar farko ta sanyi a arewacin duniyar.