Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zanga-zangar End Sars: Matan da suka jagoranci guguwar sauyi a Najeriya
- Marubuci, Daga Azeezat Olaoluwa
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC kan harkar mata a Yammacin Afirka
- An wallafa
Rinu Oduala mai shekara 22 kuma mara tsoron bayyana ra'ayinta - gwamnatin Najeriya na ganin ta a matsayin barzana ta yadda har sai da aka rufe asusunta na banki.
Tana daga cikin dubun-dubatar matasan Najeriya da suka haɗa da mata, da suka kafa tarihi a zanga-zangar da ta karaɗe ƙasar a watan Oktoba kan adawa da zaluncin ƴan sandan runduna ta musamman mai yaƙi da fashi da makami ta Sars.
Ms Oduala tana ɗaya daga cikin waɗanda suka fita tituna bayan da wani bidiyo ya yaɗu kamar wutar daji da ke nuna wani mutum da ake zargin rundunar Sars ta kashe, al'amarin da daga baya ya jawo zanga-zangar EndSars mai neman a kawo ƙarshen rundunar.
Ta samar da wani sansani a wajen ofishin gwamnan Legas ranar 7 ga watan Oktoba, da neman a rusa rundunar.
A matsayinta ta ƙwararriya a tsare-tsaren yaɗa labarai, ta san ta yadda za ta tattara kan mutane a shafukan sada zumunta domin ba ta goyon bayan - tare da samar da barguna ga mutanen da suka dinga kwana a kan tituna tsawon kwana biyu kafin ƴan sanda su kai musu hari.
Matar mai mabiya 172,000 a shafin Tuwita, tana daga cikin ɗumbin matan da suka girgiza hukumomin Najeriya a mako shidan da suka gabata. Fafutukarta ta ENdSars ta sa shafin Tuwita ya tantance shafinta ta hanyar sanya masa shuɗiyar alama.
A yau tana daga cikin kwamitin binciken shari'a kan cin zarafin da ƴan sanda ke yi da ke zama a Legas - ɗaya daga cikin buƙatun masu zanga-zangar bayan da shugaban ƙasa ya rusa rundunar.
Amma ta damu da batun tsaronta kuma tana daga cikin mutum 20 da suka shirya zanga-zangar da babban bankin Najeriya ya rufe asusunsu na banki a farkon watan Nuwamba.
"Abin da ɓacin rai ganin niyyarmu ta ganin an kawo ƙarshen zalincin ƴan sanda ya sa an yi mana tambarin ta'addanci," kamar yadda ta shaida wa BBC.
Babban bankin Najeriya ya ce ya nemi umarnin kotu kan neman rufe asusun bakin na kwana 90 don gano ta yadda suke samun kuɗaɗensu.
Ms Oduala ta ce lauyoyinta na ƙalubalantar dokar.
'Yanzu ma aka fara'
Ita ma wata mai fafutukar EndSars ɗin - lauya Modupe Odele - an ƙwace mata fasfo ɗnta a watan da ya gabata. Ta taimaka wa waɗanda aka kama a lokacin zanga-zangar ta fannin shari'a.
Kuma a makon da ya wuce, an toshe shafin intanet a Najeriya na Gamayyar Masu Rajin Kare Haƙƙin Mata - wata ƙungiya da kusan mata 10 suka kafa a watan Yuli don fafutukar neman daidaiton jinsi - wacce ta taka rawar gani a yayin zanga-zangar EndSars - kuma ba a san waye ya aikata hakan ba.
A yayin zanga-zangar ƙungiyar mai zaman kanta ta haɗa dala 385,000, kimanin miliyan 146 ta hanyar yin gidauniya sannan an kashe wasu kuɗaɗen ta hanyar bayar da taimakon shari'a ga masu zanga-zangar da aka kama, aka biya kuɗaɗen asibiti ga waɗanda suka ji rauni, tare da samar da jami'an tsaro na haya a wuraren da ake zanga-zangar da kuma raba abin kai wa baka.
Ƙungiyar ta ce za a yi amfani da sauran kuɗaɗen ne don samar da tallafi da ya haɗa da bayar da shawarwari kan lafiyar ƙwaƙwalwa ga mutanen da zalincin ƴan sanda ya shafa da kuma iyalan waɗanda suka mutu.
Sannan ƙungiyar na fatan ɗaukar nauyin bikin tunawa da waɗanda ƴan sanda suka kashe.
"Wannan somin taɓi ne kawai kan yunƙurin matasa na kawo sauyi a Najeriya, kan yadda za a inganta halin da ƙsar ke ciki," in ji Fakhrriyyah Hashim, wacce tana cikin waɗanda suka samar da Feminist Coalition, kamar yadda ta shaida wa BBC.
"Za mu ci gaba da yin hakan, musamman saboda mata," a cewarta.
Najeriya ƙasa ce da aka fi bai wa maza fifiko a kan komai, amma ko yaushe mata na bayyan ra'ayoyinsu kan buƙatar samar da sauyi, tun lokacin fafutukar adawa da mulkin mallaka.
Don haka shigewa gaba da mata suka yi a zanga-zangar EndSars ba zai zo wa hukumomi da mamaki ba.
A shekarar 1929 tarzomar mata ta Aba - da aka fi sano da "Yaƙin Mata" ya faru ne sakamakon shirye-shiryen karɓar haraji ga mata ƴan kasuwa a kudancin ƙasar.
Dubban mata ne suka shiga zanga-zangar da ta janyo aka kai hari kan bankuna da ƙona shaguna da kotunan Turawan mulkin mallaka kusan wata biyu. A ƙarshe dole ƴan mulkin mallaka suka ba da kai.
Shekara 18 bayan nan, Funmilayo Ransome-Kuti, mahaifiyar shahararren mawaƙin nan, ta haɗa kan dubban mata don nuna adawa da harajin da ake son sa wa ƙananan ƴan kasuwa.
Bayan nan ta zamo mai fafutuka sosai a lokacin neman ƴancin kan Najeriya.
Mata 20,000 da aka yi ƙiyasin sun shiga ƙungiyarta ta Abeokuta Women's Union sun yi fice sosai kan jajircewa, da rashin bayar da kai har sai sun cimma buƙatarsu.
Ndi Kato, wata mai rajin kare haƙƙin mata da ta taka rawa a zanga-zangar EndSars ta ce: "Tarihin Najeriya ya ga mata da dama da suka dinga fafutukar neman ƴanci. Ba a ɗauki fafutukar da waɗannan matan masu ƙwazo suka yi a baya da muhimmanci ba."
Ƙashin bayan EndSars
Babu wanda ya kai Aisha Yesufu, wacce tana cikin waɗanda suka samar da fafutukar ceton ƴan matan Chibok ta Bring Back Our Girls, sanin wannan. Cikin shekara shida da suka gabata Aisha da ƙungiyarsu sun yi ta aiki don ganin an ceto ƴan matan makarantar sakandare Chibok da mayaƙan Boko Haram suka sace.
Tana daga cikin masu zanga-zangar EndSars da ƴan sanda suka harbawa hayaƙi mai sa hawaye a ABuja, babban birnin Najeriya.
Amma ba ta gudu ba sannan daga baya hotonta da take tsaye ta ɗaga hannu ya zamo wata babbar alama ta fafutukar EndSars.
Ms Yesufu ta ce ba abin mamaki ba ne don mata sun zama ƙashin bayan zanga-zangar EndSars.
"A koyaushe mata ne ke tabbatar da yiwuwar abu. Duk wara zanga-zanga da ta kawo sauyi to mata ne ke jagorantarta," kamar yadda ta shaida min.
"Zanga-zangar EndSars ta yi tasiri sosai saboda rawar da mata suka taka. Musamman ga Gammayar Masu Rajin Kare Haƙƙin Mata, waɗannan matan na da ban mamaki. Haɗn kan ya ƙayatar."
'Ba gudu ba ja da baya'
Ms Kato ta ce ba a gama fafutukar ba: "Batun sake shirin da matasanmu ke yi da sake sabon lale da kuma lalubo hanyoyin da za a jimuryoyinmu ba wai yana nufin mun dai zanga-zanga ba ne."
Mata sun nuna a lokacin zanga-zangar EndSars cewa za su iya amfani da shafukan sada zumunta don a ji kukansu - wanda Ms Yesufu ta ce su yi amfani da damarsu don yaƙar rashin daidaiton jinsi.
"Ya kamata mata su yi fafutuka fiye da ta ta rajin kare haƙƙn mata zuwa nemar wa mata ƙarfin iko. Yanzu lokaci ne na kai kanmu matakin da ya dace da mu. Ya kamata mu daina yarda da hawa teburin sasantawa, ya kamata mun karɓi ragamar komai," in ji ta.
Ms Oduala ta amince cewa fafutukar za ta ci gaba.