Zaɓen Amurka na 2020: Manyan tuhume-tuhume shida da ke jiran Trump bayan zaɓe

    • Marubuci, Daga Joshua Nevett
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa

A matsayinsa na shugaban Amurka, Donald Trump ya ci gajiyar garkuwa ta musamman daga tuhuma kan aikata laifuka, kama daga manyan laifuka, zuwa na jama'a.

Yanzu, bayan da ya faɗi a zaɓen shekara ta 2020, ba da daɗewa ba Mr Trump zai sake zama kamar sauran 'yan kasa.

Hakan na nufin zai rasa duk wata dama da shugaban kasa ke samu, da zai saka shi ya fuskanci masu gabatar da ƙara da lauyoyi.

"Da zarar ya bar karagar mulki, komai zai sauya," in ji Daniel R Alonso, wani tsohon mai gabatar da ƙara na Amurka a birnin New York ya shaida wa BBC.

"Ba zai sake samun damar yin wata barazana irin ta ƙarfin ikon shugaban kasa da kuma kauce wa duk wani bincike ba."

Wani babban bincike kan aikata laifuka a birnin New York shi ne babban abin damuwa ga Mr Trump da kuma kamfanin rukunan gidajensa, da ake kira 'Trump Organization'.

Har ila yau, akwai tarin ƙararraki da suka hada da zarge-zargen aikata zamba daga wani a cikin iyalan, zuwa na aikata cin zarafin mata.

Akwai abubuwa da dama da suka shafi ƙararraki da ka iya bayyana. Anan, muna ganin kusan manyan tuhume-tuhume shida ne ne za su iya bayyana.

1) Zargi kan biyan kuɗin toshiyar baki

Abin da muka sani: Mai tallar kayan ƙawa, Karen McDougal, tauraruwar fina-finai Stormy Daniels da ikirarin kawar da kai daga abubuwan da ke faruwa.

Wannan wani labarin abun da ake fadi da abin kunyar nan na bayar da kudin toshiyar baki. Duka matan biyu sun ce sun yi mu'amala da yin lalata da Mr Trump, kuma sun karɓi kudi don su yi shiru da bakinsu, gabanin zaɓen shugaban kasa na shekara ta 2016.

A lokacin da suka fito suka faɗi gaskiya a shekara ta 2018, sun shafa baƙin fentin siyasa a ƙarƙashin shugabancin Mr Trump, tare da ƙara rura wutar binciken aikata manyan laifuka biyu.

Na farkon ya mayar da hankali kan karya dokokin gwamnatocin tarayya, ko jihohi da kuma hannun da Michael Cohen, tsohon lauyan Mista Trump' ke da shi.

Karkashin binciken, Cohen ya tabbatar da biyan matan biyu kudi. An kuma gabatar da batun biyan kudaden a gaban kotu a matsayin karya dokar kudaden yaƙin neman zaɓe, inda aka yanke wa Cohen hukuncin ɗaurin shekara uku a shekarar 2018.

Cohen ya yi zargin cewa Mista Trump ne ya 'umarce' shi ya biya kudaden, amma babu har yanzu babu wata tuhuma kan shugaban kasar. Me yasa?

Da farko, wajen tuhumar Mista Trump, dole masu gabatar da ƙara za su buƙaci shaidun cewa lallai ya bayar da umarnin Cohen ya biyan kudaden.

Na biyu kuma, ko da kuwa masu gabatar da ƙara na da isassun shaidu, ya saɓa.

Abu mai sauki, ana shirin fara bincike kan aikata laifuka na biyu kan biyan kudaden a birnin New York.

Mun san cewa babban mai shari'a na gundumar Manhattan Cyrus Vance na gudanar da bincike kan ko kamfanin Trump ya bayar da bayanan ƙarya kan abubuwan da ke da alaƙa da biyan kudade.

Abin da ba mu sani ba shi ne ko Mr Vanc na da wata shaida da za su shigar da ƙara kan aikata laifuka.

Abin da ka iya faruwa nan gaba: Bayar da bayanan ƙarya game da harkokin kasuwanci ƙaramin laifi ne a karkashin dokar New York.

Karamin laifi ne da za a iya yanke hukuncin daurin shekara daya. Yanzu ga wani ɓangare na irin dabarun Mista Vance.

Akwai kuma daurin shekara biyu kan shigar da ƙarar ƙananan laifuka a birnin New York.

"Don haka, saboda biyan waɗannan kudade sun faru sama da shekaru biyu da suka gabata, da alama masu gabatar da ƙarar ba su taki sa'a ba,'' in ji Mista Alonso.

Bayan haka kuma, akwai wasu hanyoyin.

A birnin New York, za a iya yin hukunci kan bayar da bayanan karya kan harkokin kasuwanci a matsayin babban laifi, muddin an yi amfani da hakan wajen ɓoye wasu manyan laifuka, kamar yin zamba don kauce wa biyan kudin haraji.

Manyan laifuka sun fi zama babban abu ne da za a iya hukuntawa a tsawon lokaci kana za a iya yanke hukunci mai tsanani na dauri.

Duk da haka, akwai rashin tabbas game da gabatar da ƙarar. Babu tabbaci kan ko za a iya hukunta Mista Trump a karkashin dokar birnin New York kan karya dokar kudaden yakin neman zabe - laifukan da aka daure Cohen a kan sa.

A nan ne inda wani bangare na batun binciken Mista Vance ya shigo.

2) Bincike kan zamba da kauce wa biyan haraji

Abin da muka sani: Shiri ne na ''bi-ta-da-ƙullin siyasa,'' a cewar lauyan Kamfanin Trumo kan batun binciken Mr Vance a watan Agustan 2019.

Bayanan lauyan suna da zafi.

Mista Vance bai jima da fitar da batun neman takardun da ake kira 'subpoena' ba. Ya bukaci ya ga bayanan kudaden na shekaru, da suka hada da na 'Holy Grail' - shaidar biyan kudaden haraji na Mista Trump a shekaru takwas.

Tun bayan nan, Mista Trump ya yi kokarin toshe bayanan na takardun 'subpoena', ya yi gardama a kotuna cewa hakan zai haifar da cin zarafin a siyasance.

A cikin watan Oktoba, kotun tarayya ba ta amince ba, ya saka batun bayanan biyan kudaden harajinsa a nesa da masu gabatar da ƙara.

Shakka babu, Mista Vance ya yi nuni da nuhimmancin batun biyan kudaden harajin Mista Trump a cikin takardun kotu.

Lokacin da ya bukaci bayanan harajin a cikin watan Agusta, Mista Vance ya danganta shi da ''rahoton jama'a da ka iya zama wani babban laifi ne da aka aikata a kamfanin na Mista Trump'', da suka hada da zargin bayar da takardun inshorar banki na bogi.

Da ya gabatar da ƙarar a kotu a watan Satumba ta bayyana zamba wajen biyan haraji a matsayin wani laifi da za iya bayyanawa, muddin aka gano shaidun da suka nuna hakan.

A birnin New York, za a iya tuhumar wasu nau'ukan zambar harajin a matsayin manyan laifuka, da za su iya haifar da hukuncin ɗauri mai tsawo.

Abin da ka iya faruwa nan gaba: Ana sa ran Mista Trump zai daukaka kara game da bukatar miƙa bayanan biyan kudaden harajinsa a gaban Kotun Ƙoli. A can, ana iya sasanta batun.

Ga Mista Trump, batun na da girman gaske.

"Bincike mafi girma kan aikata manyan laifuka su ne wadanda ke bankado batun haraji da na bankunansa,'' a cewar Jonathan Turley, wani farfesan shari'a a Jami'ar George Washington ya shaida wa BBC. ''Amma ko akwai tuhuma kan aikata laifuka, abu ne da har yanzu babu wata shaida.''

Muddin Mista Vance bai samo bayana biyan harajin Mista Trump ba, batun aikata laifin ka iya zama shaida ko akasin hakan.

Ta ko wane bangare, Mista Vance na bukatar wadannan takardun shaidar biyan harajin don ciyar da binciken nasa gaba.

3) Bincike kan batun kasuwancin gidaje da filaye

Abin da muka sani: Babbar mai shari'a ta New York Letitia James ta kasance ƙadangaren bakin tulu a ɓangaren Mista Trump.

Tun a watan Maris na shekara ta 2019 ne, Ms James ta riƙa jagorantar wani bincike kan ko kamfanin Trump ya aikata laifukan da suka shafi zamba kan harkokin gina gidaje.

Har ila yau, tushen wannan bincike ya haifar da koma wa ga Cohen wanda a cikin watan Fabrairun shekara ta 2019, ya shaida wa majalisar dokoki cewa Mista Trump ya ƙara zuzuta martabar ƙadadorinsa na gidaje don samun basussuka da suka ja su yadda zai samu ragi wajen biyan kudaden haraji.

Kalaman Cohen sun bai wa Ms James damar sabon wasu bayanai game da rukunin kamfanin Mista Trump. Kamar Mista Vance, Mista James sai da ya tayar da jijiyar wuya a kotuna game da wadannan bayanai.

Eric Trump, mataimakin shugaban kamfanin na Trump kuma dan shugaban kasar, ya zarge ta tayar da ƙurar ''siyasa''. Duk da haka, sai da ya rubuta neman buƙatar ya zauna tare da ita wajen bayar ba ba'asi a ofishinta cikin watan Oktoba.

Abin da zai iya faruwa nan gaba: Miss James na bukatar karin shaidun bayanai don ciyar da binciken gaba.

A ofis, Mista Trump ya musanta cewa aiki ya yi masa yawan da zai iya fuskantar batun shari'a. Yanzu, ba shi da wani dalili da zai iya bayyanawa.

Mis James ka iya tursasa wa Mista Trump ya zauna amsa tambayoyi da kuma shan rantsuwa, kamar dai ɗansa.

"Yawancin kotuna za su iya sassautawa mai rike da mukamin shugaban kasa misali kan batun dage shari'u zuwa lokacin da yafi ma sa sauki. Amma wannan ba zai zama kariya ba ga mutumin da ba shugaban kasa ne ba," inji Mista Alonso.

Sannan kararraki irin wadannan na iya janyo wa wanda aka kai kara tara ta kudi, idan aka same shi da aikata laifi. Kuma idan haka ne lamarin yake, to kotuna na iya tuhumarsa da aikata manyan laifuka.

4) Kudaden da ya samu ya yi yana kan mulki

An zarge shi da karya dokar da ta shafi kudade lokacin shugabancinsa.

Abin da muka sani: Akwai wasu batutuwa a shari'ance da suka jibanci samun riba ko karuwa ko samun wata dama ta bangaren kudi yayin da mutum ke rike da mukamin gwamnati.

To me ya hada wannan da Mista Trump?

Akwai wata ayar doka da ta bukaci dukkan jami'an gwamnatin Amurka, ciki har da shugaban kasa, da su nemi amincewar Majalisar Kasa kafin su karbi dukkan wata kyauta daga wata kasar.

Akwai shari'a har uku da ke tuhumar Mista Trump da kin neman amincewar. Daya ciinsu ta shafi sauke jami'an kasashen waje da yake yi a otel dinsa mai suna Trump International Hotel da ke birnin Washington DC.

Abin da ka iya faruwa: daga baya: Ana iya iya yin watsi da kararrakin da suka shafi wannan batun inji masana shari'a. Daya cikinsu da 'yan jam'iyyar Democrat suka shigar ta sami matsala a Kotun Kolin Amurka.

5) Kararraki kan cin zarafin mata

Abin da muka sani: Mata masu yawa sun tuhumi Mista Trump da cin mutuncinsu cikin gomman shekarun da suka gabata. Mista Trump ya musanta dukkan tuhume-tuhumen, inda ya rika kiransu "labaran karya".

Yawancin matan sun shigar da kara ne tun gabanin Mista Trump ya lashe zabe a 2016, Mista Trump ya ce zai shigar da kara kan dukkan matan, amma kawo yanzu bai kai ko daya cikinsu kotu ba.

A madadin haka sai ma wasu daga cikin matan ne suka kai shi kara. Biyu cikinsu kuma sun shigar da wasu kararrakin kan Mista Trump bayan da ya kira su makaryata.

Abin da ka iya faruwa: Za a iya ci gaba da karar a yanzu, wanda zai ba lauyoyin matan da suka kai shi kara tattaro bayanai.

A misali, suna iya neman a basu damar daukar kwayoyin halittan Mista Trump wato DNA domin gwadawa da wanda aka samu a jikin Ms Carroll, daya daga cikin matan da suka shigar da kara cewa Mista Trump din yayi mu su fyade.

Akwai kuma wata karar irin wannan da Summer Zervos ta shigar. Zervos ta taba shiga shirin Mista Trump na talabijin mai suna The Apprentice, kuma karar na iya daukar salon ta Ms Carroll.