Ko Trump ya soma karaya ne kan zaben Amurka?

An wallafa

A karon farko Shugaba Donald Trump, na Amurka ya amince da cewa watakil mulkinsa na hanyar zuwa ƙarshe yana mai cewa lokaci ne kadai zai iya bayyana ko zai ci gaba da zama a mulki.

A jawabinsa na farko da ya yi tun bayan zaben kasar da aka yi wanda Joe Biden ya samu nasara, Mr Trump ya ce, shi gwamnatinsa ba za ta sanya dokar kulle ba ga Amurkawa, sai dai ya kara da cewa bai san wacce gwamnati ba ce za ta kasance a nan gaba ba, wannan kuwa lokaci ne kadai zai bayyana hakan inji shi.

A wani taron manema labarai da ya yi a fadar gwamnatin kasar, shugaban ya yi jawabi ne a kan batun cutar korona da ke ci gaba da yaduwa a kasar.

Donald Trump ya bayyana cewa ba zai dawo da dokar kulle a kasar ba duk kuwa da halin da ake ciki yana mai cewa yin haka zai shafi tattalin arzikin kasar matuka gaya.

Kodayake shugaban ya ce an samu nasara wajen samar da rigakafi da ke maganin cutar koronar.

Cutar korona dai na daɗa zama babbar barazana a Amurka inda a baya-bayan nan ake samun mutum fiye da dubu 100 da ke kamuwa da ita a rana guda.

A baya-bayan nan an samu mutum fiye da dubu 150 da suka kamu da cutar, adadi mafi yawa da aka jima ba a samu kamar sa ba.

Tuni dai wasu jihohi a kasar suka fara takaita wasu al'amura na rayuwar yau da kullum saboda takaita yaduwarta.

Har yanzu dai shugaban na Amurka Donald Trump bai amsa cewa ya sha kayi ba a don haka ne ya ce batun mulkin kasar lokaci ne zai bayyana wanda zai mulketa.

Tuni dai Joe Biden wanda ya samu nasara a zaben kasar na 2020, ya yi alkawarin daukar matakin gaggawa wajen yaki da cutar yana mai shan alwashin cewa zai yi aiki tare da masana kimiyya da kwararru wajen yaki da cutar da kuma shawo kan yaduwarta a kasar cikin hanzari.