Masu bibiyar BBC Hausa sun bai wa Shugaba Trump shawara

Ra'ayoyin masu bibiyar BBC
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Dubban masu bibiyar shafukan sada zumunta na BBC Hausa sun ba Shugaba Donald Trump mai barin gado shawara bayan shan kaye a zaɓen shugaban ƙasa a Amurka.

Sun tofa albarkacin bakinsu ne bayan mun buƙaci masu bibiyarmu su bayyana mana irin shawarwarin da za su ba Shugaba Trump musamman bayan ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na Amurka.

A ranar Asabar ne sakamakon zaɓen Amurka ya tabbatar wa Joe Biden na jam'iyyar Democrat nasara bayan samun ƙuri'u fiye da Donald Trump na Republican.

Shugaban ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen na wasu jihohi inda ya garzaya kotu domin neman a sake ƙidayar ƙuri'un zaɓen.

Sanarwar da Donald Trump ya fitar na ƙin amincewa da sakamakon zaben da Joe Biden ya kayar da shi ya haifar da wani yanayin mai ɗaure kai - irin wanda ba a taɓa gani ba a ƙasar.

Dubban masu bibiyarmu a shafukan sada zumunta ne suka bayyana ra'ayoyinsu na shawarwari ga Trump a shafukanmu na Facebook da Twitter da kuma Instagram

A shafinmu na Facebook kaɗai, mutum fiye da dubu shida ne suka yi tsokaci kan shawarwarin da za su ba shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump.

Trump ya yi koyi da Goodluck Jonathan

Galibin mutanen da suka tofa albarkacin bakinsu sun yi kira ga shugaban ya kasance mai kishin ƙasa ya rungumi ƙaddara, ya sauka domin haka siyasa ta gada.

A Twitter @Gentle_ib ya ba Trump shawara inda ya ce - Ya sauka ya mika mulki ga Joe Biden cikin kwanciyar hankali kada a sake jin bakinsa ya yi magana.

@JaphetPhilip ya ce ya rungumi kaddara. Allah Shi ke bayar da mulki ga wadda ya ga dama, a lokacin da ya ga dama.

Ra'ayoyin masu bibiyar BBC

Asalin hoton, Awwal Ahmad

Kada ya zama Gbagbo

Wasu kuma sun yi hannunka mai sanda ne ga Trump inda suka bayar da misali kan abin da ya faru da tsohon shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo wanda yaƙi ƙi sauka daga kan mulki bayan ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa.

Ra'ayoyin masu bibiyar BBC

Ya nemi haƙƙinsa Kotu

Shawarar da wasu kuma suka ba shugaban ita ce ya jajirce ya nemi haƙƙinsa a kotu, amma kuma idan wa'adinsa ya kawo ƙarshe dole ya haƙura ya sauka.

@MalcomAbdallah ya ce kar ya yarda ya kafe sai inda ƙarfinsa ya ƙare.

@ChrisMorganJos1 ya ce Trump Ya tsaya akan abinda kotu zata yi kawai... Yauwa! Tun da Amurka ba Afrika ko Najeriya ba ce. Toh!!!

Ya koma kasuwancinsa

Wasu kuma sun bai wa Trump shawara ya koma ga kasuwancinsa ya fi masa.

Ra'ayoyin masu bibiyar BBC

Wasu kuma sun ba Trump shawara ne ya mutunta kansa domin ko da ya sha kaye a yanzu yana da damar sake tsayawa takara a nan gaba.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Dama can Trump ya sha bayyana cewa ba zai amince da sakamakon zabe ba idan bai sami nasara ba.

Wannan kuma wasu ke ganin wani yanayi ne sabo da ba a saba gani ba a siyasar Amurka.