Zaɓen Amurka Na 2020: Shin Yesu Almasihu kan sa ɗan takara ya ci zaɓen ƙasar?

    • Marubuci, Daga Lebo Diseko
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Religion Reporter
  • An wallafa

"Ubangiji ya halicce mu ne yadda yake so, don haka duk ɗaya muke.''

"Yana kaunarmu, kuma yana son mu yi farin ciki da junanmu, ba ya so kawunanmu su rarrabu.''

Zaune a kan gadonta a gidansu a unguwar Charlotte, Rose Ortiz wata matashiya ce mai shekaru 19 wacce wannan shi ne zaben da za ta yi na farko, tana magana da ni ne ta manahajar Zoom, game da fatanta kan zaben shugaban kasa na Amurka.

Saura makonni kadan kafin a gudanar da zaben da wasu ke kira mafi muhimmanci a tarihin Amurka.

Yayin da take kewaye da hotunan mawaka, Rose tana magana da ni a hankali game da addininta na Kirista, da kuma yadda take ganin yana da tasiri wajen zaben nata.

Duk da shafe makonni tana tunanin ko wa za ta zaba, Rose na ta kokarin zaba tsakanin 'yan takara biyu da dukkaninsu suna da babbar alaka da addini.

Batun cewa Shugaba Donald Trump shi ne shugaban Amurka na farko da ya halarci kasaitaccen taron gangamin shekara kan nuna kin jinin zubar da ciki a cikin watan Janairu ya burge ta.

"A matsayina na Kirista, Ubangiji ba ya son ya ga ana zubar da ciki,'' ta shaida min, ''don haka wannna wani abu ne da na yadda da bangaren Trump''.

Duk da cewa akidar Joe Biden ta darikar Katolika wani abu ne da Rose za ta iya amanna da shi, ya kamata ya kara hobbasa wajen kulla dangantakarsa da matasa.

A kasashe da dama, addini da siyasa ba kasafai suke haduwa wuri guda ba, amma a Amurka lamarin daban yake.

A jihohi kamar North Carolina batun addini ka iya zama mai matukar muhimmanci wajen fafatawa a zaben shugaban kasa.

Daya daga cikin damarar littafin Bible mai tsarki , da hakan ke nufin ka iya zaben Trump ko Biden.

Kafin a sake zabar Trump, akwai bukatar ya dauki jihohi kamar haka. Ya samu galaba sosai a nan a shekara ta 2016, inda ya kayar da Hilary Clinton da kusan kashi 4 bisa dari.

Zaben wannan shekarar na nuna cewa akwai zazzafar karawa. A daidai lokacin da nake wannan rubuta Biden yana kan gaba a jihar North Carolina.

Duka 'yan takarar shugaban kasar biyu suna saka addini a sakonnin da suke yadawa a yakin neman zabe.

Donald Trump na bukatar Amurka ta san cewa shi ne dan takarar da zai kare muradun addinin Kirista.

Abokin karawarsa Joe Biden ya ce wannan zaben wani fagen fama ne ga rayuwar kasar.

Akwai ma'ana a kan haka: fiye da uku bisa hudu na masu kada kuri'ar Kiristoci ne.

Tasirin turawa masu bin darikar Ibanjalika a shekara ta 2016 abu ne da ake ci gaba da tattaunawa a kai.

Zaben da aka gudanar a baya ya nuna cewa fiye da kashi takwas a cikin goma sun zabi Donald Trump a lokacin, kana har yanzu suna cikin muhimman bangarori na jam'iyarsa.

Amma a matsayina na Kirista bakar fata, na san cewa Mujami'ai na da bangarori da dama.

Akasarin Kiristocin 'yan darikar Ibanjalika a Amurka ba fararen fata ba ne.

Don haka, a cikin watanni kadan da suka gabata, na sha tattaunawa da mutane da ba mu saba ji daga gare su ba, a fagen fafatawar siyasa jihar North Carolina.

A wannan shekarar 'yan asalin kasar Spaniya kamar Rose za su kasance manyan kabilu ko marasa rinjaye a fagen zaben, wanda adadinsu ya kai kashi 13 bisa dari na wadanda suka cancanci kada kuri'a.

Amma kuma akwai yiwuwar ba za su fito su kada kuri'a fiye da sauran kabilu ba.

Wata cibiyar bincike a Amurkar ''Pew Research Center'' ta gano cewa "'yan kasar Spaniya da suka cancanci kada kuri'a da kuma ba su kada kuri'ar ba sun wuce yawan wadanda suka kada a ko wane zaben shugaban kasar tun daga shekara ta 1996''.

Ana daukar Kiristocin 'yan asalin kasar Spaniyar a matsayin masu zaben ganin dama. Wasu alamun tasiri ne da za su iya yi da suka kasance a idanun duka 'yan takarar shugabancin kasar biyu.

Kusan rabin 'yan asalin kasar Spaniya mazauna Amurka 'yan darikar Katolika ne, kana akwai yiwuwar su kasance 'yan ra'ayin mazan jiya ne. Amma kuma matsayin Donald Trump kan harkokin shige-da-fice abu ne da zai yi wahala a bari a baya.

Mahaifiyar Rose 'yar kasar Honduras ce kuma takardar izinin zamanta a Amurka na wucin gadi da aka ba ta yanzu haka na cikin rashin tabbas.

Ta fashe da kuka yayin da ta ke fada min yadda rashin tabbas din ya shafi iyalanta, kana ta damu game da abin da ka iya faruwa nan gaba.

" Idan ina da zabi kan me nake bukatar gani game da dan takara, zan so in gan shi yana bai wa 'yan ci rani dama.

"Ya kawai ba su dama su zauna a wannan kasar kana su zauna cikin 'yanci ba tare da wata damuwa kan tunanin korar su ba''.

Jihar North Carolina ta kasaita a fannin addinin Kirista, da sauran abuwawan da suka shafi karfafa addini da kuma littafi mai tsarki na Bible.

A kudanci nan ne garin Charlotte, mahaifar sanannen nan darikar Ibanjalika Billy Graham. Dan shi Franklin mai tsananin goyon bayan Donald Trump ne.

Amma yankin Greensboro, a arewaci wuri ne na Fada bakar fata dan darikar ta Ibanjalika Dr William J Barber II.

Mai rajin kare hakkin bil adama, Dr Barber ya ce amincewa da wasu 'yan ra'ayin mazan jiya suka yi wa Donald Trump '' shaci fadi ne''

Dr Barber ya yi misali kan tarihi mai tsawo na fafutukar siyasa a wata Mujami'ar bakaken fata, tare da zanga-zanga da gangami da yawanci limamin mujami'ar ke jagoranta.

Ya jagoranci wata kungiyar mai fafutikar adalci kan 'yancin zamantakewa da tattalin arziki da ake kira '' Poor People's Campaign''.

A matsayina na bakar fata dan Afirka ta Kudu, ina kallon inda ta gamu da rabu tsakanin fafutukar bakaken fata a Amurka, kuma a kasata, kana kuma tare da hannun wasu shugabannin mujami'a.

Pastor Wesley Morris ya yi tsamo-tsamo cikin gangamin 'yancin marasa galihu da aka yi wa lakabin da ''Poor People's campaign''. Mun tattauna da shi a taron zanga-zanga kan mutuwar wani bakar fata yayinda ya ke hannun 'yan sanda a Greensboro.

"Ina tare da addinin Kirista na Yesu Almasihu. Yesun da ba ya na'am da salon mulkin yau,'' ya ce. Ya kallon yin magana game da rashin adalci a matasyin wani hakkin da ke cikin ayyukan da ke rubuce a littafin Bible,''.

"Ni bakar fata ne da ke limanci a Amurka, wacce ke da dogon tarihi na fito-na-fito da masu fafutikar kare hakkin bil adama. Ina la'akari da haka a duk lokacin da na tsaya ina wa'azi.''."

Pastor Morris na fatan ayyukan da shi da masu fafutikar ke yi zai taimaka a jihar North Carolina.

"Yana da matukar muhimmanci cewa jiharmu na magana da murya mai karfi cewa bata yarda da irin salon manufofi da halin da muka shiga a karkashin mulkin wannan shugaban ba.''

Kuri'un bakaken fata sun ja baya sosai a zaben da aka gudanar na shugaban kasa a baya, daga kashi 66.6 bisa dari a shekara ta 2012 , zuwa kashi 59.6 bisa dari a shekara ta 2016.

Wannan kashi bakwai bisa dari da ya yi kasan shine mafi girma ga tarihin Amurkawa bakaken fata, kana cibiyar bincike ta ''Pew Research Center'' ta ce shine koma baya mafi girma acikin shekaru 20.

Mujami'ar bakaken fata a Amurkar tana da babban tasiri da karfin fada a ji.

Ina so in san ko me ya sa akwai rashin samun hadin kai idan aka zo batun janyo hankulan mutane su fito su kada kuri'a a wancan karon.

Shekarun fasto Mycal Brickhouse 28 kawai, amma yana magana tare da bayar da tabbaci da nuna son girma kamar wani wanda ya shafe shekaru yana gudanar da wa'azi.

Ya ce a shekara ta 2016 mujami'ar bakaken fata ta yi wasa da damar da ta samu a wurin jama'a, inda yanzu dole sai ta yi da gaske wajen sake janyo hankulansu.

"Mujami'ar bakaken fata ta samu tagomashi a baya. Mun samu wadanda ba su taba kada kuri'a ba a baya, amma suka kada wa shugaba Barack Obama.

"Mun samu mun zaburar da Barack Obama, amma ba mu iya yin haka ga Hillary Clinton ba.''

"Yanzu muna wani lokaci inda muke ganin wanda ka kada wa kuri'a shi ne ke da akalar yadda rayuwarka za ta kasance.''

Yana magana ne a kan annobar korona. Matsalar fannin kiwon lafiya ya kara bankado yadda ake nuna halin wariyar launin fata a Amutrka, da kawayar cutar da kuma rasa guraban ayyuka, ya yi mummunan tasiri kan bakaken fata da mutanen Latin Amurka.

Fasto Brickhouse yana ayyukan raba abinci kyauta a mujami'arsa dake Raleigh babban birnin jiharsa. Annobar ta haufar da karuwar matsala sosai.

Baya ga kyautar abincin, Alongside the free meals, masu aikin sa kai na Fasto Brickhouse suna wayar da kan jama'a cewa su yi magana da murya daya a lokacin zaben.

" Kuri'un Kiristoci bakaken fata na da tasiri a lokacin zaben, saboda mun ga cewa ya doara ne a kan ta.''

"Ban yarda cewa shugaba Trump yana gooyon bayan kare martabar Kiristoci ba '' ya shaida min. '' Na yi amanna cewa shugaba Trump yana yaudarar mabiya addinin Kirista ne kawai don ya sake cin zabe.''

Ko shakka babu akwai Kiristoci da ke kaunar abinda shugaba ke yi, kuma Rhonda Allen na daya daga cikinsu.

Wata nutsattsiya, in kuma ba wacce bata son raini ba, mai koyar da harbin bindiga ce kuma ta yi amanna mallakar bindiga 'yancin da Allah ya bai wa kowa ne.

" Wannan a ra'ayi na ne, yakin zuci ne, Yana da kyau wajen kore duk wani mugun abu. Addinin KIrista wwata bataliyar sojin Ubangiji ce a doron kasa.''

Rhonda ta ce Donald Trump " ya nuna kan sa a matsayin abokin Kiristoci'' kuma cewa ta ga '' babu irin wannan'' daga Joe Biden.

Akwai wadanda suke ganin shin me ya sa Kiristoci masu ra'ayin 'yan mazan jiya da dama ke goyon bayan shugaban kasa wanda kalamansa da abubuwan da yake aikatawa da alamu ba sa cikin ayoyin da ke kunshe a liitafin Bible.

Amma kuma a ganin Rhonda abu ne mai sauki. Ta ce ya yi ayyuka a kan abubuwan da suka fi zama muhimmai.

Kamar saka alkalai masu ra'ayin mazan jiya a Kotun Koli, Ko shakka babu amincewa ta baya bayan nan da ya yi wa wani alkali Kirista Amy Coney-Barrett zuwa kotu ya sa Kiristoci da dama kamar Rhonda ke kallon haka a matsayin shaidar cewa Shugaba Trump yana nuna damuwa akan al'amuransu.

Rhonda na kallon mallakar al'amuran da suka shafi babbar kotu a kasar a matsayin wata hanay ta sauya sabuwar doka kan batutuwan zubar da cik. wanda ta ke jira ta ga an dakara baki daya.

Addini na da tasiri a siyasar Amurka a inda ba ya yi a wasu kasashen.

An sha fada min sau da yawa cewa aniyar Hilary Clinton na kin nuna matsayin akidarta ta darikar Methodist a shekara ta 2016, da rashin mu'amala da Kiristoci ya haifar mata koma baya.

Ya sha bamban da Barack Obama, wanda mu'amala da tsare-tsarensa kan addini suka kasance masu inganci wanda ya sa wani fasto mai karfin fada a ji Rick Warren yaba masa a wajen kaddamarwar shekara ta 2009'

A shekaru kadan da suka gabata, wani daga cikin Kiristoci marasa rinjaye ya zama mai fada a ji.

Amma wasu Kiristocin yanzu suna hada kawunansu su ga cewa abinda suka fata za kasance akwai sauyi a sakamakon abin da zai biyo baya a zaben.

Na yi magana da wadanda har yanzu ba su tabbatar ko za su yi zaben ba da suka shaida min cewa suna son dan takarar da ke magan kan kimar addininsu, kana su yi magana da babbar murya kan addinin nasu.

Wsu sun shaida min cewa hakan zai zama mafi muhimmanci fiye da matsayin 'yan takarar kan wasu batutuwa daban.

A matsayina na ma'aikacin BBC na kan boye ra'ayina a gefe yayin da nake aiki a kan labarina.

Amma wannan ya kasance matsayina ne, kuma wasu hirarrakin da na yi da mutane sun taimaka wajen gyara min tunani na game da addini na.

Ban taba tsammani zan yi aiki a kan wannan ba a lokacin zaman kulle a gida, kuma ba zan taba tunanin tasirin da batun nuna wariyar launin fata zai yi a kai na ba.

Wasu abubuwan da mutane ke fada su taimaka min matuka a duk lokacin da na samu kaina cikin kalubale a addini na.

Duk wadanda na yi hira da su a jihar North Carolina na nuna damuwa kan kasarsu, da kuma damuwar abin da ke faruwa a Amurka.

Inda ra'yoyinsu suka zo daida shine tunaninsu game da litttfi mai tsarki Bible.

Addini wata mahanga ce da Amurkawa da dama ke gani a siayasa, don haka tabbas Yesu ka iya zama wani mabudi na samun galabar zaben shugaban kasa.