Fursunonin IS na sake zama barazana a duniya

Rashin saki mayakan ketare da iya haifar da karuwan hare-hare a kasashen da ake rike da su

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Rashin sakin mayakan ketare ka iya haifar da karuwar hare-hare a kasashen da ake rike da su
    • Marubuci, Daga Frank Gardner
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC Kan Shaa'anin Tsaro
  • An wallafa

Ana nuna damuwa dangane da barazanar da ka iya biyo bayan tarin fursunoni mayaka da ake tsare da su a wani wuri mara kyan gani da ke Syria. Wadannan fursunoni da galibinsu mayakan IS ne da ke kokarin ganin yadda za su kubuta.

IS ta sha alwashin 'yantar da su, da matansu da mutanen da suka dogara da su, yayin da masu fatauci ke amfani da tasu damar wajen karbar cin hanci da sunan kubutar da su.

Hukuncin da wata kotu a Burtaniya ta yanke kwanan nan, kan Shamima Begum, haifaffiyar Burtaniya, wacce aka kwacewa takardunta na 'yar kasa ya sake fito da gaskiyar wannan matsala.

Lokacin da IS ta rasa ikonta a Baghuz da ke Syria a Maris din 2019, dubban mabiyanta aka kama tare da garkame su a wasu sansanonin Kurdawa Syria.

Wannan a cewar masu suka da sauran rina a kaba, saboda babban kalubale ne da ka iya sake jefa duniya cikin rikici.

Al-Hol camp, north-east Syria (01/04/19)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mayaka dubu 40 ake da yakinin sun tsere zuwa Syria domin shiga IS tsakanin 2014 zuwa 2019

Wani bincike da Kwalejin Kings ta Landan ta wallafa ya yi gargadi cewa mayakan da ake tserewa na sake haduwa a wasu yankunan duniya, kuma hakan barazana ce domin IS na sake kafuwa.

''Akwai dubban masu tsattsauran ra'ayi, iyalan 'yan tawaye da magoya bayan IS da suka saura a Iraƙi da Syria. Sannan akwai buƙatar a yanke shawara kan ko an shirya durƙusar da Daesh baki daya.''

Wannan layi ne

Salsalar Mayaƙan

Kusan mayaka dubu 40 ake da yakinin sun tsere zuwa Syria domin shiga IS tsakanin 2014 zuwa 2019. An kiyasta cewa akwai mayakan ketare da suka tsira - wasu na gidan yari, tsakanin dubu 10 zuwa 20.

Akwai 'yan kalilan da ake sauraron shari'arsu a kotunan Iraƙi amma akasari an yasar da su a sansanin da shugabannin IS suka lashi takobin 'yantar da su, kuma cikinsu akwai mata.

Bayanan bidiyo, ''Ana mafani da yara wajen kai harin kunar bakin-wake"

A farkon wannan shekara Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai yaran mayaƙan ƙetare kusan dubu takwas da ake riƙe da su a gidan yari.

A cikin wannan adadi, sama da yara 700 ake da yakinin 'yan kasashen Turai ne - da suka hada da Burtaniya - wanda ake nuna halin ko-in-kulla kan mayar da su.

Wannan layi ne

Mata Mayaƙa

Anne Speckhard ta wata cibiya da ke nazarin tsattsauran ra'ayi, ta ce ta zanta da sama da mayaka 200 da iyalansu a cikin shekaru uku da suka gabata.

Ta kuma ziyarci sansanoni da dama a arewa maso gabashin Syria kamar Al-Hol, wanda ta ce yanayin da suke ciki abin nuna damuwa ne.

Bayanan bidiyo, " Akwai mata masu tsauttsauran ra'ayi sosai"

Matan da dama sun nuna sun fice daga IS sai dai rayuwarsu ba ta sauya ba saboda fargabar abin da ke jiransu.

Hakan kusan na nuna cewa kusan dukkanin maykan IS da ke wannan sansani akwai fargaba a tattare da su. Da dama daga cikinsu sun nuna babu ja da baya amma akwai fargabar makomarsu.

Wata kasa da ta yi kokari kwashe 'yan kasarta da ke da alaka da mayakan IS ita ce Rasha, wadda 'yan kasarta da dama mazaunan arewacin Caucasusu suka shiga kungiyar.

''Shugaban Vladmir Putin ya nuna goyon-bayansa kan dawo da mata da yara kasar,'' a cewar Ekaterina Sokirianskaya, shugaba a wata cibiya da ke nazari kan yake-yake a St. Petersburg.

Wannan layi ne

Uzuri

Zancen gaskiya, batun yasarwa ko ƙin kwashe mayaƙa ya ƙunshi dalilai uku; shari'a, jin-ƙai da tsaro.

A bangaren shari'a babu kariya idan aka ce za a bar dubban mutane -musamman yara - da ke tsare a sansani cikin galabaita babu batun shari'a.

Mayaƙan Jihadi da dama, masu zaman kansu da wadanda ke karkashin wasu, sun ce a shirye suke su koma garuruwansu don fuskantar hukunci da amincewa da zaman gidan kaso.

Bayanan bidiyo, Bibbiyar IS daga Syria zuwa Philippines

Matsalar ita ce gwamnatocin ƙasashen yamma na fargbar kawo su gida, saboda akwai yiwuwar rashin hujojji masu karfi su taka rawa wajen sakin su wanda haka ka iya zama barazana ga al'umma.

Akwai kuma fargabar zaman su a gidan yari a cunkushe na iya tasiri ga rayuwar wayanda ba laifi guda suka aikata ba, ko sake gurbata tunaninsu idan sun hadu da muggan mayakan Syria da Iraƙi.

A bangaren jin-ƙai, akwai matsin lamba da caccaka daga kungiyoyin jin-kai da sauran mutane kan yanayin galabaita da ake ciki a sansanin da ake rike fursunoni.

Child walking in Al-Hol camp (22/07/19)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kungiyoyin agaji na korafin cunkoso a gidan yari

Akwai dan tausayi a ko ina a duniya kan mutanen da aka tsare dasu cikin akuba ko da masu laifi ne.

Sai dai kasashen yamma sun rasa karfin ikonsu da dama a gabas ta tsakiya tun shekara ta 2001 lokacin da Amurka ta rinka kwasar daruruwan wayanda ake zargi zuwa gidan yarin Guantanamo Bay a Cuba.

Ga ƙasashen Turai da dama, da su kansu ke alla-wadai da Guantanamo Bay, abin kunya ne a garesu a ce sun kasa tabuka komai kan 'yan kasar su.

Shamima Begum (file photo)
Bayanan hoto, Shamima Begum, wacce ta rasa takardunta na zama 'yar kasar Burtaniya saboda ta shiga IS

Zuwa yanzu, sama da 'yan Burtaniya 800 suka koma kasar su daga yaki a Syria, kuma basa wata barazana mai girma kan tsaro.

Amma wadanan mutane ne da akasari suka fice daga Syria tun farko samo yakin kasar.

A yau M15 (hukumar leƙen asirin Burtaniya) da 'yan sanda na nuna damuwa cewa akasari wayanda ake rike dasu sun sake gurbata, saboda tsawon shekarun da suka dauka suna zama tare da masu tsauttsauran ra'ayi.

Ma'aikatar cikin gidan a Burtaniya, ta ce za ta zo ganin wadanda ake zargi da laifuka a gurfanar da su a Iraƙi da Syria.

Wannan layi ne

Sai me?

Abu mai wahala ne a raba mayaƙan da iyalansu, a kawo su gida a bar mazajen da sune mayakan su fuskanci shari'a? Tunanin Anne Speckhard kenan.

''Akasarin mata,'' a cewarta, ''idan aka yi nasarar yi musu shari'a za su fuskanci hukuncin zaman yari na tsawon lokaci. Amma idan sun je gidan yari, a ƙalla yaransu na iya ziyartarsu. Ba su makale a Syria cikin hadari ba.

''Don haka abin da ya dace shine dawo da yaran da iyayensu tare. Duk da cewa hakan watakil da wuya, amma a kalla yaransu za su samu kariya da tsaro.''

Mayakan Kurdawan Syria, da ke yaki da IS da yanzu kuma ke kula da sansanin, na da tasu matsalolin da ke addabar su.

Matakin janye dakarun Amurka na wucin-gadi da shugaba Trump ya yi, ya ba da damar ci gaba da hare-hare.

Wannan layi ne