Badaƙalar NDDC: Akpabio ya yi amai ya lashe kan bayyana 'yan majalisar da aka bai wa kwangila

Akpabio

Asalin hoton, Godswill Obot Akpabio

Bayanan hoto, Minista Godswill Akpabio
An wallafa

Ministan ma'aikatar da ke kula da yankin Niger-Delta Godswill Akpabio ya tura wa majalisar wakilan Najeriya wasika bayan da ta ba shi wa'adin kwana biyu domin ya wallafa sunayen 'yan majalisar da ya yi zargin cewa suna cin fiye da kashi 60 cikin 100 na kwantaragin da hukumar raya yakin Niger-Delta take bayarwa.

Jinkirin da aka samu gabanin isar wasikar ya sa kakakin majalisar ya umurci Akawun majalisar da ya bi matakan da suka dace don gurfanar da ministan a gaban kuliya, bisa tuhumarsa da yin karya da bata sunan 'yan majalisar.

Hon Kabiru Rurum, dan kwamitin majalisar ne da ke gudanar da bincike a kan zargin badakalar kudi a hukumar NDDCn, kuma yana zauren majalisar lokacin da kakakin ya karanta wasikar wadda ya ce tana cike da waskiya.

Wani dan jinkiri da aka samu gabannin isar wasikar ta sa kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ya umarci Akawun majalisar da ya fara tattara lauyoyin majalisar domin su bi duk matakan da suka dace wajen gurfanar da ministan a gaban shari'a domin tuhumarsa da shirga karya, tare da shafa wa 'yan majalisa kashin-kaji.

Ya yi zargin cewa ministan da wasu jami'an gwamnati sukan yi irin wadannan karairayin ne da nufin dauke hankalin jama'a daga gaskiyar lamari, tare da shiriritar da binciken da ake yi.

Don haka yace majalisar ba za ta raga wa mai yin irin wannan ba, komai girman mukaminsa a ciki da wajen gwamnati.

Sai dai abin tambaya shi ne ko mene ne takamaiman matsayin majalisar yanzu?

Hon Rurum ya ce: ''A yanzu dai an karanta bayani kuma an samu bayanai biyu, na farko an umarci lauyoyin majalisa su gurfanar da shi a kotu kafin zuwan takardarsa.

"Na biyu kuma shugaban majalisa bayan ya gama karanta wasika ya mika wa kwamitin da'a don su sake nazarin takardar don su ba da shawara kan irin matakin da ya kamata a dauka a kansa.''

Wannan binciken hukumar NDDC da 'yan majalisar wakilai ke yi dai babban al'amari ne sakamakon yadda zai shafi makomar martabar 'yan majalisar…idan suka yi shiru ko suka bari ya shiririce, to zargin da ake musu zai tabbata kenan.

Idan kuma suka ci gaba da kwakwa ba a san abin da gaba za ta haifa ba.

Wannan layi ne

Tun da fari dai 'yan Najeriya sun zuba ido don ganin ko me zai biyo baya yayin da wa'adin da majalisar dokokin kasar ta bai wa ministan ma'aikatar raya yankin Neja Delta kan fallasa 'yan majalisar da yake zargi da cin gajiyar kaso mai tsoka na kwangilolin da hukumar NDDC ke bayarwa ke cika ranar Alhamis din.

Majalisar dai na gudanar da binciken almubazzaranci na fiye da naira biliyan 81, sama da dala 210,000 a hukumar.

An kafa hukumar ta raya yankin Neja Delta shekara 20 baya domin inganta rayuwar al'ummar yankin da ke da arzikin mai.

A ranar Litinin ne kuma bayan Shugaban hukumar ta NDDC, Daniel Pondei ya sha tambayoyi daga kwamitin majalisar aka ga ya kife kai kamar ya suma.

Daga nan aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawa.

Ministan ma'aikatar raya Neja Delta yayin da ya bayyana gaban kwamitin a ranar Litinin, ya yi ikirari cewa "'yan majalisar sune suka fi cin gajiyar kwangilolin da hukumar ta bayar.

Da aka tambaye shi ta yaya, ministan sai ya ce, "Yanzu na gama faɗin cewa muna da takardu da ke nuna cewa 'yan majalisar dokoki ake ba wa akasarin kwangilolin na hukumar NDDC".

Sai dai wannan iƙirarin ya fusata Kakakin majalisar wakilan, Mista Gbajabiamila inda ya ba da wa'adin sa'oi 48 ga ministan ya fitar da sunayen mutanen da suka ci gajiyar da kuma cikakken bayani kan kwangilolin da aka bai wa 'yan majalisar ko kuma su fuskanci fushin doka domin dai ganin ya amsa umarnin majalisar.

Wannan layi ne

To ko Akpabio zai bayyana sunayen 'yan majalisar?

'Yan Najeriya na dakon ƙarin bankaɗa daga binciken da ake gudanarwa idan har aka wallafa 'yan majalisar a jadawalin sunayen.

Godswill Akpabio dai tsohon ɗan majalisa ne kafin karɓar mukamin minista a Agustan 2019.

A baya-bayan nan ne kuma, tsohuwar shugabar hukumar NDDC Joy Nunieh ta zargi Akpabio da almundahana; ta shugabanci hukumar ne tsawon wata huɗu kacal kafin a kore ta.

Ms Nunieh ta zargi Akpabio da hannu a tsige ta inda ta ce ya sha matsa mata lamba ta yi rantsuwa don binne almundahanar da aka tafka a hukumar.

Ministan ya musanta zarge-zargen inda ya ce an sauke ta ne saboda "rashin girmama na gaba a aiki".

A lokacin da mukaddashin shugaban hukumar ta NDDC, Mista Pondei da sauran jami'ai suka bayyana gaban majalisa, ya zargi shugaban kwamitin da ke bincikar hukumar ta NDDC, Olubunmi Tunji Ojo da cin hanci tare da ƙin amsa tambayoyin da kwamitin ya riƙa jefa masa.

A lokuta da dama, ana zargin 'yan majalisa a Najeriya da aikata cin hanci ta hanyar karɓar kwangila daga ma'aikatu da hukumomin gwamnati da kuma yin cushe a kasafin kuɗi.

Daniel Pondei

Asalin hoton, NDDC

Bayanan hoto, Daniel Pondei

Ko wane mataki Majalisar Dokokin za ta ɗauka idan zarge-zargen da Akpabio ya yi ba su da tushe?

Wani masanin shari'a ɗan Najeriya da ke zama a Burtaniya Barista Bulama Bukarti ya shaida wa BBC cewa ko da ministan ya gaza fitar da sunayen, majalisar dokokin abu ɗaya kawai za ta iya yi shi ne "ba wa Shugaba Buhari shawarar sauke ministan daga kan muƙaminsa".

"Shawara ce ba dole ba ne".

"a baya, mun ga yadda majalisar dokokin Najeriya ta ba da shawarwari ga shugaban amma ba ɗaya daga ciki daya aiwatar".

"Misali buƙatar 'yan majalisar ta sauya shugaban hukumar yaƙi da masu yiwa arzikin ƙasar ta'annati Ibrahim Magu bata samu shiga ba a wajen shugaban".

Wannan layi ne

Me zai faru idan zargin ministan ya tabbata?

A cewar Barista Bulama Bukarti, idan zarge-zargen da aka yi wa 'yan majalisar ya zama gaske, "'yan majalisar da suka karɓi kwangiloli daga hukumar sun yi abin da ya saɓwa dokokin Najeriya".

"SIdan aka saɓa dokokin majalisa kuma majalisar na iya yanke shawarar dakatar da 'yan majalisar da aka samu da hannu tare da umartarsu sumayar da kuɗaɗen da suka karɓa".

"Za a iya bayyana sunayensu ga jama'a kan abin da suka yi".

"Kazalika, laifi ne a samu ɗan majalisa da hannu a wata badaƙala ƙarkashin sashe na 24 na 'dokar ɗa'ar ma'aikata' ta 'yan majalisar".

Wannan layi ne

Abin da majalisar ya kamata ta yi wa 'yan majalisar da aka samu da laifi

Wani tsohon Kakakin majalisar wakilai Ghali Umar Na'abba ya ce "idan har akwai zarge-zarge kan mambobin majalisa, kamata ya yi kwamitin ɗa'a ya yi bincike".

Idan har zarge-zargen gaskiya ne, sai a miƙa waɗanda suka yi laifin hannun hukumomin da abin ya shafa domin su fuskanci tuhuma"

..

Asalin hoton, Buhari Sallau

Shin Buhari ya sa baki?

Duk da rashin jituwar da aka samu tsakanin jami'an hukumar NDDC da majalisar dokokin Najeriya, Shugaba Buhari ya gargaɗi ministocinsa da sauran shugabannin hukumomin gwamnati da kada su nuna 'rashin girmamawa' ko yi wa majalisar 'maƙarƙashiya'.

Shugaban ya ɗan sa baki yayin wani taro da shugabannin majalisun ƙasar.

Zuwa yanzu, za a ci gaba da bincike yayin da 'yan Najeriya ke dakon ganin yadda binciken badaƙalar kuɗin naira biliyan 81 a hukumar NDDC da aka ƙirƙireta domin magance matsalolin da al'ummar yankin Neja Delta mai arzikin mai ke fuskanta.

Wannan layi ne