Shin ana zaman doya da manja ne tsakanin Buhari da ‘yan majalisar dokoki?

An wallafa

Matakin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauka ranar Talata na gwale 'yan majalisar dattawan kasar bayan sun yi kira a gare shi ya sauke hafsoshin tsaron kasar ya sa masu nazari na tambaya kan ko dai ana yakin sunkuru ne tsakanin shugaban da 'yan majalisar.

A makon jiya ma, shugaban ya umarci minista a ma'aikatar kwadago ya ci gaba da shirinsa na daukar mutum 770, 000 aiki duk da dakatarwar da 'yan majalisar suka yi wa shirin.

Wasu dai na ganin watakila wannan wata alama ce ta sabanin da ke kunno kai ganin a mulkin shugaban na farko an yi ta samun irin hakan tsakanin sa da majalisa ta takwas.

Ko da yake manazarta harkokin siyasa na gani hakan ba abin mamaki ba ne ganin cewa zubin majalisar ba wai ta wani sauya da yawa ba ne, sannan kusan abin da suka tarar suka dora nasu a kai.

Malam Kabiru Sa'idu Sufi wanda ke Nazari kan harkokin Siyasa a Najeriya ya ce, sabanin tsakanin bangaren zartarwar da ta majalisa a mulkin dimokradiya, musamman a tsarin shugaban kasa mai wuka da nama ba bakon abu ne.

Ya ce idan aka yi waiwaye an sha samun irin haka a majalisun da suka gabata tun daga majalisa ta 4 har zuwa ta 8, sai dai kawai a wannan karon ba a taba tunanin za a soma samun irin wannan ba tun a yanzu.

Malam Sufi ya ce akwai dalilai da dama da suka sa ake wannan tunanin, duba da cewa an shekara ana zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu sai ake ganin kamar zai dore a haka.

'Kai ruwa rana'

Fadar gwamnatin Najeriya dai ta taka muhimmiyar rawa wajen nada shugabannin majalisun kasar biyu wanda hakan ne ya sa ake ganin za a iya samun jituwa kuma ba lallai a samu takun-saka kamar abin da ya faru a zamanin majalisa ta takwas ba.

Amma kuma a halin yanzu gashi ana kai ruwa rana, kuma dalilin da ya sa aka yi tunanin ba za a zo wannan gabar ba shine ganin yadda sabon kunshin majalisa ta 9 tazo daidai da bangaren zartarwa.

Sannan shi kansa bangaren zartarwa ya taka muhimmiyar rawa waje kafa wannan shugabanci, in ji Malam Sufi.

"Sai dai kuma ba abin mamaki ba ne duba da cewa akwai dalilai da dama da ke kunshi a tsarin shugaba mai wuka da nama, ya tanadar da cewa kowane bangare na cin gashin kansa kowanne na da huruminsa da damamankin sa kuma kowanne na da damar takawa dayan sa burki."

Masanin ya ce, a yanzu akwai wasu dalilai da suka shafi ita kanta wanann majalisar ta 9, domin a wannan hali da ake ciki yanayin tsaro na kasa da matsin lamba da ake fuskanta shi ya sanya aka ja layi tsakanin bangarorin biyu.

'Ba ta sauya zani ba'

Ana iya cewa kusan dabi'a ce ta wannan dimokradiya, saboda tun lokacin da aka kafa wannan zangon a 1999 ake samun rashin jituwa ko tsakanin 'yan jam'iyya guda ko kuma ita kan ta tsarin shugabanci,

Malam Sufi yace kafin wannan lokaci, a baya ana yi tunanin da wuya sabanin ta kai wanda ake gani a sauran majalisun da suka gabata.

"Na fadi hakan ne saboda rawar da bangaren zartarwa ya taka wajen nade-naden shugabannin majalisun kasar biyu.''

Amma waccan tunanin ta rushe domin kuwa a yanzu wannan yanayi da yake kunon-kai da wuya an tsallake maimaita abin da muka gani a zamanin majalisa ta 8.

"Idan kuma hakan ya tabbata to kusan muna iya cewa ba ta sauya zani ba."

Rikicin zai zo karshe?

Malam Sufi ya ce a yanzu zai yi wuri a yanke hukunci kan makomar rikicin da ke neman kuno kai, amma dai ya danganta da yadda bangarorin biyu suka rike al'amari ko suka bi da batun har a kai karshen sa.

Ba a raina rigimar siyasa, kuma a yanzu ya yi wuri a iya danganta rikicin da matsayin barazan, inji Sufi.

"Amma akwai gudun kar ya zabi gibi ko sanadi da ka iya illa ga jam'iyyar APC ko bude kofa ga 'yan hamayya.''

Karin labaran da za ku so ku karanta

Sharhi, Umaymah Sani Abdulmumin

Yanzu dai an wuce shekara daya a zango wannan Mulki na shekara hudu.

Shiyasa masana ke ganin akwai bukatar yin takatsantsan saboda daga irin wadanan kananan rashin jituwa ake fadawa a rikici.

Sannan jam'iyyun hamayya na amfani da irin wannan dama wajen inganta kawunansu.

Kafin wannan lokaci a makon da ya gabata wasu 'yan majalisar sun nuna damuwa kan tafiyar hawaniyar wasu ayyukan gwamnatin Buhari.

A shekarun mulkinsa na farko Shugaba Buhari ya yi ta samun matsala da bangaren majalisa musamman kan nade-naden wasu mukamai da tsare-tsaren da ya rinka bijirowa da su, inda kowane bangare ya rinka gwada karfin ikonsa da doka ta tanadar.

Wannan na daga cikin dalilan da suka haddasa rigingimu da kuma baraka a jam'iyyar APC da kuma balewar da wasu 'ya'yan jam'iyyar suka rinka yi.

Yanzu dai 'yan Najeriya sun zura ido don ganin yadda zata kaya da kuma rikicin da ake hasashen ka iya sake zama cikas wajen cimma muradai ko ayyukan da gwamnati ta sanya gaba.