Masu kula da gidan zoo din da aka kora sun koma aiki kyauta

Asalin hoton, Cango Wildlife Ranch
- Marubuci, Daga Navin Singh Khadka
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Environment correspondent, BBC World Service
- An wallafa
Jenna Lowe mai shekara 23 ta shafe kimanin shekara biyu tana aiki a gidan ajiye namun daji na Kongo.
Ta bayyana cewa "dalilin da ya sa nake tashi da safe shi ne na kasance da waɗannan dabbobin masu kyau, ba tare da sanin cewa nan gaba za su iya shiga wani hali ba".
Gidan zoo din wanda yake a wajen garin Oudtshoorn da ke Afrika Ta Kudu, za a iya cewa ya fara haɓaka ne shekaru 40 da suka gabata, inda ya fara daga gonar ajiye kadoji zuwa babban gidan zoo wanda a halin yanzu an san shi a faɗin duniya.
A halin yanzu akwai dabbobi iri daban-daban sama da 90 a gidan zoo ɗin.
Amma abu na farko da Jenna ta fara cewa shi ne me zai faru da damisa (cheetahs) da kuma birrai da muke lura da su?
Abokiyar aikin Jenna wato Angelique Oktober ita ma tana da tunani ɗaya da Jenna. "Mu ne uwayen waɗannan dabbobin, kuma uwaye ba su barin 'ya'yansu a lokacin da suka fi buƙatar su," in ji Angelique mai shekaru 25.

Asalin hoton, Cango Wildlife Ranch
Bayan kwana ɗaya, Jenna da Angelique sai suka saka tufafin aikinsu inda suka koma bakin aiki - amma ba tare da biyansu albashi ba. A daidai lokacin da suka isa kofar shiga gidan zoo ɗin, sai suka ga cewa ba su kaɗai ba ne suka amince su koma bakin aiki domin gudanar da aiki kyauta.
Sama da ma'aikata 40 sun yanke shawarar komawa bakin aiki domin ci gaba da taimakawa a daidai lokacin da ake kullen korona.
An tilasta wa masu gidan zoo din rage ma'aikata daga 78 zuwa 24 domin tabbatar da cewa gidan zoo ɗin ya ci gaba da aiki a lokacin kullen korona.
"Da dama daga cikinmu da ba mu samun albashi muna nan, domin taimakawa," in ji Craig Gous.

Asalin hoton, Cango Wildlife Ranch
"A lokacin da muke ganin cewa ba wani ci gaba dangane da raguwar korona, sai muka samu ci gaba," in ji mai gidan zoo ɗin Andrew Eriksen a wata tattauna wa da BBC.
"Ma'aikata da dama sai suka fara shigowa cikin tufafin aiki, sai suka ci gaba da kula da dabbobin cikin jin daɗi - ba tare da tunanin ko za a biyan su ba."
Muhimmancin kula da dabbobi
Akwai sama da dabbobi 4,000 a Gidan Zoo na Cango, kuma masu wurin sun bayyana cewa ana kashe kusan $118,0000 domin kula da dabbobin a duk wata.
Kafin annobar, ana samun mutum 120,000 da ke ziyartar gidan zoo ɗin a duk shekara.
Sai dai a halin yanzu an shafe kusan watanni huɗu da kulle gidan zoo ɗin, tun bayan da gwamnatin Afrika Ta Kudu ta saka dokar kulle.
Sai dai an fara sasauta dokar kullen a hankali, amma har yanzu ba a bayar da dama ga masu wuraren yawon buɗe ido su fara aiki ba.
"Hakan babban ƙalubale ne wurin gudanar da wannan wuri," in ji Mista Eriksen.
"Ba mu samun wani tallafi daga gwamnati ba, kuma mun dogara ne kan masu zuwa gidan zoo din domin samun kuɗin shiga.
Ya bayyana cewa da farko ya yi wa ma'aikatan da zai kora rajista da wata hukuma ta gwamnatin Afrika Ta Kudu da za ta biya su albashin su da suka rasa.

Asalin hoton, Cango Wildlife Ranch
"Wannan tsarin na wata uku ne kacal, kuma a halin yanzu mun shafe watanni huɗu a rufe, ba lallai su samu kuɗin ba.
Ƙalubalen annobar korona ga gidan zoo
Gidajen zoo da kuma na dabbobin ruwa a faɗin duniya sun bayyana cewa dokar kulle ta sa da ƙyar suke rayuwa, duk da tallafin da wasu gwamnatocin suke bayar wa ga wasu gidajen zoo ɗin.
Gidan zoo na Chester da ke Birtaniya ya yi gargaɗin cewa wannan dokar ta kulle za ta iya sa gidan zoo ɗin ya durƙushe.
"Watannin da suka gabata sun kasance masu wuya ga mambobinmu," in ji Gavrielle Kirk-Cohen, daraktar watsa labarai ta ƙunigyar masu gidajen zoo da na dabboin ruwa na duniya wato World Association of Zoos and Aquariums (WAZA).
Ƙungiyar WAZA na da mambobi 300 a faɗin duniya. An yi ƙiyasin cewa akwai gidajen zoo sama da 10,000 a faɗin duniya sai dai babu alƙaluma a hukumance.

Asalin hoton, Cango Wildlife Ranch
Gidan zoo din da ba mutane
Ma'aikatan da suka koma domin ci gaba da aiki kyauta a gidan zoo ɗin sun bayyana cewa ɗabi'un dabbobin sun sauya tun bayan da aka rufe wurin.
"Dabbobin na tunanin me ya sa ba mutane," in ji Ms Lowe. "Suna fito da kawunansu su ga ko akwai mutane sun shigo.
"Sun cika jin bacci ba kamar lokacin da ba, muna shiga domin duba su sosai."
Masana harkokin zoo ɗin sun bayyana cewa wannan dokar kullen ta ƙara danƙon zumunci tsakanin ma'aikatan gidan zo da dabbobi a faɗin duniya.

Asalin hoton, Cango Wildlife Ranch










