Coronavirus a duniya: Shin jemagu na yaɗa cutar korona?

Asalin hoton, Getty Images/BBC
Tunanin jemagu sun jefa Iroro Tanshi cikin yanayi na shauki, ''akwai abin burgewa tattare da su! ta yi murmushi.
Tanshi, 'yar Najeriya ce da ke karatun digirin-digirgir a Jami'ar Fasaha ta Texas da ke Amurka, tana cikin masana kimiyya kalilan da ke fatan kawo sauyi a tunanin mutane kan jemagu - wanda ke fuskantar kyama sakamakon tunanin da ake da shi cewa suna taka rawa wajen sake yada cutar korona.
Rahotanni kashe-kashe da korar jemagu, daga Australia zuwa Indonesia, sun ja hankulan masu kare tsuntsun a duniya baki daya.
Amma ga dalilan da suke sanya daura alhaki kan wannan tsuntsaye marasa laifi.
Me ya sa mutane ke tsangwamar jemagu?

Asalin hoton, Chidiogo Okoye/SMACON/BBC
Mutane na tsangwamar jemagu saboda wata cuta da ake kira Sars-Cov2, cutar da ta haddasa Covid-19, kashi 96 cikin 100 na cutar ta samo asali daga wannan halitta mai alaka ko sifa irin ta jemagu a cewar Tanshi.
Wannan dalili ya sa ana zargin jemagu. Ko daya ke akwai alaka tsakanin halittun a cewar binciken.
''Binciken baya-bayan nan ya nuna cewa shekaru 40 zuwa 70 da suka gabata, cutar Sars-Cov2 ta sama asali ne daga cutar da ke jikin horseshoe bats,'' a cewar Tanshi, ''wannan na kuma sake tabbatar da cewa ba lallai wadanan jemagu ke yada cuta zuwa ga dan adam ba.''
Dr Paul Webala, babban malami ne a fannin halittun dawa a Jami'ar Maasai Mara a Kenya, ya ce: ''rayuwar jemagu da dan adama akwai shamaki, don haka idan har cutar SARS-CoV-2 ta samo asali ne daga jemagu to lallai akwai abinda ke tsakaninsu wanda shi ke yada ta".
Wannan dalili ya sa ake cewa, jemagu ne salsalar cutar, amma ba lallai su suke yada ta ba ga mutane.
Wa za a dorawa alhaki?

Asalin hoton, Dr Paul Webala/BBC
Tanshi da abokanta na kimiyya suna da yakinin cewa mutane ke da alhakin yada annoba tsakaninsu ba wai jemagu ba.
Dr Webala ya ce halaye da dabi'un mutane ne suke yada annoba. ''Akwai sauyi a adadi ko yawan tsuntsaye da halittun dawa wanda yanayin da wasu dabi'u bil adama ke kawo raguwarsu a doron kasa.
''Shaidu da dama sun nuna cewa kokarin hana dabobbi ko taka rawa wajen mutuwarsu a doran kasa ya taka rawa wajen yaduwar sabbin cutuka da a baya ba a san da su ba, a cewar Tanshi.
Kashe jemagu, ba zai ba da kariya daga korona ba. Hasalima, kokarin batar da su ko tarwatsu a doran kasa na sake tsananta yanayin da ake ciki da karuwa cutuka a cewar masana.

Asalin hoton, Getty Images/BBC
''Kusan kashi 70 na jinsin jemagu sama da 14,000 na rayuwa ne ta hanyar cin kwari, a cewar Dr Webala.
''Akasarin irin wadanan halittu ba su da tasiri ga lafiyar dan adam,'' a cewarsa, sai dai suna yada cutuka irisnu zazzabi maleriya.
Akwai riba a rayuwa da Jemagu?

Asalin hoton, Getty Images/BBC
''In dai kana sanya tufafi, za ka sha gahawa ko shayi, kana cin hantsi ko sauran nau'ikan abinci da ake nomawa, to kullum rayuwarka ta na somawa ne da jemagu,'' a cewar Dr Webela.
Jemagu na da muhimmanci wurin wasu sauye-sauye da irin abubuwa da ake sarrafawa. Misali daga abinci zuwa kayan shafe-shafe, kayan adon gida da magunguna.
Jemagu sun yi tasiri a Indonesia wajen noma, Madagascar ta yi nasara wurin kare bishiyunta na kuka sannan akwai dimbin abubuwa da wadanan halittu ke da tasiri a kansu.
Nazarce-nazarce da dama sun nuna yadda jemagu suka samawa manoma a Amurka bilyoyin daloli a shekara da taimakawa wajen rage asarar amfanin gona.
Akwai wani abu na burgewa tattare da Jemagu?

Asalin hoton, Wellcome Collection/BBC
''Jemagu halittu ne na musamman; da kusan kowacce nahiya akwai su,'' a cewar Tanshi. Ta ce a matsayinta na mai bincike kan wannan halitta ta kutsa dazuka, tsaunuka da kogo.''
Rayuwar Jemagu abin sha'awa da burgewa ne, a cewarta.
Dokta Webala ya yi bayani kan burinsa na kare wadannan dabobbi daga karewa a duniya.
''Ya ce bincike ya nuna suna da garkuwa mai karfi da ke karesu daga cutuka.''
Ga wadanda suka nazarci wannan daban sun san cewa akwai kuskure kan yadda aka fahimcesu, maimakon a kyamace su akwai bukatar fahimtar muhimmancinsu a rayuwa.












