Coronavirus: Yadda annobar cutar korona ta sauya mafarkanmu

    • Marubuci, Daga Pooja Chhabria
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa

Kusan mako biyu da fara aiki da dokar zaman gida, wata matashiya mai shekara 19 a kasar Philippines ta fara wasu irin mafarkai.

"Ina kwance a asibiti da tsakar dare wani likita na yi min tiyata a hannuna," in ji Elleisha Angeles.

"Bayan wani dan lokaci, na fita daga asibitin da hannu daya kawai. Na tuna na ga likitan yana yawo yana wasa da hannun nawa da ya cire.

Ya ma fara tsaga shi, kuma na yi matukar dimaucewa."

Bayan nan, ta yi mafarkin rasa wasu abubuwan: "Ko kudi ko kuma komfutata ta tafi da gidanka."

Sai dai ba Elleisha ce kawai ke fuskantar irin wannan mafarkai ba.

Annobar cutar korona na matukar sauya duniya, da ma mafarkai.

Mutane da yawa sun ce tun da annobar ta barke a kasashe sama da 175 kuma aka tilastawa masu zama a gida, suke samun mafarkai barkatai masu tsoratarwa.

Tashin hankali

Deirdre Barret na tattara irin wadannan mafarkan tun watan Maris don fahimtar yadda suka sauya tun farkon annobar.

Ita ce Farfesa a bangaren halayyar dan Adam a Jami'ar Harvard kuma marubuciyar littafin The Committee of Sleep.

"Duk wani abu mai daga hankali na sa karuwar samun mafarkai masu ban tsoro - kuma bincikena na dauke da irin wadannan sosai," a cewarta.

Wasu daga cikin wadanda suka ba da gudunmuwa a binciken sun ce suna samun mafarkai da suka danganci wani abu mai daga hankali: "Bayan da na kalli fim din Contagion, na yi mafarki ina dauke da cutar Covid-19.

A lokacin da nake mafarkin, a zahiri na ji numfashina na daukewa kuma ina jin zafi, ganina ya fara gushewa. Na san mutuwa zan yi.

Sai aka yi min wata allura don samun sauki kuma ta warkar da cutar, amma bana tunanin ta yi aiki."

Deirdre ta yi bincike kan abubuwa da dama masu daga hankali a baya: Amurkawa bayan harin 9/11, 'yan Kuwait bayan da Iraki ta kaddamar da hare-hare a kasar, sojojin Burtaniya a sansanonin fursunonin yakin Nazi.

A aikinta, yake-yaken na da wasu abubuwa masu zama a rai sosai da kwakwalwa ke alakanta yakin da su, shi ya sa suke bayyana a mafarki - amma wannan annobar ta yanzu ta bambanta.

Makiyin boye

"Makiyin boye ne, kuma abubuwan da suka danganci wannan cutar sun fi yawa," a cewarta.

"Mun sha samun mutane suna mafarkin taron kwari, ko zaftarewar kasa da ambaliyar ruwa na Tsunami, guguwa da girgizar kasa."

Charlie na ganin cewa abubuwan da ya fi tsoro na bayyana a mafarkansa.

Tun da aka tursasa wa mutane zama a gida, matashin mai shekara 24 na gundumar Wiltshire a Ingila na samun mafarkai masu ban tsoro da suka kunshi mayan gizo-gizo.

"A wani mafarki da na yi, wani katon gizo-gizo ya hawo kan gadona daga karkashin gadon.

Ya kai girman mage, ga shi fari kuma kafafuwansa na da rassa.

Na fice daga dakin da gudu ina kuruwar neman taimako. Sai mahaifiyata ta kama shi ta sa a wata leda sai ta fita da shi waje, inda ya yi ta motsi a cikin ledar, daga nan kuma sai na farka," in ji shi.

Yana yawan yin mafarkin gizo-gizon amma wani lokaci yana sauya girma da fasali amma a duka mafarkan, yana bayyana ne a cikin gidan.

"Ko yaushe mafarkan na faruwa ne a wurin da na fi samun kwanciyar hankali, wato gadona, don haka idan ina yi sai in ga kamar gaske ne!"

Dierdre na ganin cewa zama a gida na sa mutane su rika tuna mafarkansu sosai kamar ya faru da gaske.

Wani dalili shi ne, mai yiwuwa mutane na bacci tsawon sa'o'i fiye da yadda suka saba a baya.

"Mutane da yawa da bacci ba ya isar su saboda yanayin yadda suke dadewa a aikinsu, ko kuma saboda fita yawo da abokansu, a yanzu suna samun bacci sosai."

Wata daga cikin wadanda suka bayar da gudunmawarsu a binciken Dierdre ta ce, ta yi mafarkin tana zaune a wani wurin shakatawa amma nan da nan ya zama mugun mafarki.

"Ina zaune ina hira da kawaye na a kan wani benci. Sai muka ji kara kuma sai mu ka ga wata katuwar bindiga mai girman gaske a sararin samaniya ta wuce ta samanmu da sauri.

Sai bindigar ta fara jujjuyawa tana setin mutane tana harbinsu, suna mutuwa.

Sai ta juyo wurinmu, kuma sai na fara gudu ina kokarin boyewa."

Mafarkai wasu abubuwa ne da kwakwalwa ke samarwa da har yanzu ba a fahimce su ba, kuma har yanzu an kasa ba da kwakkwaran bayani danagne da su.

Kuma biliyoyin mutane na yin su ko wane dare.

Luigi de Gennaro, wadda ke nazari kan mafarkan 'yan Italiya da aka killace yayin annobar, ya gano cewa an samu karuwar mutane masu tuna mafarkan da suka yi.

Matakin 'REM'

Ta gano cewa dalilin ba ya rasa nasaba da baccin da bai da inganci saboda rashin kwanciyar hankali.

Rashin kwanciyar hankali na iya sa mutane su rika farkawa cikin dare, ko kuma idan suna bacci a wani mataki na bacci da ke kira Rapid Eye Movement (REM).

A matakin REM, idanuwa na yawan motsi, numfashi na sauyawa kuma yadda jinni ke gudana a jiki ma na sauyawa, sai jiki ya shiga wani mataki na rashin iya motsawa da ake kira 'atonia'.

Wanann na faruwa ne duk minti 90 a lokacin bacci, kuma a wannan matakin ne kwakwalwarmu ke mafarki.

Don haka idan mutum ya farka a lokacin da yake wannan mataki, akwai yiwuwar za su fi tuna abubuwan da suka faru a mafarkansu sosai.

"Mafarkai martani ne na yadda muka dauki annobar," a cewarta.

"Muna fuskantar karuwar mutane masu samun mugayen mafarakai a wannan lokaci."

Niamh Devereux, daga Dublin, ta ce ta ga wata fatalwa tsirara a lambu lokacin da ta halarci wata liyafa a mafarki.

"Wata fatalwa tsirara mai ban tsoro ta zo ta kewaye dukanmu kuma raguna na ta yawo a tsakankaninmu," in ji mai shekaru 28 din.

'Na yi matukar tsorata'

"Babu wanda ya kula da abin da ke faruwa, amma ni na yi matukar tsorata da fatalwar da ragunan, musamman ma dai fatalwar. Fatalwar wani tsoho ce."

Kwararru sun amince abubuwan da muke gani yau da kullum a ido biyu na da tasiri kan mafarkan da muke yi. Kuma girman tasirin da ya yi a rayuwarmu, haka girman yadda zai shafi mafarkanmu.

Wannan ya sa mutanen da suke bakin daga suka fi samun mugayen mafarkai.

Kwanan nan Italiya ta amince a fara amfani da wata manhaja ta gano mutanen da suka yi mu'amala da masu dauke da cutar korona mai suna "Immuni" don hana cutar yaduwa.

Carlotta ta kalli labarai inda aka bayyana wannan, sai kawai labarin ya bayyana a mafarkinta:

"Na yi mafarki na tashi na ji wani abu a makale a goshi na. Na je kewaye na tsaya gaban madubi. Na matsar da gashina da ya lullube goshina, kawai sai na ga wasu maballai guda uku.

Biyu daga cikinsu na da wata 'yar jar wuta yayin da dayan ke da koriyar wuta. Wani ya gaya min cewa koriyar wutar na'urar GPS ce da ke sa ido kan ayyukan da mutum yake yi.

Ban san abin da jar wutar ke nufi ba, amma na danna maballin da ke dauke da koriyar wutar sai kawai na tashi daga baccin."

Mai tattara mafarkai

Ta aika wannan mafarkin zuwa wani shafin intanet mai suna idreamofcovid, wanda wata mata mazauniyar jihar California ta bude a yayin annobar.

Erin Gravley ba masaniyya a kimiyya ba ce kuma ba mai bincike ba ce. Ta yi tunanin bude shafin ne bayan ta yi wani mafarki inda mutane ke ta barin tazara a tsakaninsu.

"Mutane na ta barin a kalla mita biyu a tsakaninsu, ba sa yin musabiha da sauransu. Na yi tunanin, ko dai wannan annobar ta fara shiga mafarkan mutane ne," kamar yadda ta bayyana mana a wani sakon email.

'Yar uwarta na taimakawa wajen yin zanen da zai dace da mafarkan kafin a wallafa su a shafin.

Erin na fata wannan aikin nata zai taimaka wajen tattara tsare-tsaren mafarkai yayin da annobar ke sauyawa: "Zai taimaka wajen ganin daidai yadda mafarakai suka sauya yayin da ita ma duniyar ta sauya".

Akwai yiwuwar tattara mafarkai da yawa a jihar New York da ke kasarta. Kawo yanzu, ita ce jihar da ta fi ko wace kasa yawan masu dauke da cutar korona.

Wata mazauniyar jihar, da shekarunta bas u haura sittin ba, ta bayyana wani mafarki da ta yi kwanan nan: "Ina cikin wani kwale-kwale a wani tafki sai wata igiyar ruwa mai kama da tsunami ta yo kaina.

Na daure na haye ta. Sai wata ta sake bayyana, wadda ta fi ta baya girma. Wannan ta zo inda na ke kuma ingiza nib akin ruwan. Na ga manyan duwatsu a gabana. Sai na farka."

Amma mafarkin ya zo min kamar gaske.

"Sai jikina ya rika ba ni cewa wannan igiyar ruwan ta farko, alama ce ta Covid-19 kuma ta biyu alama ce ta sauyin yanayi. Ba ni da yadda zan yi in san yadda na kare."

Mafarkai masu kyau

Za a iya ganin cewa kowa na mugayen mafarkai a wannan lokaci amma bah aka abin yake ba.

"Kuna iya jin mamaki amma akwai wasu rukuni na mutane da ke samunmafarkai masu kyau," in ji Deirdre Barrett.

"Wasu na ganin raguwar gurbatar yanayi ko kuma suna ganin samun maganin cutar a mafarki."

Neeru Malhotra, ta babban birnin Indiya, New Delhi na daya daga cikin wadanann mutanen.

"Tun da aka fara wannan kullen, na ke mafarkin dakunan otal masu kyaun gaske. A talabijin kawai na taba ganin irin wadannan wurare masu matukar kyau!

Idan kuna tunanin yadda za ku sa mafarkanku su zama masu kyau, masu bincike kan bacci na da shawara:

"Da abin da muke kira "tarairayar mafarki", kana iya gaya wa kanka abin da kake so ka gani a mafarkinka kafin ka yi bacci," in ji Deirdre Barret.

"Ku yi tunanin wani mutum ko wuri da kuke so, ko hawa jirgin sama. Ko kuma ku tuna wani mafarki mai kyau da kuka taba yi. Ku yi nananta wa kanku abin da kuke so ku gani a mafarki yayin da bacci ke daukarku."

"Wannan na sa ku samu jin daidai yayin da bacci ke daukarku, kuma akwai yiwuwa mai karfi da ke nuna cewa bukatarku za ta biya."

Nikita Deshpande ce ta yi zane