Me ya sa jami’an tsaron Najeriya suka fi coronavirus kashe mutane?

Police

Asalin hoton, Nigeria Police

    • Marubuci, Ishaq Khalid
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
  • An wallafa

Hukumar kare hakkin bil-Adama ta kasa a Najeriya wato National Human Rights Commission, ta ce jami'an tsaro dake aikin tabbatar da dokar kulle da aka kafa a wasu sassa na kasar don yaki da annobar cutar korona, sun ma fi ita kanta annobar kashe mutane.

Hukumar ta ce jama'a ne suka gabatar da shaidu da hujjoji da ke tabbatar da kashe-kashen mutane da ake zargin jami'an tsaro da aikatawa. Ta ce bincikenta ya nuna cewa jami'an tsaro sun kashe mutane akalla 18 daga lokacin da dokar takaita zirga-zirgar ta soma aiki a ranar 30 ga watan Maris.

Ita kuwa cutar korona, kamar yadda alkaluman hukumomin lafiyar kasar suka nuna, ta kashe mutane 12 ne kawo ranar Alhamis lokacin da hukumar kare hakkin bil-Adaman ta fitar da rahotonta.

Najeriya mai yawan mutane kimanin milyan 200, ta tabbatar da samun mutane fiye da 400 masu dauke da kwayar cutar kawo yanzu amma ana fargabar zata yadu cikin hanzari a yankunan kasar masu cunkoson jama'a muddin ba a yi hattara ba.

Babu tabbacin lokacin da za a daina amfani da matakan takaita zirga-zirga a yankuna na kasar.

Jami'an tsaron Najeriya sun yi 'kaurin suna'

'Yan sanda

Asalin hoton, Nigeria Police

Jami'an tsaron Najeriya da suka hada da 'yan sanda da sojoji sun dade da yin kaurin suna inda ake zarginsu da gallaza wa farar hula da kisa ba ba tare da shari'a ba da kuma tatsar kudade daga jama'a ta hanyar tsoratarwa da azabtarwa, ko kuma ta hanyar cin hanci da rashawa.

Wannan lamari ne dake wanzuwa tun kafin zuwan annobar Korona da kuma dokar da aka kafa da niyyar hana yaduwarta. Kungiyoyin kare hakkin bil-Adama na ciki da wajen kasar sun sha zarginsu da keta hakkin bil-Adama da kuma rashin bin ka'idojin aiki.

Misali, a cewar wata cibiya mai mazauni a Amurka da ake kira Council on Foreign Relations wadda ke nazarin lamura a kasashen duniya, jami'an tsaro na gwamnati sun kashe akalla mutane 1,476 a Najeriya cikin shekara guda da ta gabata.

A cikin rahoton nata hukumar kare hakkin bil-Adama ta kasa, wadda hukuma ce ta gwamnatin Najeriya, ta ce ta samu 'faruwar lamura 8 na kisan mutane ba tare da an yi masu shari'a ba, da suka kai ga mutuwar mutane 18.''

Hukumar ta ce a jimlace ta samu korafe-korafe guda 100 daga mutane a jihohi 24 na Najeriya- ciki har da Legas da Ogun da Abuja - wato yankuna uku na kasar da a farkon makon nan shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da tsawaita masu dokar kulle da makwanni biyu.

Su ma wasu jihohin sun dauki matakai daban-daban na takaita zirga-zirga a yankunansu. Jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda da sojoji da dai sauransu ne aka bai wa alhakin tabbatar da ana bin dokar da matakan.

'Yan Najeriya ba su yi mamakin kashe-kashen farar hular ba

Soja

Asalin hoton, Getty Images

Wannan rahoto na hukumar Kare Hakkin bil-Adama ta kasa a Najeriya bai zo ga 'yan kasar da dama da mamaki ba. Sai dai suna bayyana takaicinsu kan faruwar lamarin.

Wasu 'yan kasar na ganin dama kashe farar hula ba tare da shari'a ba abu ne da ake zargin jami'an tsaro na aikatawa tun kafin zuwan annobar Korona da kuma dokar takaita zirga-zirga don shawo kanta.

To sai dai wani abin jawo hankali a nan shi ne ba kungiyoyin da suka saba yi wa jami'an tsaron kakkausar suka, irinsu Human Rights Watch da Amnesty International ne, suka fara fitar da rahoton caccakar jami'an tsaron ba.

Wannan karon sukar ta fara fitowa ne daga hukuma ta gwamnatin Najeriya, wadda bisa al'ada takan yi taka-tsantsan wajen ragargazar jam'an tsaro a bainar jama'a - wato ba kasafai ta ke kasancewa kan gaba wajen sukar jami'an tsaro ba.

Amma hukumar kare hakkin bil-Adaman ta National Human rights Commission ta kasance kan gaba wajen sukar 'yan sanda da wasu rukunonin jami'an tsaro a wannan lokaci na annobar Korona.

Wasu 'yan Najeriya ta kafofi daban-daban ciki har da a shafukan intanit na cewa wannan matsala ce da dama 'yan kasar ke fuskanta a kulli-yaumin, amma an sake waiwayarta ne albarkacin cutar Korona.

Wasu kafofin labarai na cikin gida a kasar sun ma ambato babban lauyan nan mai fafutikar kare hakkin bil-Adama, Femi Falana, na cewa bayanan da yake da su sun nuna cewa wadanda jami'an tsaro suka kashe, sun dara 18 da hukumar kare hakkin bil-Adama ta kasa ta bayar.

'Yaki da cutar korona ba yaki da ta'addanci ba ne'

Police

Asalin hoton, Nigeria Police

Jami'an tsaron Najeriya cikin shekaru da dama sukan gudanar da ayyuka iri-iri kama daga yaki da kananan barayi, da manyan 'yan fashi da kuma yaki da ta'addanci da rigingimu tsakanin al'umomi.

To amma kamar sauran ma'aikata a Najeriya da sauran sassan duniya, wannan ne karon farko da suke aiki mai nasaba da yaki da annobar cutar Korona wato COVID-19 wadda sabuwar cuta ce da ta zama annoba game-duniya.

A cewar Kabiru Adamu, shugaban wata cibiya mai zaman kanta da ke nazari kan lamuran tsaro wato Beacon Consulting Limited, wani abin lura shi ne ga alama 'yan sandan Najeriya da sauran jami'an tsaro masu tabbatar da dokar kullen ba su fahimci bambancin aiki a yanayin annobar cuta da kuma a yanayi na tabarbarewar tsaro kamar yaki da ta'addanci ba.

Ya ce kuma kamar ba a wayar masu da kai sosai da sosai ba kan yadda za su gudanar da aikin na tabbatar da matakan takaita yaduwar cutar ba.

Mai sharhi kan tsaron ya kara da cewa sakamakon kuncin rayuwa da kuma dokar kullen wasu jama'a na cikin fushi, don haka za su iya samu rashin fahimta da jami'an tsaro har lamarin ya ta'azzara. '

"Cikin lalama ya kamata jami'an tsaro su rika nuna wa jama'a cewa taimakonsu suke yi domin kare lafiyarsu ta yadda jama'a za su fahimta a maimakon amfani da karfi da tursasawa'', inji Kabiru Adamu.

Masana dai na ganin jami'an tsaro da farar hula ya kamata su hada hannu cikin girma da arziki da fahimtar juna wajen yaki da Korona - wadda hankoronta shi ne ta samu galaba a fadin duniya - don a gudu tare a tsira tare.

Shugaba Buhari ya yi magana mai harshen damo

Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Kawo yanzu dai hukumomin tsaron Najeriya ba su maida martani a hukumance ga zargin na hukumar kare hakkin bil-Adama ta kasa ba. To amma a bayan sun sha musanta zarge-zargen keta hakkin bil-Adama suna masu cewa sukan bi ka'idodjin aikinsu sau da kafa, kuma duk jami'in da aka samu da karya ka'idar aiki akan hukunta shi.

Hakazalika, a farkon wannan wata bayan kafa dokar kullen, rundunar 'yan sandan Najeriya ta shawarci 'yan kasar da su kai rahoton jami'ai masu kauce wa ka'idar aiki, tare cewa dole ne a tabbatar 'ba a keta hakkin 'yan Najeriya ba bisa kowane irin dalili.''

Bisa dukkan alamu, wani hanzari ba guda, su kansu mahukunta sun tabbatar da cewa ana samun jami'ansu da kan keta hakkin bil-adama da cin zarafin farar hula.

A yayin da ake aiki da dokar takaita zirga-zirgar, rundunar 'yan sanda a jihar Legas ta kama wani jami'i dansanda da aka gan shi a wani bidiyo da aka wallafa a kafofin sadarwa na intanit yana karbar kudi Naira 40000 daga wani farar hula a kan titi a matsayin fansa don a bar shi ya wuce.

Kakakin rundunar, DSP Bala Elkana, ya shaida wa BBC cewa tuni aka karbi kudin daga dan-sanda aka mayar wa mutumin da aka zalunta, ana kuma yi dan-sandan shari'a.

Short presentational grey line

Haka zalika, rahotanni sun bayyana cewa an rage wa wani jami'i dansandan girma a jihar Akwa Ibom sakamakon samun sa da laifin cin zarafin wani ma'aikacin lafiya da ke hanyar zuwa aiki a lokacin dokar kullen duk da cewa ma'aikatan lafiya ba su cikin wadanda aka takaita wa zirga-zirga musamman zuwa wuraren aikinsu.

To amma 'yan Najeriya da dama na cewa matakan da hukumomin ke dauka ba su taka kara sun karya ba, idan aka yi la'akari da girman matsalar ta keta hakkin bil-Adama a fadin Najeriya.

Yayin da ya ke wa 'yan Najeriya jawabi a ranar Litinin lokacin da ya sanar da tsawaita doka a Abuja da jihohin Legas da Ogun, Shugaba Muhammadu Buhari ya isar da wani sako mai harshen damo kan rawar

jami'an tsaron kasar wajen tabbatar da ana aiki da dokar takaita zirga-zirgar.

Ya ce "hukumomin tsaro sun tashi haikan wajen tunkarar kalubalan yanayin da ake ciki tare da nuna jarumta, kuma ina yaba masu. Ina horonsu da su ci gaba da sa ido matuka, da yin tsayin daka, da kuma taka-tsantsan, ba tare da yin watsi da hakkokin tsaro ba.''

Yayin da ake ciki gaba da fuskantar annobar korona, da dokar kulle da kuma wasu lamura masu nasaba da tsaro, 'yan Najeriya da dama na nuna shakku kan yiwuwar halayyar jami'an tsaron kasar ta kyautata a nan kusa, duk da tabbacin da hukumomi ke bayarwa da kuma ikirarin kokarin kawo kyakkyawan sauyi ga yadda jami'an tsaron ke gudanar da ayyukansu.