Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Me ya sa cutar ta fi kashe bakaken fata a Amurka?
- Marubuci, Daga Aleem Maqbool
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Washington
- An wallafa
A wurin mafi yawan Amurkawa, bambancin launin fata da ake nuna wa mafi yawan mutanen da suka mutu na da alaka da bakin-cikin da suke ciki wanda bai zo musu da mamaki ba.
Biranen da ke Chicago da News Orleans da Las Vegas da kuma jihohin Maryland da kuma South Carolina na cikin wadanda suka ba da rahoton bayanai da ke da alaka da wariyar launin fata, wadanda kuma galibin wadanda suka kamu da wannan cuta bakake ne.
Wannan na iya kasancewa saboda rashin daidaiton da ake nunawa a Amurka na tsahon lokaci da muka saba da shi, sauran dalilan watakila irin abubuwan da ba a taba zato ba wadanda za a iya magancewa.
Nan bayanan mutum uku ne da wannan rikici ya shafa ta hanyoyi daban-daban - labaransu sun bayyana dalilan da ya sa bakaken Amurkawa suka fi shiga hadarin cutar.
"Yana matukar cutar da al'ummarta"
"Yar uwata Rhoda ita ce babba a cikin iyalan gidanmu. Ita ta fara zuwa kwaleji a gidanmu, ta samu digiri kuma ta ke koyarwa a makarantar gwamnati," inji Rabaran Marshall Hatch da ke Chicago.
"Irin matan nan ne masu faran-faran da mutane. Tana da kwakwalwa. Ba ta kai kanta inda ba ta je ba kuma tana da mutunci sosai."
Rabaran Marshall Hatch ya matukar shakuwa da 'yar uwar tasa, wadda yawanci ta ke masa kida a cocinsa. A ranar 4 ga watan Afrilu ne Rhoda Hatch mai shekara 73 ta mutu bayan kwashe kwana takwas tana amfani da na'urar nunfashi ta Ventilator.
Kwana biyu gabanin nan, babban abokin Rabaran Marshall Hatch, Larry Harris shi ma ya mutu, yana da shekara 62. duka su biyun Covid-19 ce sanadiyyarsu.
A takaice mutane hudu da ke da kusanci da shi duka sun mutu ta dalilinta, Abin da ya sa ya ce tana ruguza bakaken fata 'yan Amurka da ke makwabtaka da shi a West Garfiels Park in da yake zama.
"Mun yi kokarin samun kabarin da za a binne 'yar uwata a ranar Asabar, amma abin ya yi wuya sama da ko yaushe." in ji Rabaran.
"Amma kusan duk mun yi hasashen cewa duk lokacin da annoba irin wannan ta zo, za ta fi shafar mutanen da suke cikin kangin tattalin arziki."
Kamar yadda kididdiga ta bayyana, yankin West Garfield Park da bakaken fata suka fi yawa na da bambancin shekara 16 na tsahon rayuwar mutane, kasa da na yankin Chicago inda fararen fata suka fi yawa da ke tazarar mil uku kawai.
Bayanan da aka fitar sun nuna kashi 68 cikin 100 na wadanda coronavirus ta kashe bakaken fata, lokacin da su ne kashi 30 cikin 100 na adadin mutanen birnin.
Mutanen da ke zaune a yankin Rabaran Marshall Hatch suna da wahalar samun inshorar lafiya kuma suna zaune ne a gidajen da ke da cunkoson jama'a in ka kwatanta da adadin 'yan kasar baki daya.
Matasa bakaken fata sun ta wallafa cin mutuncin da jami'an tsaro ke mu su a manyan shaguna a kafafen sada zumunta, ko kuma su rika korarsu idan suka gansu da takunkumin baki da hanci.
"Ko bani da lafiya, ina zuwa aiki"
"Cikin abokan kasuwanci wadanda suke zuwa wajenmu, ba za ka taba sanin wanda ke da wata matsala ba."
Clarionta Jones mai shekara 24 daga birnin News Orleans na tsoron kamuwa da wannan cutar, amma ba ta da wani zabi mai yawa kan hakan. Tana aiki a wani kantin zamani ne kuma tana cikin mutane masu muhimmanci a wurin.
"Ni kadai ce na ke samun kudi a gidanmu, duk da cewa ba abin da kowa ya yi tsammani ba ne, kawai aka bukaci mu ba da kudin haya na watan Afrilu.
"A maganar gaskiya, idan ba ni da lafiya nakan sha magani kawai na tafi aiki. Bana son rasa kudina, ina da yara biyu. Wannan ba zabi ba ne."
Clarionta ta shaida mani cewa manajansu na cewa kada su sake su sanya safar hannu ko kuma takunkumin fuska lokacin da suke ciniki da abokan huldarsu. Tana jin bai kamata ta yi jayayya ba saboda kar ta rasa aikinta.
A kasashe da yawa na duniya muna ganin yadda ma'aikata masu muhimmanci da masu gudanar da ayyuka, ke fama da karancin albashi, a lokacin da wannan cuta ta Covid-19 ke kara yaduwa. A Amurka idan kace "karancin albashi" babu shakka kana nufin "bakar fata".
Amma Clarionta ta fadi wani abun mamaki.
"Da farko na ji ana cewa coronavirus ba ta kama baki. Ina nufin hakan na nuna babu bakaken fata a China amma lokacin da ta fara yaduwa a nan sai na ga mutane daban-daban na kamuwa."
Wannan labaran karyar ba iya New Orleans suka tsaya ba sun yadu har zuwa wasu sauran sassan kasar.
A tsakiyar watan Maris, mawakin jihar Atlanta Waka Flocka ya shiga kafar radiyo yana cewa "coronavirus ba ta kama bakake. A fadi wanda ta kama. Ba ta taba su kwata-kwata."
A wani bincike da aka gudanar, masana kiwon lafiya sun ce akwai bukatar cike gibin da ake da shi game da ilimi kan cutar.
"Tsarin bambancin launin da ake da shi ya kamata a zarga"
A matsayin kwamishina a birnin da kimanin kashi 40 cikin dari na mazaunansa bakake ne, yada labaran karya abu ne da Dakta Jeanette Kowalik ke fama da shi a kullum a wajen aikinta a Milwaukee da ke Wisconsin.
Amma sashen da ta ke aiki na ta kokarin fitar da sabbin dabarun dakile labaran karyar da ke cewa cutar ta fi alaka da matafiya 'yan kasashen ketare, Covid-19 ta tsayar da birnin da ta ke.
A makon da ya gabata an samu kimanin mutum 80 da suka kamu a birnin, kuma kaso 70 cikin dari cikinsu bakake ne," Dakta Kowalik ta shaida mani.
Ta bayyana abin da ta ke ganin shi ne dalilin da cutar ta fi kama bakake 'yan Amurka.
"Da yawa daga bakaken fata na da wata matsalar rashin lafiya da ke kisa, kamar su ciwon zuciya, ciwon siga, asma, kiba." in ji Dakta Kowalik.
Ta kuma yi magana kan wasu boyayyun hanyoyi da ake amfani da su wajen cutar da lafiyar bakaken Amurkawa, tana kafa hujja kan wasu bincike da ke nuna rayuwar mutum na raguwa kwatankwacin dadewar sinadarin Cortisol a jikinsa, wanda yake janyo tsufa da wuri, kuma hakan na da alaka ne da damuwar da mutum ke shiga saboda matsalar nuna wariya.
"Wadannan duka abubuwa ne da za su bayu zuwa banbancin launin fata, kuma wadannan manufofi ne da ake amfani da su a kasar na tsahon lokaci,"
Dakta Kowalik ta ce yadda ake cutar da bakaken Amurkawa da wadannan rikice-rikice da kuma wahalhalun da suke fuskanta wajen gwajin da coronavirus a unguwannin marasa galihu, yasa suna jin an ana nuna cewa basu da amfani.
Wani karin rahoto daga Eva Artesona
Abin da ya janyo duka wadannan abubuwan - tawagar BBC kan labaran karya
Jita-jitar da ake ta yadawa kan hanyoyin kariyar halittar bakaken fata game da Covid-19, dake yawo a kafafen sada zumunta tun karshen watan Janairu.
Labaran sun samo asali ne saboda rashin samun bullar coronavirus a Afrika a lokacin, da kuma warkewar da dan makarantar nan dan kasar Kamaru ya yi daga cutar cikin gaggawa a China.
Kan kuskure an ta wallafe-wallafe a Facebook a tsakiyar watan Faburairu, da ke ikirarin wani dan shekara 21 ya warke daga cutar "saboda kalar fatarsa".
Amma a zahirin gaskiya, babu wata shaida da ke nuna samun lafiyarsa na da alaka da launin fatarsa.
Sai dai hakan na da alaka da wani ikirari da bashi da tabbas kuma aka rika yadawa a kafafaen sada zumunta a wasu daga cikin kasashen nahiyar Afrika, da suka hadar da Najeriya, Kenya, Uganda da kuma Zambia.
Almarar kan kwayoyin kariya ta yi ta yawo a intanet a yankunan bakaken fata 'yan Amurka, inda aka rika barkwanci da su da kuma ba'a a intanet.