Coronavirus da chloroquine: Akwai hujjar cewa yana aiki?

A doctor holds tablets of chloroquine

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Chloroquine maganin zazzabin maleriya ne
    • Marubuci, Daga Jack Goodman da Christopher Giles
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check
  • An wallafa

A fadin duniya, an samu karuwar bukatar magungunan da aka saba amfani da su wajen warkar da zazzabin maleriya, don shawo kan coronavirus, yayin da gwamnatoci ke gaggawar samo magungunan sabuwar cutar.

Chloroquine, da wani magani da ake samu daga cikin sa, hydroxychloroquine, sun yi kaurin suna a 'yan kwanakin nan - duk da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na cewa babu wata shaidar cewa magungunan na aiki.

Don haka, wace shaida ake da ita yanzu ta cewa suna aiki a matsayin maganin coronavirus, kuma wa ye amfani da su?

Me muka sani game da wadannan magungunana?

Shugaba Trump ya sha yin magana kan yiwuwar hydroxychloroquine a matsayin maganin coronavirus a tarukan manema labarai a fadar White House.

A wani taron manema labarai kwanan nan, ya ce: "Me za a rasa idan aka gwada? A gwada kawai."

A wani bidiyo da a yanzu Facebook ya cire saboda saba ka'idojinta na labaran bogi, Shugaban Brazil Jair Bolsonaro ya ce hydroxychloroquine na aiki a wasu kasashen".

President Trump

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Hydroxychloroquine: "Ba zai maka illa ba? Yi amfani da shi."

An dade ana amfani da magungunan da ke dauke da chloroquine a matsayin maganin maleriya don rage zazzabi da kumburi, kuma burin shi ne magungunan za su dakushe kwayar cutar da ke janyo Covid-19.

"Da alama chloroquine na kasha coronavirus a binciken da aka yi a dakin gwaji. Likitoci sun ce akwai shaidar cewa yana taimakawa," in ji James Gallahger, wakilin BBC na bangaren lafiya.

Babu isasshiyar shaida a yanzu da ke nuna cewa sun warkar da masu fama da Covid-19.

Akwai kuma hadarin kamuwa da wasu cutukan Kaman lalacewar koda da hanta idan aka yi amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba.

"Muna bukatar manyan gwaje-gwaje a wurare daban-daban don tabbatar da karfin magungunan kan wannan cuta," in ji Kome Gbinigie na Jami'ar oxford kuma marubucin wani rahoto kan gwajin maleriya a kan Covid-19.

Sama da bincike 20 ake gudanarwa, ciki har da Amurka da Burtaniya da Sufaniya da China.

Wani minister a Burtaniya Michael Gove y ace kasarsa na "gudanar da bincike a gaggauce kan magungunan maleriya" don ganewa idan suna da wani tasiri kan Covid-19.

A Amurka, ana ci gaba da gwaje-gwaje da wasu hade-haden magunguna da suka hada da chloroquine da hydroxychloroquine da azithromycin wajen warkar da masu fama da Covid-19.

Wadanne kasashe ne suka amince a yi amfani da su?

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka, FDA, ta bayar da umarnin amfani da wadannan magungunan a wani mataki na "gaggawa" ga wasu asibitoci 'yan kalilan.

Wannan ba ya nufin cewa FDA ta ce lallai magungunan na aiki. Amma tana nufin cewa a wasu lokutan, asibitoci na iya bukatar amfani da magungunan daga cikin ma'ajiyar gwamnati don magance Covid-19.

A female scientist in a coronavirus testing lab

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Masana kimiyya na Amurka sun fara gwaji don ganin ko chloroquinezai taimaka wajen magance coronavirus

Gwamnatin Amurka ta ce wani kamfanin samar da magunguna na kasar Jamus ya bayar da hydroxychloroquine, kwatankwacin gwaji miliyan 30, ga ma'ajiyar kasar.

Wasu kasashen na amfani da wasu magungunan maleriya.

Faransa ta bai wa likitocinta damar rubuta wa marasa lafiya masu Covid-19 wadannan magungunan, amma hukumar da ke sa ido kan harkokin lafiya a kasar ta yi gargadi kan cutukan da jhakan zai iya jawowa.

Ma'aikatar lafiyar Indiya ta bayar da shawarar amafani da hydroxychloroquine a matsayin hanyar kariya ga ma'aikatan lafiya, da iyalan da suka yi mu'amala da masu dauke da cutar idan dai har likita ne zai rubuta masu.

Sai dai, hukumar bincike ta gwamnatin Indiya ta yi gargadin kan amfani da wadannan magungunan na maleriya ba a bisa ka'ida ba kuma ta ce har yanzu a matakin 'gwaji' a ke kuma ana mafani da su ne kawai a lokacin da aka shiga mawuyacin hali.

Kasashen Gabas ta Tsakiya da dama sun ba da umarnin mafani da wadannan magunguna ko kuma suna gudanar da bincike. Kasashen sun hada da Bahrain (wacce ta ce tana daya daga cikin kasshen da suka fara amfani da hydroxychloroquine kan masu Covid-19) da Maroko da Algeria da Tunisia.

Shin akwai isashhen chloroquine?

Yayin da ake nuna sha'awar amfani da wadannan magunguna wajen magance Covid-19, kasashe da yawa na fuskantar karuwar bukatarsu kuma a yanzu sun yi karanci.

Chloroquine da sauran magungunan da ake samu da jikinsa sun dade ana samunsu a shagunan sayar da magunguna musamman a kasashe masu tasowa saboda maleriya.

Wannan kuma ya kasance haka ne duk da raguwar karfinsu wajen magance maleriyar, saboda cutar na kara sauya salo kuma tan akara karfi.

Kasar Jordan ta haranta sayar da hydroxychloroquine a shagunan sayar da magunguna don hana sayensu a jibge.

Haka ma Kuwait inda ma'aikatar lafiyarta ta yanke shawarar janye duka magungunan da ke dauke da sinadarin daga shagunan sayar da magunguna masu zaman kansu kuma ta amince asibitoci da cibiyoyin lafiya ne kawai za su iya amfani da su.

Kenya ta haramta sayar da shi har sai idan mutum ya nuna takardar likita.

Indiya na daya daga cikin manyan masu samar da magungunan maleriya kuma ta sanya haramci kan fitar da su waje.

Shugaba Trump ya mika kokon bara ga Firayim MInistan Indiya Narendra Modi, da y aba Amurka damar shigar da magungunan daga Indiyar. Rahotanni sun nuna cewa Indiya na duba yiwuwar amsa wannan bukata.

Amfani da su ba a bisa ka'ida ban a iya zama hadari

A Najeriya, ana amfani da kwayoyin magani masu dauke da chloroquine don cutar maleriya, duk da cewa a shekarar 2005 aka haramta amfani da shi saboda yadda karfinsa ya ragu wajen kawar da zazzabin maleriyar.

A scientist examines test samples

Asalin hoton, Reuters

Labarin wani bincike da aka yi a China a watan Fabrairu kan amfani da chloroquine kan coronavirus ya jawo muhawara mai karfi a Legas, don haka mutane suka fara sayensa suna jibgewa.

Biyo bayan kalaman Mista Trump kan matsayin magungunan wajen magance coronavirus, abin ya kara ta'azzara kuma magungunan sun kare kaf a shaguna. Amma hukumar kula da yaduwar cutuka ta Najeriya ta shaida wa mutane cewa su daina shan shi. "WHO ba ta amince da amfani da chloroquine wajen magance #Covid-19 ba."

Wakilin BBC a Legas, Daniel Semeniworima y ace mutane sun yi watsi da shawarar kuma wannan na janyo masu wasu cutukan masu muni.

Hukumomi a jihar legas sun ce an samu mutanen da suka sha chloroquine ya yi masu yawa har ya yi masu illa a jihar.