Tsuntsayen daji na yada cutar mura

Tsuntsaye masu yin Hijira

Asalin hoton, science photo library

Bayanan hoto, Tsuntsaye masu yin Hijira
An wallafa

Tsuntsayen da ke yin kaura za su iya yada cututtukan da za su haddasa murar tsuntsaye a duniya - a cewar masana kimiyya.

Sun yi gargadin cewa, annobar murar tsuntsayen za ta zamo ruwan dare nan gaba a kasashen da ba su zama cikin shirin ko ta kwana.

A cewar wasu kwararrun masu bincike na kasar Netherlands, ta yiwu wasu tsuntsaye da suka yi wo Kaura daga Rasha suka yada wata kwayar cutar murar tsuntsaye da ta riski wasu agwagi a wata gonar su a Brittaniya a bara.

Suka ce, hadarin da Kwayar ga bil-adam kadan ne, to amma kamata ya yi a rinka sa ido kan tsuntsaye na daji dake yin kaura.

A bara ne aka samu nau'in murar tsuntsayen H5N8 a Rasha da Gabashin Asia da Amurka ta Arewa da wasu kasashe 4 na Turai da suka hada da Brittaniya.

Cutar ta sanya an kashe miliyoyin kaji.

A Brittaniya, agwagi sun kamu da kwayar cutar a wani gidan kiwon kaji dake Driffield, a Yorkshire.

Annobar murar tsuntsayen da ta barke a wannan makon a Hampshire nau'in H7N7 ce, kuma ba ta da wata babbar illa.

Masana kimiyya a Cibiyar kiwon lafiya ta Erasmus dake Rotterdam a Netherlands sun ce samun kwayar cutar ta murar tsuntsaye nau'in H5 a tsakanin tsuntsayen dake Kaura daga Rasha da wasu cututtukan da aka gano daga wasu tsuntsayen na daji da kaji, abin damuwa ne matuka.

Kungiyar wasu kwararrun likitoci a karkashin jagorancin Dr Ron Fouchier sun rubuta a mujallar kimiyya cewar "nan gaba za a iya samun karuwar annobar murar tsuntsayen musamman a wasu kasashen da ba su zama cikin shirin ko-ta-kwana.