Murar tsuntsaye na kara bazuwa a Nigeria

Asalin hoton, AFP
An wallafa
Gwamnatin Najeriya ta ce cutar murar tsuntsaye ta bazu zuwa jihohi 16 na kasar.
A wajen wani taron manema labarai da ya kira ranar Litinin a Abuja, Ministan lafiya na kasar, Dr. Haliru Alhassan, ya ce har yanzu ba a samu wani mutum da ya kamu da cutar a kasar ba.
Sai dai kuma rahotanni daga sassa daban-daban na Najeriyar sun nuna cewa cutar ta hallaka dubban kaji a kasar.
A farkon watan Janairu ne cutar ta bulla a kasar, inda ta fara bulla a jihohin Kano da kuma Lagos.







