An fitar da sabbin ka'idojjin maganin cutar AIDS

Hukumar lafiya ta Duniya, watauWHO, ta bullo da wasu sabbin ka'idojin maganin cutar dake karya garkuwar jiki watau HIV AIDS ko CIDA , da ta ce zasu taimaka wajen kare miliyoyin mutane daga mutawa sanadiyyar cutar.
Hukumar ta na son a rika bayar da wata kwayar magani daya da ta kunshi wasu kwayoyi uku ga marassa lafiyar da suke a matakin farko na kamuwa da cutar da a lokacin garkuwar jikinsu tana da karfi.
Sabon tsarin zai sa a samu karin mutanen da suke samun magani da hakan zai rage yawan wadanda ke dauke da kwayar cutar da za ta tsananta har ta kai matsayin cikakkiyar cutar ta kanjamau,wanda a tsarin da ake bi a yanzu yawan mutanen da ke dauke da kwayar cutar da zata kai ga cikakken matsayin nata zai tashi daga miliyan 16 zuwa 26 a kasashe masu tasowa.
Ana kaddamar da sabon tsarin ne a wani taron yaki da cutar na duniya a Malaysia.







