Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
...Daga Bakin Mai Ita tare da Mika'il Bin Hassan
Latsa hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon
Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.
A wannan kashi na 86 ɗin, BBC ta tattauna da Mika'il Bin Hassan wanda tsohon ɗan wasan Kannywood ne, inda watakila wasu masu kallo za su ce sun daɗe ba su ganshi ba.
An haife shi kimanin shekara 45 da suka wuce kuma shi asalin mutumin Ƙaramar Hukumar Mai Gatari ne ta ce Jihar Jigawa amma an haife shi kuma ya girma a Kano.
Ya soma harkar fina-finai ne a jami'a inda ya fara da wasan daɓe lokacin da suke da wata ƙungiya mai suna 'Galaxy Entertainment Club'.
Mika'il ɗan wasa ne marubuci ne mai sarrafa kemara ne kuma darakta ne. Fim ɗin da ya fito da Mika'il shi ne Furuci kuma ya ce tsawon rayuwarsa ya yi fim kimanin 50 zuwa 70.
Sai kuma fina-finan da ya bayar da umarni ba su fi 20 ba.