Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Annabi ne ya fara Maulidi saboda haka ba bidi'a ba ne - Sheikh Halliru Maraya
Sheikh Halliru Maraya, malamin addini a Kaduna ya ce Annabi Muhammad SAW ne ya fara yin nuni ga murnar ranar haihuwarsa da ake kira Maulidi.
"An tambayi Annabi Muhammad SAW dangane da azumin Litinin da ya ke yi. Sai annabin ya ce ranar ne aka haife ni", in ji Sheikh Halliru.
Malamin ya kara da cewa kamata ya yi Musulmi su girmama watan na Maulidi kasancewar a watan ne Allah ubangiji ya bai wa duniya kyautar da babu irinta ga duniya wato haihuwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Abubuwan da ya kamata a yi lokacin Maulidi:
Malamin ya lissafa wasu abubuwan da ya kamata a yi a lokacin Maulidi amma wadanda ba su saba da shari'a ba.
- Taro domin nuna mu'ujizar Annabi da halayensa domin yin koyi da shi
- Yin azumi
- Sada zumunci
- Ziyartar marasa lafiya a asibiti
- Yin sadaKa
- Ciyar da jama'a
Sai dai malamin ya ce bai kamata a yi duk abin da shari'a ba ta amince da shi ba kamar cakuɗuwar maza da mata, ihuce-ihuce, shaye-shaye da dai sauransu.
Rabi'ul Awwal, wata ne na kalandar musulunci da wani ɓangaren musulmin duniya ke bikin zagayowar ranar da aka haifi manzon Allah, Annabi Muhammad S.A.W.
Musulmai da dama sun yi amannar cewa a watan Rabi'ul Awwal, aka haifi Annabi Muhammadu (SAW).
Sai dai ba dukkanin Musulmi ne ke bikin haihuwar Ma'aiki SAW, saboda sabanin fahimta. Akwai wani ɓangare na malamai da ke nuna rashin dacewar gudanar da bikin maulidi.