Mummunar gobarar daji da ke mamaye garuruwa a Turkiyya
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A ƙalla mutum takwas ne suka mutu a wasu gobarar daji da ta mamayi garuruwa a kudancin Turkiyya.
Gobarar tana ta ci ganga-ganaga a yankunan da ke kusa da gaɓar Bahar rum inda ta tilasta wa mutane tserewa.
An shafe kwana shida wutar na ci gaba da ci, dalilin da ya sa hakan ya zamo mafi muni da Turkiyya ta gani cikin gwamman shekaru.