Ba a samu kuskure ba daga VAR a wasanin karshe a Premier League, kafin a kada kuri'a ko ya dace a soke fasahar ko a ci gaba da amfani da ita a kakar 2004/25.
Wasu jami'ai ne suka bibiyi wasannin da aka buga ranar Lahadi 19 ga watan Mayu, musammam hukuncin da VAR ta gudanar, inda ba a samu kuskure ba.
Sai dai sun ce an samu kuskure a yanke hukunci daga rafli karo shida, ciki har da na Tomas Soucek ya ci Manchester City da hannu, yayin da VAR ta ci an sa hannu a karawar da City ta ci 3-1.
Haka kuma jami'an sun ce ya dace da aka karbi kwallon da Gabriel Martinelli ya ci Everton a wasan da Gunners ta yi nasara 2-1, wadda tun farko aka ce ya saka hannu.
Ranar 6 ga wwatan Yuni za a kada kuri'ar ko ya dace a ci gaba da amfani da VAR ko kuma a soke ta.
Ana sa ran samu kungiyoyi 14 daga 20 su amince ko akasin hakan kafin a zartar hukunci.
Sai dai ƙungiyoyin Premier sun bukaci a dawo da fasahar kula da satar gida a 2024/25.