SUBSTITUTION, Man City 0-2 Man Utd
Manchester City ta yi canji
Manchester City ta samu kwana kuma Kevin de Bruyne ne ya buga, amma Andre Onana ya fitar da ita.
Shi kenan De Bruyne ya fita an canja shi da Julian Alvarez.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a fagen wasanni a fadin duniya a wannan lokacin.
Mohammed Abdu
Manchester City ta yi canji
Manchester City ta samu kwana kuma Kevin de Bruyne ne ya buga, amma Andre Onana ya fitar da ita.
Shi kenan De Bruyne ya fita an canja shi da Julian Alvarez.
An buga ƙwwallo ya bugi turke
Erling Haaland baya taka rawar gani, amma ya samu wata dama ya buga ƙwallo sai dai ya bugi turke.
Dama mai kyau da City ta samu da aka koma zagaye na biyu.
Manchester United na neman fenariti, bayan da Scott McTominay amma irin yanayi ɗaya ne da ba a bai wa Manchester City ba tun kan hutu.
Pep Guardiola ya yi canji, wanda ya saka Manuel Akanji da Jeremy Doku, wadanda suka canji Mateo Kovacic da kuma Nathan Ake.
Hull City ce ƙungiyar farko da ta ci wasa a zagayen farko aka soke da aka koma fili a wasan karshe a FA Cup shekara 10 da ta gabata.
Hull City ce ta fara cin Arsenal kwallo biyu daga baya aka farke.
Wannan shi ne daya daga wasa mafi kayatarwa da Ten Hag ya ja ragamar United a matakin kociyan Manchester United.
Za su huta minti 15 sannan a koma zagaye na biyu, ko United za ta dauki FA Cup na 13 jimilla ko kuma City za ta dauki na takwas a tarihi?
Wannan ce taswirar yadda ƴan wasan Manchester United, Alejandro Garnacho da Kobbie Mainoo suka samu damar cin ƙwallaye.
Manchester United ta dage sai ta lashe FA Cup na bana, wadda ta kara na biyu a raga ta hannun Kobbie Mainoo.
Manchester United tana nuna da gaske take a karawar.
Manchester United ta zura kwallo a raga amma an soke, bayan da aka ce Garnacho ya yi satar gida.
Alejandro Garnacho ya ci ƙwallon da ya bai wa United damar shiga gaban Manchester City
Ɗan wasan Arsenal, Jorginho da mai tsaron ragar Tottenham Guglielmo Vicario suna cikin ƴan ƙwallo 30 da Italiya ta bayyana na ƙwarya-ƙwarya domin Euro 2024.
Sai dai ba a gayyaci ɗan wasan Lazio, Ciro Immobile da Marco Verratti, wanda ya koma ƙungiyar Qatar, Al-Arabi daga Paris St-Germain cikin Satumba ba..
Ko Manchester City za ta lashe FA Cup na biyu a jere na takwas jimilla ko kuma Manchester United za ta dauki na 13 a tarihi.
An fara wasan karshe a Wembley
We're under way in the FA Cup final at Wembley.
Manchester City ta canja yan wasa uku daga wadanda suka buga mata wasan karshe da ta doke West Ham United 3-1 ranar 19 ga watan Mayyu.
Inda ta saka John Stones da Nathan Ake ada kuma Mateo Kovacic, yayin da Ruben Dias da Manuel Akanji da kkuma Jeremy Doku ke benci.
Ƴan Man City 11 da za a fara wasa da su a cikin fili:Ortega, Walker, Stones, Ake, Gvardiol, Rodrigo, Kovacic, De Bruyne, Bernardo, Foden, Haaland.
Masu jiran kar-ta-kwana: Carson, Dias, Grealish, Doku, Alvarez, Akanji, Nunes, Bobb, Lewis.
The players are in the buildingpublished at 13:5713:57
Man City v Man Utd (15:00 BST)
There's just over an hour to go until kick-off and players from both sides are making their way into the dressing rooms.
It's fair to say Manchester City players are in casual clothing while the Manchester United players are suited and booted.
Mai rike da kofin Champions League na mata, Barcelona za ta buga wasan karshe da Lyon ranar Asabar a filin wasa na Bilbao da ake kira San Mames Stadium.
Wannan dama ce ga Barcelona ta lashe kofin karo na uku, hakan zai sa ta zama ta uku da ta dauki Champions League na mata karo uku.
Ita kuwa Lyon tana fatan kara mamaye gasar zakarun Turai, wadda ke shirin lashe na tara jimilla.
Barcelona ce ta fitar da Chelsea a zagayen daf da karshe, yayin da Lyon ta kai wasan karshe bayan doke Paris St-Germain.
Wannan shi ne karo na hudu a jere kuma na biyar a kaka shida da Barcelona ta kai zagayen karshe, ita kuwa Lyon za ta buga wasan karshe karo na 11.