Bayern Munich ta dauki Kompany sabon kociyanta

An wallafa

Kociyan Burnley, Vincent Kompany ya amince ya zama sabon wanda zai horar da Bayern Munich.

Ƙungiyar Jamus ta yi zawarcin Kompany, bayan da ta tuntuɓi kociyoyi da yawa, wadanda ba su amince su maye gurbin Thomas Tuchel ba.

Rahotanni da yawa na cewa Kompany ya amince da ƙunshin ƴarjejeniyar da aka gabatar masa da za ta kare a karshen kakar 2027.

Sai dai mataimakin Kompany a Burnley, Craig Bellamy ba zai bi kociyan zuwa Allianze Arena ba, amma Floribert Ngalula da Bram Geers za su taimaka masa aikin.

Bayern Munich ta tuntubi kociyan Bayern Leverkusen, Xabi Alonso da Julian Nagelsman, wanda ya taɓa jan ragamarta, wanda yanzu yake tawagar Jamus da na Austria, Ralf Rangnick duk ba su amince da tayin ba.

Tuchel ya tattauna da Bayern Munich a cikin watan Mayu, domin ya ci gaba da jan ragamar ƙungiyar, amma ba su kai ga cimma matsaya ba.

Haka kuma Bayern ta nemi mai horarwar dake jin yaren Jamusanci, inda Kompany ya taba taka leda a Hamburg ya iya yaren.

Tsohon ƙyaftin ɗin Manchester City ya taka rawar gani a aikin koci a Anderlecht da Burnley, wanda ya lashe Championship da kai ƙungiyar Premier League a bara.

Sai dai ya saka ƙokarin da ƙungiyar ya kamata ta ci gaba da taka leda a babbar gasar tamaula ta Ingila, wadda ta yi ta biyun karshe, za ta koma Championship a badi.

Wanda ya lashe kofin Premier League hudu ya zama mai horar da Anderlecht a 2020, wadda ya fara yiwa wasa daga nan ya koma Turf Moor da aiki.