Ko Chelsea za ta taka rawar gani a kakar bana kuwa?

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Ra'ayoyinku da kuke tafka muhawa a BBC Hausa Facebook

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  2. Dani Alves ya koma Pumas UNAM ta Mexico

    Dani Alves ya saka hannu kan kwantiragin komawa kungiyar kwallon kafa ta Mexico mai suna Pumas UNAM.

    Dan kwallon Brazil mai tsaron baya, zai koma taka leda a babbar gasar Mexico, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a Barcelona a karo na biyu da ya koma Camp Nou.

    Mai shekara 39 ya sake zuwa Barcelona a karo na biyu a Nuwambar 2021, shekara biyar bayan da ya bar Camp Nou zuwa Juventus.

    Dani Alves

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Raphinha ya fara El Clasico da cin Real Madrid kwallo

    Raphinha, sabon dan kwallon da Barcelona ta dauka a bana, shi ne ya ci Real Madrid a wasan sada zumunta a Las Vegas din Amurka.

    Karawar ta El Clasico, ita ce ta farko da kungiyoyin Sifaniya suka fara a bana tun kan fara kakar tamaula da za a fara a cikin watan Agusta.

    Dan kwallon tawagar Brazil, ya koma kungiyar Camp Nou daga Leeds United kan kwantiragin da ta kai fam miliyan 55 a farkon watan nan.

    Kawo yanzu dan wasan ya ci wa Barcelona kwallo biyu kenan a wasannin atisayen da take yi a Amurka.

    Raphinha ya zura kwallo a ragar Real Madrid a minti na 27 a wasan farko da Robert Lewandowski ya yi wa sabuwar kungiyarsa Barcelona tamaula.

    Real Madrid, wadda ta yi karawar ba tare da Karim Benzema ba, ba ta buga kwallo ya nufi raga ba ko sau daya a fafatawar.

    Raphinha

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Ko Chelsea za ta fuskanci kalubale a kakar bana?

    Kungiyar Chelsea ta buga wasannin sada zumunta a Amurka, inda ta doke Club America ta Mexico da ci 2-1 daga baya ta yi rashin nasara a hannun Charlotte FC a bugun fenariti, sannan Arsenal ta casa ta 4-0.

    Sai dai Thomas Tuchel ya ce Chelsea ta cancanci rashin nasara a hannun Arsenal ya kuma tuhumi 'yan wasa kan kwazon da suka sa a fafatawar.

    Thomas Tuchel

    Asalin hoton, Reuters

  5. Haaland ya ci Bayern a wasansa na farko a Manchester City

    Sabon dan kwallon da Manchester City ta saya a bana, Erling Haaland ya fara ci mata kwallo a wasan da ta doke Bayern Munich 1-0 a Amurka.

    Kungiyoyin biyu sun buga wasan sada zumunta a tsakaninsu domin gwada sabbin 'yan kwallon da suka saya, don shirin tunkarar kakar da za a fara cikin Agusta.

    Sau biyu ana dakatar da wasan, sakamakon karar tsawa da ta auku a lokacin tsaka da fafatawar a Wisconsin.

    Haaland, wanda ya koma City kan fam miliyan 51.2 daga Borussia Dortmund, ya ci kwallon a minti na 12 da fara karawar ta sada zumunta.

    Erling Haaland

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Senegal ta bi sahun Tunisia da Najeriya a jerin tawagar kwallon kafa ta Afirka da ta lashe kyautar wadda tafi taka rawar gani a nahiyar karo hudu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. West Ham ta amince za ta dauki Scamacca daga Sassuola

    West Ham ta amince da farashin fam miliyan 30.5 daga Sassuolo kan daukar dan wasa Gianluca Scamacca.

    Dan kwallon tawagar Italiya, mai shekara 23, zai zama na hudu da West Ham za ta dauka a bana.

    Kociyan West Ham, David Moyes na ta kokarin kara karfin gurbin masu zura kwallaye a raga, yana kuma fatan daukar dan wasan Chelsea, Armando Broja.

    Scamacca shi ne na biyu a yawan cin kwallaye a gasar Serie A mai 16 a raga a wasa 36 a kakar da ta wuce.

    Gianluca Scamacca

    Asalin hoton, Getty Images

  8. An yi wa dan Alin ba ta isarka ajo a Marabar 'Nyanya

    Ranar Lahadi gidan wasa na Idris Bambarewa da ke karamar hukumar Karo a jihar Nasarawa, Najeriya ya karrama Dan Alin ba ta isarka a damben safe.

    Kudawa da yawa sun halarci damben don ganin sun fitar da Dan Ali kunya, inda aka yi dambe da dama.

    Ga jerin wasannin da aka fafata:

    To bari mu fara da damben manya da aka yi tsakanin Shagon Autan dan Bunza daga Jamus da Ilele shagon Garkuwan mai caji daga Kudu.

    Damben ya kayatar a turmi biyu da suka yi, sai dai ba kisa.

    Yalo Dan Zuru Guramada ya dambata da Abba Dogon Sisco daga Kudu, inda suka yi turmi uku ba kisa aka raba su.

    Shi kuwa Koronabirus Shagon dan Alin bata isarka daga Kudu mai biki, wasa biyu ya buga, inda ya fara doke Dogon mai masaukin baki Guramada, ya kuma yi turmi daya da Shagon Tanko na Tunga shima Guramada amma ba kisa.

    Damben Aljanin Arewa da Biyun Sama’ila daga Kudu tumi uku suka yi, ba a fidda gwani ba.

    Dan Dabar Autan dan Bunza daga Arewa ya doke Shagon mai masauki Guramada, Bahagon Yalo dan Zuru gudamada ya yi nasara a kann Dogon Shagon Gwagwarwa daga Kudu.

    Sai wasan da Garkuwan Autan dan Bunza daga Arewa ya buge Shagon Champion daga Kudu a dan kankanin lokaci.

    Bayanan bidiyo, Damben Ilele da Autan dan Bunza ajon Dan Ali
  9. 'Yar Najeriya Tobi Amusan ta kafa tahiri a gasar tseren duniya

    'Yar Najeriya Tobi Amusan ta lashe kyautar zinariya a gasar mita 100 ta tseren mata ta Duniya da ake gudanarwa a Amurka.

    'Yar wasan mai shekara 25 ta kafa tarihin ne a zagayen kusa da karshe inda ta kai layi cikin minti 12 da dakika 12.

    A baya dai Ba'amurkiya Kendra Harrison ta kafa irin wannan tarihi a 2016 inda ta kai layi a minti 12 da dakika 20.

    Amusan ta fi yin gudu a zagayen karshe ( ta yi minti 12 da dakika shida), amma ba a amince da nasararta ba saboda iska mai karfi da ke kara mata gudu.

    Tobi Amusan

    Asalin hoton, Getty Images

  10. Barkanmu da kasancewa

    Jama'a barkanmu da kasancewa a shirin labaran wasanni da yadda kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ke gudana a rana irin ta yau.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper zan gabatar da shirin da fatan za ku kasance da BBC Hausa a koda yaushe.

    Za ku iya bayar da gudunmuwa ko tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko a Twitter.