West Ham ta amince za ta dauki Scamacca daga Sassuola

Asalin hoton, PA Media
West Ham ta amince da farashin fam miliyan 30.5 daga Sassuolo kan daukar dan wasa Gianluca Scamacca.
Dan kwallon tawagar Italiya, mai shekara 23, zai zama na hudu da West Ham za ta dauka a bana.
Kociyan West Ham, David Moyes na ta kokarin kara karfin gurbin masu zura kwallaye a raga, yana kuma fatan daukar dan wasan Chelsea, Armando Broja.
Scamacca shi ne na biyu a yawan cin kwallaye a gasar Serie A mai 16 a raga a wasa 36 a kakar da ta wuce.
Ya fara yi wa tawagar Italiya tamaula a watan Satumba, wanda kawo yanzu ya buga wasa bakwai, amma bai ci mata kwallo ba kawo yanzu.
'Yan wasan da West Ham ta dauka a kakar nan sun hada da Nayef Aguerd da Alphonse Areola da kuma Flynn Downes.
Haka kuma kungiyar ta birnin Landan na fatan daukar Jesse Lingard, wanda ya ci mata kwallo tara a karawa 16 a Premier League a wasannin aro da ya yi mata.
Manchester United ce ta bai wa West Ham aron Lingard a 2020-21.
To sai dai kuma Lingard, dan kwallon Ingila ya zabi ya koma Nottingham Forest, wadda za ta fara buga Premier a bana, bayan da kwantiraginsa ya kare a karshen kakar da aka kammala a Old Trafford.











