Bayern Munich ta lashe Champions League

Wannan shafi na kawo muku yadda ake fafatawa kai-tsaye tsakanin Bayern Munich da PSG a wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai ta Champions League na 2019-2020.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. An take wasa, PSG 0-0 Bayern Munich

    Karon farko kenan da PSG ke taɓa ƙwallo a wasan ƙarshe na Champions League kuma ta biyar daga ƙasar Faransa.

  2. Ko Robert Lewandowski zai lashe kyautar Balon D'or?

    Lewandowski

    Asalin hoton, Getty Images

    Robert Lewandowski ya ci ƙwallo a wasa tara a jere a Champions League, wanda Cristiano Ronaldo kawai ya fi shi zira ƙwallaye a wasanni a jere - ƙwallonsa 55 a duka gasanni a kakar bana.

    Game da ko Lewandowski zai lashe Balon D'or, Owen Hargreaves; tsohon ɗan wasan tsakiyar Bayern ya ce: " Ƙwarai kuwa. Ina ganin wanda shi ma zai shiga rukunin shi ne Kylian Mbappe."

  3. Aiki ga me ƙare ka!

    Bayern Munich ce ƙungiya ta farko da ta taɓa lashe dukkanin wasanta 10 na farko a Champions League.

    Aiki ga me ƙare ka!

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Ronaldinho, Beckam, Ibrahimovic ba su kai PSG ko'ina ba

    Mbappe 23 Neymar 16 Di Maria 11

    Asalin hoton, Getty Images

    Ku tuna zaratan 'yan ƙwallo da suka haɗa da Ronaldinho David Beckam da Zlatan Ibrahimovic duka sun saka rigar nan mai launin shuɗi da ja amma dukkaninsu babu wanda ya iya kai PSG ko da wasan kusa da na ƙarshe.

    Amma yanzu alamu sun nuna cewa Neymar da Mbappe da Angel Di Maria za su iya taimaka wa ƙungiyar cimma abin da ta kasa cikin shekara 50 da kafa ta.

    Ƙwallayen da suka ci a Ligue 1 da Champions League na bana

    • Mbappe 23
    • Neymar 16
    • Di Maria 11
  5. Yadda tsayuwar ƙungiyoyi za ta kasance, PSG vs Bayern Munich

    Kowacce ƙungiya sauyi ɗaya ta yi daga wasan da suka buga na semi fayinal.

    Golan PSG Keylor Navas ya warke daga jinyar da ya yi a bayan cinyarsa kuma zai maye gurbin Sergio Rico.

    Bayern Munich ta yi sauyi a karon farko tun bayan cigaba da wasanni a watan Yuni.

    Kingsley Coman ya maye gurbin Ivan Perisic a gefen hagu.

    PSG

    Asalin hoton, BBC Sport

    Bayern

    Asalin hoton, BBC Sport

  6. Wasa ne na musamman - Kocin Bayern, Hansi Flick, PSG vs Bayern Munich

    Hansi Flick

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayern Munich ta shirya tsaf domin yin "duk mai yiwuwa" ta kammala wannan kakar cikin salo na musamman ta hanyar lashe Champions League, in ji kocin ƙungiyar, Hansi Flick.

    Zakarun Jamus ba sa yi wa sauran ƙungiyoyi da wasa a baki ɗayan kakar wasa ta 2019-20 kuma ba abin mamaki ba ne idan suka jinjina kofin nan a birnin Lisbon a wannan dare.

    Idan har ta yi nasarar lashe kofin na Champions League a karon farko tun shekarar 2013, Bayern za ta ɗaga kofin Turai da na Bundesliga a kaka guda karon farko kenan a tarihinta.

    "Wasa ne na musamman," in Flick, wanda ƙungiyar tasa ta lashe dukkanin wasa 10 a jere a Champions League na bana - babu ƙungiyar da cinye ta.

  7. Tarihi ba ya tare da PSG a yau amma za ta iya kafa sabo, PSG vs Bayern Munich

    PSG

    Asalin hoton, Getty Images

    Wannan ne karon farko da PSG take zuwa wasan ƙarshe a gasar ta Champions League kuma wannan zubin 'yan wasan na mai horaswa Thomas Tuchel, su ne na 41 da suka samu halartar gasar a tarihin ƙungiyar.

    Sai dai fa ƙungiyoyi shida na baya-bayan nan da suka taɓa zuwa wasan ƙarshe a karon farko ba su kai labari ba.

    Ƙungiya ta ƙarshe da ta je wasan ƙarshe a karon farko kuma ta sha kashi ita ce Borussia Dortmund, inda Juventus ta doke ta a 1997.

  8. Barkanmu da yammacin wasan ƙarshe na Champions League, PSG vs Bayern Munich

    Umar Mikail ke muku maraba da shigowa shafin sharhi kan wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai ta Champions League kai-tsaye tsakanin Bayern Munich da Paris Saint-Germain.

    Ku biyo mu don ganin yadda za a ɓarje gumi.