Real Madrid ta bai wa Barcelona tazarar maki biyu

Wannan shafi ne kai tsaye da ke dauke da labarin wasanni da ake fafatawa a karshen mako musamman wasan Espanyol da Real Madrid.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Canjin Espanyol

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  2. Guardiola ya ce Man City za ta yi wa Liverpool tarbar girma

    Pep Guardiola ya ce 'yan wasan Manchester City za su yi wa na Liverpool wacce ta lashe kofin Premier League tarbar girma idan za su kara a Etihad ranar Alhamis.

    Shi ne wasan farko da Liverpool za ta buga a Premier League, tun bayan da ta lashe kofin a karon farko tun bayan shekara 30.

    Liverpool ta ci kofin bana saura wasa bakwai-bakawi a karkare kakar bana da tazarar maki 23 tsakaninta da Manchester City.

    Kuma nasarar da Chelsea ta doke Manchester City da ci 2-1 a gasar Premier League a Stamford Bridge ya sa kungiyar ta Anfield ta zama zakara a shekarar nan.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Espanyol 0-1 Real Madrid

    Kwazon da Benzema ke yi wajen cin kwallo da bayar wa a zura a raga.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Ceballos ya kai Arsenal wasan daf da karshe a FA Cup

    Dani Ceballos ne ya ci wa Arsenal kwallo na biyu da ya kai kungiyar wasan daf da karshe a FA Cup, bayan doke Sheffield United 2-1 ranar Lahadi.

    Gunners ce ta fara cin kwallo ta hannun Nicolas Pepe a bugun fenariti, bayan da Chris Basham ya yi wa Alexandre Lacazette keta a da'ira ta 18..

    • Aubameyang ba ya da tabbas a Arsenal
    • David Luiz zai ci gaba da zama a Arsenal shekara daya

    Daga baya ne mai masukin baki, Sheffield ta farke ta hannun McGoldrick saura minti uku a tashi daga karawar.

    Bayan da alkalin wasa ya kara lokaci ne Arsenal ta ci kwallo na biyu ta hannun Ceballos wanda ke buga wa kungiyar wasannin aro.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, Getty Images

  5. An koma zagaye na biyu - Espanyol 0-1 Real Madrid

    Shin ko Real Madrid za ta tsira da maki uku ko kuwa?

    Ko canjaras aka yi Real tana ta daya a teburi, illa dai kar ta bari a doke ta a Espanyol.

  6. Ra'ayinku a BBC Hausa Twitter

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Espanyol 0-1 Real Madrid

    An je hutu.

  8. Espanyol 0-1 Real Madrid

    An yi karin lokaci daf ake a je hutun rabin lokaci.

  9. An ci kwallo - Espanyol 0-1 Real Madrid, Casemiro

    Kwallo ce aka buga wa Benzema shi kuma yana tare da mai tsaron baya sai ya sa dunduniya nan da nan ta je wajen Casemiro shi kuma bai ba ta lokaci ba ya zura a raga.

    Real Madrid ta samu maki uku kawo yanzu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. Espanyol 0-0 Real Madrid

    Real Madrid ta samu kwallo ta yi kokarin sai da buga ta shiga ragar Espanyol an kuma yi runtsi amma daga baya gola Lopez ya sa hannu ta yi waje zuwa kwana.

  11. Espanyol 0-0 Real Madrid

    Dama mafi kyau da Real Madrid ta samu daga Karim Benzema ya buga kwallo zuwa raga amma mai tsaron raga Diego Lopez ya rike gam..

  12. Espanyol 0-0 Real Madrid

    Espanyol ta ci kwallo sau daya a minti na 45 kan kafin hutu a wasa 13 da ta yi da Real Madrid a bara shi ne da suka tashi 4-2.

  13. Espanyol 0-0 Real Madrid

    Toni Kroos ya yi bugun tazara zuwa cikin ragar Espanyol, inda Sergio Ramos ya a kai amma ta je wajen gola kai tsaye.

  14. Katin gargadi - Espanyol 0-0 Real Madrid

    Katin gargadi na farko da aka yi wa dan wasan Espanyol, Marc Roca bayan da ya yi wa Eden Hazard keta.

  15. Espanyol 0-0 Real Madrid

    Dan kwallon Espanyol, Wu Lei yana mamaki da alakalin wasa bai bayar da bugun tazara a kusa da da'iara ta Real ba, bayan da ya hada jiki da Ramos ya fadi.

  16. Espanyol 0-0 Real Madrid

    Espanyol na samun damarmaki a wannan karawar ta nuna ita ma maki ukun take bukata kamar yadda Real ke fatan samu a Espanyol.

    Wu Lei yana tare da kwallo a kusa da da'ira ya buga amma ta yi sama ta fita waje,

  17. Espanyol 0-0 Real Madrid

  18. Espanyol 0-0 Real Madrid

    Idan aka yi canjaras Real Madrid za ta koma ta daya a kan teburi saboda nasarar da bta yi a El Clasico.

  19. Espanyol 0-0 Real Madrid

    Kyaftin din Real Madrid Sergio Ramos ya samu dama mai kyau da aka bugo masa kwallo ya sa kai kuma yana daf da ragar Espanyol amma ta yi sama ta fita waje.

    Ramos ya kama kai ya durkusa kasa ya san dama ce mai kyau ya barar.

  20. Espanyol 0-0 Real Madrid

    Espanyol ta kusan shiga gaba kuma Wu Lei ya buga kwallo an kuma tare kwallon da ya buga.