Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Real Madrid ta koma matakinta na daya a teburin La Liga

Wannan shafi ne da ke dauke da labarin wasanni da karawar da Real Madrid ke karbar bakuncin Real Mallorca da sanar da ku wainar da ake toyawa a fanni wasanni.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Real Madrid 0-0 Mallorca

    Real Madrid na kara sa kaimi inda Karim Benzema ya buga kwallo kusa da mai tsaron aga amma ya buge ta haka ma Gareth Ball ya buga daga wajen gidan Mallorca.

  2. Real Madrid 0-0 Mallorca

    Vinicius Jr ya dauki kwallo ya kuma bai wa Eden Hazard a cikin da'ira ta 18 sai dai dan wasan na Belgium ya ji matsi ya koma da baya da kwallon.

  3. Real Madrid 0-0 Mallorca

    Babu dai wani gagarumin abin da ya farau illa dai Real Madrid ke rike kwallo kamar yadda ta saba yi.

  4. Real Madrid 0-0 Mallorca

    Madrid tana buga wasan a filin da take atisaye Estadio Alfredo di Stefano, bayan da ake gyaran Santiago Bernabeu.

  5. Real Madrid da Mallorca

    An take kwallo.

    Ko Real za ta koma ta daya a kan teburin La Liga?

    Sai na da minti 90 za mu san wannan amsar.

  6. Real Madrid da Mallorca

    'Yan wasa na cikin fili yanzu za a sa wasa.

  7. Wadanda za su taka leda Real Madrid da Real Mallorca

  8. Ra'ayinku ta BBC Hausa Twitter

  9. Iago Aspas Juncal ya ci kwallo 100 a gasar La Liga

  10. Real Madrid da Real Mallorca

  11. Ra'ayin da kuke aiko wa ta BBC Hausa Twitter

  12. Real Madrid da Real Mallorca

  13. Wadanda za su buga wa Mallorca

  14. Ra'ayin da kuke aikowa ta BBC HAusa Twitter

  15. Real Madrid da Real Mallorca

  16. Wadanda za su buga Real Madrid

  17. Wasannin da aka buga da wanda ya rage ranar Laraba

  18. Real Madrid da Real Mallorca

    Wadanda suke kasan teburi a gasar La Liga da ake kokarin karkare wasannin mako na 31.

  19. Real Madrid da Real Mallorca

    Barcelona ce ke jan ragamar teburi, bayan da ta buga wasa 31, ita kuwa Real ta yi 30, Za ta kara da Real Mallorca.