Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Real Madrid ta koma matakinta na daya a teburin La Liga

Wannan shafi ne da ke dauke da labarin wasanni da karawar da Real Madrid ke karbar bakuncin Real Mallorca da sanar da ku wainar da ake toyawa a fanni wasanni.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Liverpool ta ya canji

  2. An koma zagaye na biyu - Real Madrid 1-0 Mallorca

  3. An je hutu - Real Madrid 1-0 Mallorca

  4. Ra'ayinku ta BBC Hausa Twitter

  5. An ci kwallo - Liverpool 4-0 Crystal Palace, Sadio Mane

    Sadio Manene ya ci wa Liverpool kwallo na hudu, bayan da kungiyar ta je ta buga 0-0 a gidan Everton.

  6. Liverpool da Crystal Palace

    Za ku iya zaben dan wasan da ya fi taka rawar gani a karawa tsakanin Liverpool da Crystal Palace Latsa nan

  7. Martial ya ci wa United kwallo uku rigis a karon farko

    Anthony Martial ya ci wa Manchester United kwallo uku rigis a karon farko gasar Premier League, kuma karon farko da United ta doke Sheffield a Old Trafoord tun bayan shekara bakawi.

    Robin van Persie ne na karshe da ya ci wa United kwallo uku igis a gasar Premier League.

  8. Katin gargadi - Real Madrid 1-0 Mallorca

    An bai wa kyaftin din Madrid, Sergio Ramos bayan da ya yar da Ante Budimir zuwa kasa.

  9. Real Madrid 1-0 Mallorca

    An bayar da lokacin asha ruwa a dan huta.

  10. Real Madrid 1-0 Mallorca

    Madrid ta buga kwallo sau tara kuma uku ne suka nufi raga kai tsaye.

    Masu tsaron raga su ne da karancin taba tamaula a wasan nan kawo yanzu.

  11. Real Madrid 1-0 Mallorca

    Real ta kara samun dama inda Eden Hazard ya samu kwallo ya kuma shiga da ita gidan Mallorca ya kuma buga amma ta yi fadi.

  12. An ci kwallo - Liverpool 3-0 Crystal Palace, Fabinho

    Liverpool ta kara kwallo na uku a ragar Palace da zarar an ci Manchester City ranar Alhamis a Stamford Bridge za a bai wa Liverpool kofin Premier League na bana na kuma farko tun bayan shekara 30.

  13. An ci kwallo - Atalanta 1-2 Lazio

    Atlanta ta zare kwallo daya daga biyun da aka zura mata a gasar Serie A.

  14. Rafael Varane na buga wa Real wasa na 200

  15. Real Madrid 1-0 Mallorca

    Vinicius Jr da gaske yake a wasan nan. Karim Benzema ne ya bashi kwallo inda ya daga ta ta kuma yi kyau sosai amma ta bugi turke da tuni ya zura kwallo na biyu a wasan.

    .

  16. Liverpool 2-0 Crystal Palace

  17. An ci kwallo - GOAL - Real Madrid 1-0 Mallorca, Vinicius Jr

    Kwallo mai kyau da aka ci a raga, bayan da Luca Modric ya bai wa dan wasan har Gareth Bale zai dauka amma sai ya bar wa Vinicius wanda ya daga kwallo ta fada ragar Mallorca.

  18. Real Madrid 0-0 Mallorca

    Kdan ya rage a ci kwallo mai kyau bayan da Mallorca ta samu dama ta hannun Iddrisu Baba ya buga kwallo daga yadi na 25.

    DSai a Thibaut Courtois ya mike hannunsa kafin ya samu kwallon.

  19. Katin gargadi - Real Madrid 0-0 Mallorca

    Dan wasan Mallorca Ante Budimir ya samu kati mai ruwan dorawa bayan da ya yi wa Raphael Varane gula a fuska.

  20. Ra'ayin da kuke aikowa ta BBC Hausa Twitter