Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Barcelona ta dare kan teburin gasar La Liga

Wannan shafi ne kai tsaye da ke dauke da labarin wasa a gasar La Liga tsakanin Barcelona da Athletic Bilbao da wasu labaran wasanni da suke gudana ranar Talata.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Ra'ayinku a BBC Hausa Twitter

  2. Barcelona da Athletic Bilbao

  3. Athletic Bilbao

    Tana kaka ta biyu karkashin koci Gaizka Garitano mutumin da ya fitar da Barca a Copa del Rey a watan GFabrairu.

    Athletic ta kai wasan karshe a gasar da za ta buga da Real Sociedad karawar hamayya, sai dai bullar cutar korona ta sa aka dakatar da buga wasan karshen.

    Sai dai kuma Athletic ta yi rashin nasara a wasa hudu da ta buga a La Liga a cikin watan Fabrairu.amma ta yi biyar tun daga nan ba a doke ta ba, hakan ya sa take ta tara a kan teburi tana kuma neman gurbin shiga gasar Europa League a badi.

    Sakamakon wasa biyar da ta buga baya a La LigaAthletic 1-0 VillarrealValladolid 1-4 AthleticAthletic 1-1 Atlético MadridEibar 2-2 AthleticAthletic 1-0 Real Betis

    Wadanda ke kan gaba a ci mata kwallaye a Lik da sauran wasanni sun hada da Raúl García(10);Iñaki Williams(9);Iker Muniain(6);Yuri Berchiche(6)

  4. Masu rauni a Barcelona

    Wadanda ke jinya a Barca sun hada da Frenkie de Jong da Ousmane Dembélé da kuma Sergi Roberto.

    Sai dai kuma Samuel Umtitiis ya kammala hukuncin dakatar da shi da aka yi.

  5. Haduwa da suka yi a tsakaninsu

    Barcelona ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gidan Bilbao kuma sun yi haduwa uku ba tare da Barca ta zura kwallo a ragarta ba.

    Duk wasanni ukun ba a Camp Nou aka yi ba, kuma Bilbao ta kawo karshen wasa 14 ana doke ta a jere a Camp Nou a La Liga.

    Sai dai duk da kokarin da Bilbao ke yi a wasa da Barca rabon da ta yi nasara a Camp Nou tun 2001.

    Wasa biyar baya da suka kara:

    06/02/20 (CUP) Athletic 1-0 FC Barcelona16/08/19 (LIGA) Athletic 1-0 FC Barcelona10/02/19 (LIGA) Athletic 0-0 FC Barcelona29/09/18 (LIGA) FC Barcelona 1-1 Athletic18/03/18 (LIGA) FC Barcelona 2-0 Athletic

  6. Wadanda za su buga wa Barcelona wasa

  7. Barcelona da Ahletic Bilbao

  8. Ra'ayinku da kuke aikowa ta Twitter a BBC Hausa

  9. Barcelona tana da jan aiki a gabanta

    Barcelona za ta buga wasa a Camp Nou ba 'yan kallo a karawa mai zafi da Athletic Club, bayan 0-0 da ta buga da Sevilla a gasar La Liga.

    Tuni dai Real Madrid ta ci Real Sociedad ta kuma koma ta daya a kan teburi duk da maki iri daya 65 da kowacce keda shi, amma nasara da Real ta yi a El Clasico ya sa ta dare kan teburi.

    Saboda haka Barcelona na bukatar makin nan ta sake hawa kan teburi kafin Madrid ta buga wasa da Real Mallorca ranar Laraba.

  10. Barcelona da Athletic Bilbao

  11. Jama'a barkanmu da saduwa cikin shirin labarain wasanni kai tsaye a karawa tsakanin Barcelona da Athleic Bilbao a gasar La Liga.

    Za ku iya bayar da gudunmuwarku ko tafka muhara a BBC Hausa Facebook ko kuma ta Twitter,

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper zan kasance tare da ku.