Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Barcelona ta dare kan teburin gasar La Liga

Wannan shafi ne kai tsaye da ke dauke da labarin wasa a gasar La Liga tsakanin Barcelona da Athletic Bilbao da wasu labaran wasanni da suke gudana ranar Talata.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    An ci gaba da wasa.

  2. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Ana dan shan ruwa domin akwai zafi a Barcelona ya kai 24C dan lokaci kenan da alaklin wasa ya bayar.

  3. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Lionel Messiya sa kwallo mai kyau zuwa ga Luis Suarez wanda ya yi kokari ya fito da ita amma ta yi wajen fili.

  4. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Wannan ne wasa na 150 a jere da Inaki Williams ke buga wa a La Liga tare da Athletic.

    Rabon da bai buga La Liga ba tun 2016.

    Ya yi motsi mai kyau inda Inigo Lekue ya sa masa kwallo amma bai samu ba.

  5. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Athletic ta dauko kwana daga bangaren hagu. Sun kuma buga dan dan kadan amma ta je wajen Yeray Álvarez ya sa kai amma ta yi saman raga.

  6. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Luis Suarez ya yi bani in baka da shi da Lionel Messi amma nan da nan mai tsaron ragar Athletic Unai Simon ya yi sauri ya fito ya kama kwallon da Suraez ya hau kanta komai zai iya faruwa.

  7. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    An kai hare-hare bakawi kawo yanzu wato 4-3 inda na Barcelona biyu suka nufi raga, ita ma Athletic na ta biyu sun nufi ragar.

  8. arcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Dan kwallon Athleti, Inaki Williams yana da kyau. Ya yi gudu ya samu kwallo yana zuwa ya maka ta zuwa ragar Barcelona amma ta bugi bayan raga ba wani hadari, kuma Marc-Andre ter Stegen bai tashi hankalinsa ba.

  9. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Barcelona na neman yin sakaci - dan asan Athletic, Mikel Balenziaga ya buga kwallo daga yadi na 30 zuwa ragar Barcelona amma ta yi fadi da yawa.

  10. Yan wasa uku ke amsa Unai da biyu da ake kira Inigo a Athletic a wannan wasan.

  11. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Lionel Messi yana cikin annashuwa - Ya ja kwallo ya fice daga cikin masu tsaron baya ya kuma yi kokarin ya daga kwallo ta haura mai tsaron raga amma ba wata matsala.

  12. Barcelona ta yi rashin nasara a wasa daya kacal daga 70 da ta buga a La Liga a gidanta, shi ne 4-3 da ta tashi da Real Betis ranar 11 ga watan Nuwambar 2018.

    Sun ci 14 da canjaras daya a karawa 14 a bana, illa rashin nasara a El Clasico.

  13. Barcelona 0-0 Atheleico Bilbao

    Barcelona na samun damarmaki. Luis Suarez ya yi kokari ya buga kwallo amma mai tsaron baya ya tare ta amma ta je wajen Sergio Busquets wanda ya buga daga yadi na 20 amma an tare kwallon. whose 20-yarder

  14. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Barcelona ta ja kwallo zuwa gidan Athletico sai dai Luis Suarez ya yi iya kokarinsa ya tadda kwallon amma hakan bai yi wu ba.

  15. An take leda Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

  16. Messi na neman kwallo daya ya cika 700 da ya ci, Barcelona v Athletic Bilbao

    Lionel Messi ya ci kwallo 699 a sana'arsa ta kwallon kafa inda guda 629 ya zura a Barca da 70 da ya ci wa tawgar Argentina.

    Ya zura wa Athletic kwallo 10 ya bayar da hudu aka zura a raga a karawar da ya yi da kungiyar.

  17. Barcelona da Athletic Bilbao

  18. Wadanda za u buga karawar

    Barcelona ta yi canjin 'yan wasa biyu kan yadda ta fuskanci Sevilla a karawar da ta tashi ba ci.

    Ta saka Arthur da kuma Antoine Griezmann wadanda suka maye gurbin Ivan Rakitic da kuma Martin Braithwaite..

  19. Barcelona v Athletic Bilbao

    Sau biyu Athletic Bilbao na cin Barcelona a bana da ya hada da wasan farko a La Liga da kuma a Copa del Rey karawar daf da na kusa da na karshe.

    Rabonda Barca ta doke Athletic tun cikin Maris din 2018.

    Ita kuwa Athletic ba ta ci wasa a Camp Nou ba tun 2001.

  20. Yadda teburi yake kawo yanzu