Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Barcelona ta dare kan teburin gasar La Liga

Wannan shafi ne kai tsaye da ke dauke da labarin wasa a gasar La Liga tsakanin Barcelona da Athletic Bilbao da wasu labaran wasanni da suke gudana ranar Talata.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Canji - Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Canji biyu da Barcelona za ta yi Ansu Fati da kuma Ivan Rakitic sun maye gurbin Sergio Busquets da kuma Antoine Griezmann.

    Barcelona na neman maki ukun nan ido rufe..

  2. Katin gargadi - Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Barcelona ta samu bugun tazara, bayan da Unai Nunez ya kama kwallon da Luis Suarez ya buga, an kuma ba shi katin gargadi wato mai ruwan dorawa.

  3. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Kwallo daya ce aka buga ta nufi raga tun da aka koma zagaye na biyu ita ce wadda Antoine Griezmann. Amma har yanzu shiru kake ji.

  4. Canji - Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Athleti za ta yi canji biyu a tare inda Iker Muniain da Dani Garcia za su maye gurbin Unai Lopez da kuma Inigo Cordoba.

  5. Canji - Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Barcelona ta sa matashi mai shekara 20mai buga tsakiya, Riqui Puig ya maye gurbin Arthur, wanda ake alakanta shi da cewar zai koma Juventus.

  6. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Antoine Griezmann ne ya samu kwallo a cikin da'ira ta 18 kawai sai golan Athleic Unai Simon ya yi kokari ya tare kwallon da ya buga masa.

  7. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Kwallo mai kyau da Barcelona ta raba sai dai Arturo Vidal ya sa ta yi sanyi hi bai bayar ba bai buga ta zuwa raga ba hakan ya yayyafa ruwan sanyi a zafin da aka taho da kwallon.

  8. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Har yanzu wasan bai dauki zafi ba tun da suka sha ruwa suka dawo zagaye na biyu. Kowa wasan yana da mahimmaci a wajensa.

  9. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Antoine Griezmann ya yi kokarin bai wa Luis Suarez kwallo amma dan wasan Athletic ya karbe ya kuma ja a guje.

  10. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    An tsayar da wasa alkalin wasa zai daure igiyar takalminsa.Ba zan iya tuna ko na taba ganin haka a tamaula.

  11. An koma zagaye na biyu - Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    An sa wasa zagaye na biyu ko Barcelona za ta samu maki uku kuwa. Kar ku manta Real ce ta daya a kan teburi za ta buga wasa ranar Laraba da Real Mallaroca.

  12. An hura hutu - Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

  13. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Antoine Griezmann ya yi kokarin bai wa Lionel Messi kwallo nan da nan alakalin wasa ya shiga ya ba ta wasan.

  14. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Ana takaddamar jifa sai alkalin wasa ya hura usur.

  15. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    An kara minti biyu ko Barcelona za ta amfana a wannan karon?

  16. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Lionel Messi ya maka kwallo daga yadi na 22 amma ta yi sama ta fita waje.

    Watakila sai an dawo daga hutu zai bude wuta Barcelona na bukatar maki uku a wasan nan Athletic na tare gida domin tana son zuwa Europa League a badi.

  17. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Dan ruwan da 'yan wasa suka sha ya sa musu kasala ba a kazar-kazar kafin su dan huta.

  18. Yadda kungiyoyin ke murza Leda

  19. Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    Barcelona ta samu kwana kuma Messi ne ya bugo amma Inaki Williams ya sa kai ta yi waje ba wani hadari.

  20. Katin gargadi - Barcelona 0-0 Athletic Bilbao

    An bai wa dan kwallon Barcelona katin gargadi wato Sergio Busquets bayan da ya yi wa Inaki Williams keta hakan na nufin ba zai buga karawar da Barcelona za ta yi da Celta Vigo ranar Asabar ba.