Bayern Munich 1-1 Monchengladbach
Dama mai kyau da Bayern ta samu.!
Joshua Kimmich ne ya buga kwallo zuwa wajen Benjamin Pavard wanda ya sa kai amma kwallo ya yi waje.
Wannan shafi ne da zai ke zuwar muku da labarin wasanni kai tsaye kan gasar Bundesliga karawar mako na 31 da sauran labarin wasanni da ke gudana a sassan duniya.
Mohammed Abdu
Dama mai kyau da Bayern ta samu.!
Joshua Kimmich ne ya buga kwallo zuwa wajen Benjamin Pavard wanda ya sa kai amma kwallo ya yi waje.
Bayern ta ci kwallo 90 daga wasa 30 a kakar bana it ace kan gaba a yawan sharara kwallaye bayan wasa 30 a tarhin Bundesliga.

Asalin hoton, Getty Images
Bayern za ta saka 'yan wasa biyu a jere..
Alphonso Davies zai maye gurbin Lucas Hernandez yayin da Kingsley Coman ya maye gurbin Mickael Cuisance.
Ko wadannan canji za su bai wa Munich damar hada maki kuwa?
Monchengladbach ce kan gaba a rike kwallo kuma ita ke kai hare-hare masu zafi.
Ba kasafai ake sa Bayern matsi a cikin wasannin da take buga wa a gida ba.
Wannan wasan yana daga daya daga cikin manya da za a ke sa ran kece raini.
Da akwai wasan Real Mallorca da Barcelona da na kofin kalubalen Italiya karawar daf da karshe.
Idan baku manta ba Thomas Muller da Robert Lewandowski ba sa buga karawar bayan da aka yi musu hukuncin dakatarwa wasa daya.
Monchengladbach ta kara samun dama daga wajen Patrick Herrmann ya buga kwallo amma kuma Manuel Neuer ya hana kwallo ya shiga raga..
Monchengladbach ta ci gaba da sa matsi inda ta tsaya wannan karon ta bangaren hagu ta bugo kwallo amma golan Bayern ya sa kafa ya hana ta yi tasiri.
Baki ne za suyi canji inda mai tsaron raga Tony Jantschke ya maye gurbin Nico Elvedi.
Gladbach ta yi canji na biyu kenan bayan Thuram tana da saura uku a nan gaba.
An koma wasa zagaye na biyu a yanzu kowa yana da maki daidai kenan.
Za a buga minti 45 nan gaba
Benjamin Pavard shi ne dan kasar Faransa na farko da ya ci gida sau biyu a tarihin Bundesliga.
Ta farkon ma a karawa ce da Monchengladbach.
A yanzu a wannan sakamakon Bayern tana da maki biyar tsakaninta da Dortmund kuma saura wasa uku-uku a karkare Bundesliga ta shekarar nan.
Bayern Munich tana da jan aiki a gabanta a wasannan idan har tana son ta yi abun kirki in ba haka ba Monchengladbach wadda ke harin gurbin Champions League a badi za ta iya samun maki uku a karawar.
Ana ta yin kura-kure a fili kuma wannan karon Monchengladbac ta amfana bayan da dan wasanta Patrick Herrmann sai ta bugi kafar Benjamin Pavardgets ta fada ragar Munich.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Lucas Hernandez ya fadi kasa sai da ya yi kara.
Kawo yanzu Bayern na kara matsi ta kuma samu damar haka tun bayan da Gladbach ta fitar da Thuram wanda ya yi rauni.
Shekarar Joshua Zirkzee 19 kuma kwallo na uku da ya ci wa Bayern a kakar bana.
Bayern ta zura kwallo a raga duk da kokarin da gola Yann Sommer ya yi.
Golan na Mochengladbach ya samu kwallo daga Matthias Ginter wanda ya yi kokari ya mayar masa sai kawai Joshua Zirkzeeto ya tsinci dami a kala ya kuma zura a raga.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Bayern ba ta kai wasu hare-hare ba, sai dai golan Monchengladbach, Yann Sommer ya yi kokari da ya tare kwallon da Lucas Hernandez ya buga masa kuma dama ce mai kyau.
Hari mai kyau da Munich ta yi wadda Monchengladbach keta kai mata hare-hare tun da aka take wasa.
Jonas Hoffmanhas ne ya zura kwallo a ragar Munich, sai dai kuma ba a karbi kwallon da tsohon dan wasan Borussia Dortmund ya ci ba saboda an ce ya yi satar gida.
Bayern sai ta lkara kula kenan komai zai iya faruwa.