Messi ya ci wa Barcelona kwallo na hudu

Wannan shafi ne da zai ke zuwar muku da labarin wasanni kai tsaye kan gasar Bundesliga karawar mako na 31 da sauran labarin wasanni da ke gudana a sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Kwallo na biyu - Mallorca 0-2 Barcelona, Martin Braithwaite

    Kwallon farko da Martin ya ci wa Barcelona

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  2. Mallorca 0-1 Barcelona

    Minti 10 da fara wasan Barcelona ke rike da kwallo amma Mallorca na sa matsi inda Dani Rodriguez zai iya zama hadari.

  3. Mallorca 0-1 Barcelona

    Sergi Roberto na taka rawar gani a gefen hagu babu mai tare shi sai yadda yaga dama yake yi da tamaula.

  4. Mallorca 0-1 Barcelona

    Mallorca ta samu dama mai kyau da ya kamata ta farke kwallo inda Takefusa Kubo mai buga wasa aro daga Real Madrid ya nemi mai tsaron ragar Barcelona shi kuma ya ture kwallon ta yi wajen fili.

  5. Mallorca 0-1 Barcelona

    Yadda magoya bayan Barcelona ke bibiyar karawa da Mallorca.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Mallorca 0-1 Barcelona

    Messi ya zame amma kwallon ta je wajen De Jong,shi kuma ya tura wa Roberto ya ja ta a jefen fili .

    Nan da nan ya bugo ta zuwa wajen Griezmann shi kuwa bai amfana da kwallon ba.

  7. Mallorca 0-1 Barcelona

    Barcelona ta fara da karfinta sai hare -hare take kai wa tasan da tazarar maki biyu ne kacal tsakaninta da Real Madrid wadda za ta fafata da Eibar ranar Lahadi.

  8. Mallorca 0-1 Barcelona

    Mallorca za ta iya barin 'yan ukun karshen teburi idan za ta doke Barcelona.

  9. An ci kwallo - Mallorca 0-1 Barcelona, Arturo Vidal

    Kasa da dakika daya Barcelona ta ci kwallo, kuma Jordi Alba ne daga gefen fili ya bugo kwallo kai tsaye ta je daidai kan Arturo Vidal shi kuwa bai jira ba ya sa kai ta fada raga.

  10. Bayanan bidiyo, Sarki Junior - Mai Barcelona
  11. An sa wasa Mallorca 0-0 Barcelona

  12. Mallorca da Barcelona

    Lionel Messi ya zama sabon mutum ya yi aski ya kuma yi gyaran fuska kamar ba shi ba.

  13. Napoli 1-1 Inter Milan Mertens ya kafa tarihi

    Dries Mertens ya zama dan kwallon Napoli da ke kan gaba a cin kwallaye a tarhin kungiyar mai 122.

    Dan wasan mai shekara 33 yana kungiyar tun kakar 2013.

    .

  14. Mallorca v Barcelona

    'Yan wasa da alakalai da jami'ai sun fito don buga daya daga wasan La Liga na karshe a ranar Asabar.

    Za a fafata ne ba tare da 'yan kallo ba.

  15. Goman karshe a kan teburin La Liga

    Kai tsaye

    Asalin hoton, BBC Sport

  16. Wadanda ke kan gaba a teburin La Liga

    Kai tsaye

    Asalin hoton, BBC Sport

  17. Real Mallorca da Barcelona

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. Ko Barcelona za ta lashe kofin La Liga na bana?

    Bayanan bidiyo, Comrade Sani Solari - Mai goyon bayan Barcelona
  19. Mallorca v Barcelona

    Mai shekara 21 mai tsaron baya na Uruguay, Ronald Araújo zai buga wa Barcelona wasa na biyu idan anjima.

    Ya fara yi wa Barca a wasan da ta doke Sevilla 4-0 ranar 6 ga watan Oktoba.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Juventus ta kai wasan karshe a Copa Italiya

    Juventus ta kai wasan karshe a gasar cin kofin kalubale na Italiya, duk da tashi ba ci tsakaninta da AC Milan.

    Juventus mai rike da Copa Italiya 13 ta samu wannan damar bayan da tun 13 ga watan Fabrairu suka buga 1-1 a Turin a karawar da suka yi ba 'yan kallo.

    Cristiano Ronaldo ya barar da fenariti a wasan.

    Juventus za ta fafata a wasan karshe ranar Laraba tsakanin wadda ta yi nasara a wasam Inter Milan da Napoli.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, AFP