Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Messi ya ci wa Barcelona kwallo na hudu

Wannan shafi ne da zai ke zuwar muku da labarin wasanni kai tsaye kan gasar Bundesliga karawar mako na 31 da sauran labarin wasanni da ke gudana a sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. An ci kwallo - Bayern Munich 0-1 Monchengladbach

  2. Za a yi canji - Bayern Munich 0-0 Monchengladbach

    Ya yi kokari ya ci gaba da wasan amma dole sai hakura Marcus Thuram ya yi daga karshe.

    Dan kasar Switzerland, Breel Embolo ne ya maye gurbinsa.

    Wannan babbar koma baya ce ga Monchengladbach domin Thuram yana taka rawar gani saura canji hudu ya ragewa kungiyar.

  3. Bayern Munich 0-0 Monchengladbach

    Jerome Boateng ne ya taka wa Marcus Thuram burki kan harin da yake kokarin kai wa Bayern wanda ya hana shi yin wani abin kirki.

    Thuram ya ji radadin shigar da Boateng ya yi masa da ana tunanin sai an duba shi amma ya mike ba wata matsalar zai ci gaba da wasan.

  4. Bayern Munich 0-0 Monchengladbach

    Thuram na buga wasan a matsayin mai cin kwallo ya kuma fara nuna kansa da abin da zai iya yi a wasan na yau.

    Monchengladbach na fatan a karshen kakar bana za ta samu gurbin shiga gasar Champions League ta badi.

  5. Bayern Munich 0-0 Monchengladbach

    Marcus Thuram ya kai kora dan wasan Monchengladbach amma an kwarfe shi tun kafin ya yi barna.

    An bayar da bugun tazara.

  6. An take kwallo - Bayern Munich 0-0 Monchengladbach

  7. Bayern na dafa da lashe Bundesliga na bana

    Bayern Munich za ta iya lashe kofin bana idan ta doke Monchengladbach koda yake nasarar da Borussia Dortmund ta yi a kan Fortuna Dusseldorf na nufin sai sun kara jira kan su lashe kofin bana.

    Bayern za ta iya lashe kofin Bundesliga na takwas a jere kafin Dortmund ta karbi bakuncin Mainz ranar Laraba.

    Bayern ta doke Monchengladbach ta kuma casa Werder Bremen ranar Talata nan take za ta karbi kofin Bundesliga na bana kuma na takwas a jere.

  8. Manyan wasanni uku da za a buga ranar Asabar

    Bundesliga karawar mako 31 - Bayern Munich da Borussia Monchengladbach

    Kofin kalubalen italiya - Napoli da Inter Milan

    La Liga wasan mako na 28 - Mallorca da Barcelona

  9. Wadanda za su buga wa Bayern wasa

  10. Za a ci gaba da gasar Premier ranar 17 ga watan Yuni

    'Yan wasan Premier League za su saka riga mai dauke da rubutun Black Lives Matter a wasa 12 da za a ci gaba da gasar cin kofin bana.

    Haka kuma mahukunta sun amince dan kwallo zai iya sa gwiwarsa kasa kafin wasa ko anan cikin yi ko idan an tashi a lokacin Premier League.

    Wannan na daga cikin goyon bayan masu zanga-zanga kan kashe George Floyd a Amurka.

  11. Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Bundesliga

    • Robert Lewandowski Bayern Munich 30
    • Timo Werner RB Leipzig 25
    • Jadon Sancho Borussia Dortmund 17
    • Wout Weghorst Wolfsburg 14
    • Rouwen Hennings Fortuna Dusseldorf 14
    • Jhon Cordoba FC Koln 13
    • Robin Quaison FSV Mainz 12
    • Sebastian Andersson FC Union Berlin 12
    • Serge Gnabry Bayern Munich 12
    • Kai Havertz Bayer 04 Leverkusen 11
    • Marco Reus Borussia Dortmund 11
    • Erling Haaland Borussia Dortmund 11
    • Florian Niederlechner FC Augsburg 11
  12. Wasa ne mai zafi da za a kara Bayern da Gladbach

  13. Sakamakon wasannin mako na 31 da aka buga Asabar

  14. Kocin Jamus na taka rawar gani a kakar bana

    Filck ya lashe wasa 23 daga 26 da ya fafata a matsayin kocin Bayern Munich ya kuma dara Pep Guardiola da wasa biyu a lokacin da ya ja ragamar kungiyar Jamus a wasa 26.

  15. Wadanda za su buga wa Gladbach wasa

  16. Lewandowski ba zai buga karawar ba

    Lewandowski ya ci kwallo 30 a gasar bana ya taimaka aka zura uku a raga.

    Müller ya taimaka an ci kwallo 20 a raga ya kuma ci bakawi da kansa sai dai ba za su buga wasan yau ba saboda dakatar da su da aka yi.

    A wasan Jamus na mako na 30 kowanne ya samu katin gargadi da ya sa ba su a fafatawa ta anjima.

  17. Sharhin wasan Bayern da M'Gladbach za mu kawo muku

    Za mu kawo muku sharhi da bayanan gasar Bundesliga a wasa tsakanin Bayern Munich da Borrusia Monchengladbach a daya daga fafatawar mako na 31.

    Bayern tana ta daya a kan teburin Bundesliga ita kuwa Gladbach tana ta hudu a kan teburi.

  18. Jama'a barkanmu da saduwa cikin shirin labarin wasanni kai tsaye da zan gabatar muku a wasan Bundesliga tsakanin Bayern Munich da Borrusia Monchengladbach da na La Liga tsakanin Real Mallorca da Barcelona.

    Za ku iya bayar da gudunmuwa ko tafka muhawara a BBC Hausa Facebbok ko a Twitter a BBC Hausa.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tw zan gabatar muku da shirin.