Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Messi ya ci wa Barcelona kwallo na hudu

Wannan shafi ne da zai ke zuwar muku da labarin wasanni kai tsaye kan gasar Bundesliga karawar mako na 31 da sauran labarin wasanni da ke gudana a sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. 'Yan wasan da za su buga wa Barcelona

  2. Sharhi kan wasan Real Mallorca da Barcelona

  3. Sakamakon wasannin La Liga da aka buga Asabar

  4. An ci gaba da gasar La Liga karawar mako na 28

  5. 'Yan wasan da za su buga wa Real Mallorca

  6. Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da wannan shafin.

    Idan anjima zan kawo muku fafatawar La Liga a wasa tsakanin Real Mallorca da Barcelona da fatan za ku tara idan anjima tun daga 8:00 na dare.

  7. Karashen wasannin mako na 31 ranar Lahadi

    FSV Mainz 05 da AugsburgMatch

    Schalke 04 da Bayer Leverkusen

  8. Bayer Munich 2-1 Monchengladbach

    Gladbach ta ci wasa uku daga biyar baya da suka fafata kan wasan yau,

  9. Bayern Munich 2-1 Monchengladbach

    Duk da karawar ba Robert Lewandowski da kuma Thomas Muller.

    Duk da haka Bayern ta doke Gladbach da ci 2-1 a wasan mako na 31.

    Leon Goretzka ne ya ci wa Munich kwallo na uku.

  10. An tashi wasa - Bayern Munich 2-1 Monchengladbach

    Idan har Bayern ta doke Werder Bremen ranar Talata za ta lashe kofin Bundesliga na bana kuma na takwas a jere.

  11. Bayern Munich 2-1 Monchengladbach

    Dole Monchengladbach ta ji takaici ganin duk kokarin da ta yi amma an kara mata kwallo na biyu kuma ita ce kan gaba a taka leda a gidan Munich.

  12. Bayern ta kara kwallo - Bayern Munich 2-1 Monchengladbach

  13. Bayern Munich 1-1 Monchengladbach

    Baki sun kara canji Breel Embolo, wanda ya maye gurbin Marcus Thurman an fitar da shi kuma Laszlo Benes ne ya maye gurbinsa.

  14. Saura minti 10 a tashi wasa

    Monchengladbach na saka kaimin ta tashi da maki daya a gidan Bayern.

    Amma dai ta kula da bayanta kar ayi mata sakiyar da ba ruwa daf da za a tashi wasa.

  15. Bayern Munich 1-1 Monchengladbach

    Matashin dan wasa Joshua Zirkzee zai ci gaba da tuna wasan nan zuwa lokaci mai tsawo ganin shi ne ya ci wa Bayern kwallon.

    Mai shekara 19 ya fita daga wasan, inda Kwasi Okyere Wriedt ya maye gurbinsa.

  16. Bayern Munich 1-1 Monchengladbach

    Wannan maki dayan idan har Monchengladbach ta samu a Bayern zai zama abin alfahari duk da raunin da Thuram ya ji a farkon wasa aka cire shi a karawar.

    Haka kuma fitatcen dan wasanta Alassane Plea baya buga wasan saboda dakatr da shi da aka yi..

  17. Bayern Munich 1-1 Monchengladbach

    Saura minti 15 a tashi daga wasan. Rabon da Bayern ta yar da maki a gasar Bundesliga tun ranar 9 ga watan Fabrairi.

    Tun daga lokacin kungiyar ta ci wasa tara a jere a gasar ta Bundesliga ta bana.

  18. Canji - Bayern Munich 1-1 Monchengladbach

    Patrick Herrmann ya yi wa Monchengladbach kokari a karawar nan, sai dai kuma an saka mai tsaron baya Oscar Wendt ya maye gurbinsa.

    Shi ko dai bakin so suke su sha da maki daya za su tsare gida ne?

  19. Har yanzu ana gaban Munich a rike kwallo

  20. Bayern Munich 1-1 Monchengladbach

    Canji da Bayern ta yi mai kyau ne domin tana sa kaimi kawo yanzu.

    Serge Gnabry ya buga kwallo ta nufi raga amma gola, Yann Sommer ya tare ta kuma yi waje.

    Kansa zai fashe da wannan kokarin da ya yi, bayan kuskuren da ya yi aka zura masa kwallo a raga.