Kwallo na biyu - Mallorca 0-2 Barcelona, Martin Braithwaite
Kwallon farko da Martin ya ci wa Barcelona
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da zai ke zuwar muku da labarin wasanni kai tsaye kan gasar Bundesliga karawar mako na 31 da sauran labarin wasanni da ke gudana a sassan duniya.
Mohammed Abdu
Kwallon farko da Martin ya ci wa Barcelona
Minti 10 da fara wasan Barcelona ke rike da kwallo amma Mallorca na sa matsi inda Dani Rodriguez zai iya zama hadari.
Sergi Roberto na taka rawar gani a gefen hagu babu mai tare shi sai yadda yaga dama yake yi da tamaula.
Mallorca ta samu dama mai kyau da ya kamata ta farke kwallo inda Takefusa Kubo mai buga wasa aro daga Real Madrid ya nemi mai tsaron ragar Barcelona shi kuma ya ture kwallon ta yi wajen fili.
Yadda magoya bayan Barcelona ke bibiyar karawa da Mallorca.
Messi ya zame amma kwallon ta je wajen De Jong,shi kuma ya tura wa Roberto ya ja ta a jefen fili .
Nan da nan ya bugo ta zuwa wajen Griezmann shi kuwa bai amfana da kwallon ba.
Barcelona ta fara da karfinta sai hare -hare take kai wa tasan da tazarar maki biyu ne kacal tsakaninta da Real Madrid wadda za ta fafata da Eibar ranar Lahadi.
Mallorca za ta iya barin 'yan ukun karshen teburi idan za ta doke Barcelona.
Kasa da dakika daya Barcelona ta ci kwallo, kuma Jordi Alba ne daga gefen fili ya bugo kwallo kai tsaye ta je daidai kan Arturo Vidal shi kuwa bai jira ba ya sa kai ta fada raga.
Lionel Messi ya zama sabon mutum ya yi aski ya kuma yi gyaran fuska kamar ba shi ba.
Dries Mertens ya zama dan kwallon Napoli da ke kan gaba a cin kwallaye a tarhin kungiyar mai 122.
Dan wasan mai shekara 33 yana kungiyar tun kakar 2013.
.
'Yan wasa da alakalai da jami'ai sun fito don buga daya daga wasan La Liga na karshe a ranar Asabar.
Za a fafata ne ba tare da 'yan kallo ba.
Mai shekara 21 mai tsaron baya na Uruguay, Ronald Araújo zai buga wa Barcelona wasa na biyu idan anjima.
Ya fara yi wa Barca a wasan da ta doke Sevilla 4-0 ranar 6 ga watan Oktoba.
Juventus ta kai wasan karshe a gasar cin kofin kalubale na Italiya, duk da tashi ba ci tsakaninta da AC Milan.
Juventus mai rike da Copa Italiya 13 ta samu wannan damar bayan da tun 13 ga watan Fabrairu suka buga 1-1 a Turin a karawar da suka yi ba 'yan kallo.
Cristiano Ronaldo ya barar da fenariti a wasan.
Juventus za ta fafata a wasan karshe ranar Laraba tsakanin wadda ta yi nasara a wasam Inter Milan da Napoli.