Bayern Munich ta ragargaji Leverkusen da ci 4-2

Wannan shafi ne da ke dauke da labarin wasanni da ke gudanar a karshen mako don sanar da ku irin wainar da ake toyawa kai tsaye.

Rahoto kai-tsaye

  1. An ci kwallo - Dusseldorf 1-2 Hoffenheim, Steven Zuber

  2. Canjin dan wasa - Leverkusen 1-3 Bayern

    Canji na hudu da Leverkusen za ta yi. Kungiyar na ta kokarin gani ta farke kwallo biyu da aka zura mata ko raba maki ne suyi.

    Julian Baumgartlinger ya canji Paulinho.

  3. Dokar canjin 'yan wasa biyar

    Kungiyoyi za su fara canja 'yan kwallo biyar a wasa amma na wucin gadi don kawo sauki wajen karkare kakar bana da zarar an ci gaba da wasanni kamar yadda Fifa ta bayar da shawara.

    Ana sa ran yin amfani da wannan shawarar na wucin gadi har zuwa karshen kakar 2020.

    Hukumar Fifa ta ce ba za a koma wasa kai tsaye ba har sai jami'an lafiya da gwamnatoci sun amince cewar komai ya koma yadda ya kamata.

    Cibiyar kungiyar kwallon kafa ta kasa ce wato Ifab keda alhakin amincewa da wannan shawarar da Fifa ta bayar.

    BBC ta fahimci cewar Ifab za ta amince da wannan shawarar saboda tun a baya an tattauna kan batun ta yadda za a taimaka wa 'yan kwallo da walwalar su.

    Yadda ake son gudanar da tsarin

    • A gasar da aka amince a sauya 'yan kwallo uku, za su iya saka biyar jumulla a lokacin wasa.
    • Za a yi amfani da tsarin canja 'yan wasa biyar kamar yadda ake yi a lokacin da ake sa uku da kuma lokacin hutu.
    • Watakila da yiwuwar saka dan wasa na shida bayan karin lokaci.
    • Za a ci gaba da wannan tsarin ga karawa tsakanin tawagar kasa da kasa har zuwa 31 ga watan Disambar 2020.
    Kai tsaye

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Canji - Leverkusen 1-3 Bayern

    Canji uku a lokaci daya da Leverkusen ta yi.

    Wendell ya maye gurbin Leon Bailey, Florian Wertz ya canji Karim Bellarabi sai kuma Kerem Demirbay da ya canji Nadiem Amiri.

  5. An koma zagaye na biyu

  6. Chelsea ta kulla yarjejeniyar daukar Werner

    Chelsea ta kulla yarjejeniya domin dauko dan wasan RB Leipzig Timo Werner.

    Rahotannisun ce za a sayar da dan wasan mai shekara 24, wanda ya ci kwallo 25 a gasar Bundesliga a kakar wasan da muke ciki, a kan £54m.

    Ana ta rade radin cewa dan wasan dan kasar Jamus zai koma Liverpool ya kuma ce yana alfahari da jin dadin alakanta shi da batun.

    Amma BBC Sport ta fahimci cewa Liverpool ba ta sha'awar sayen Werner, wanda ya ci wa tawagar Jamus kwallo 11 a wasa 29 da ya yi.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Leverkusen 1-3 Bayern

    Leverkusen ce ta fara cin kwallo daga baya aka farke aka kuma kara mata biyu.

    Saura minti 45 nan gaba da za su fafata, ai dai da jan aiki a gaban Leverkusen.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Sakamakon wasannin ranar Asabar

    Kai tsaye

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Hutun rabin lokaci - Leverkusen 1-3 Bayern

    Da alamai dai Bayern Munich za ta hada maki uku a wasan kuma saura minti 45 nan gaba.

    Watakila kwallayen su haura haka.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. An ci kwallo - Leverkusen 1-3 Bayern, Serge Gnabry

    Serge Gnabry ya ci wa Bayern kwallo na uku, kuma gudu ya yi mai kyau da kwallo ya kuma daga ta ama ta fada gidan kifi.

  11. An ci kwallo - Leverkusen 1-2 Bayern, Leon Goretzka

  12. Katin gargadi - Leverkusen 1-1 Bayern

    An bai wa Thomas Muller katin gargadi shima ba zai buga wa Munich wasa na gaba ba.

    Hakan na nufin a wasan Bayern Munich na gaba Muller da Lewandowski ba za su buga wasa na gaba ba.

  13. Katin gargadi - Leverkusen 1-1 Bayern

    Labari mara dadi ga Bayern da Lewandowski inda ya yi wani laifi da bai kamata ba a daf da tsakiyar filin wasa, inda rafli ya ba shi katin gargadi.

    Hakan na nufin ba zai buga wasan mako na 31 ba a gasar Bundesliga ta gaba.

  14. An ci kwallo - RB Leipzig 1-0 Paderborn, Patrik Schick

    RB Leipzig ta ci Paderborn kwallo, kuma Timo Werner yana da hannu a ciki, domin shi ne ya bugo wa Patrik Schickto shi kuma ya zura a raga cikin ruwan sanyi.

  15. An ci kwallo - Leverkusen 1-1 Bayern, Kingsley Coman

    Bayern ta ci gaba da saka matsi inda aka samu kuskure daga Leverkusen.

    Daga tsakiya ne Leon Goretzka ya zame kwallon ta bar wajensa shi kuwa Kingsley Comanand ya samu ya kuma zabi wurin da ya jefa ta a gidan kifi.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. An hana kwallo - Dusseldorf 1-1 Hoffenheim

    Wasa dai ya koma 1-1 bayan da aka hana kwallon da Rouwen Hennings ya ci na biyu, kuma VAR ce ta yanke hukuncin.

  17. An ci kwallo- Dusseldorf 2-1 Hoffenheim, Rouwen Hennings

    Rouwen Hennings ya kara samun dama ta biyu ya kuma ci wa Dusseldorf kwallo sune ke kan gaba a yanzu haka.

    Hakika wannan wasan na kallo ne kila a yi ruwan kwallaye.

  18. RB Leipzig 0-0 Paderborn

    Dan wasan da Chelsea ta amince ta dauka Timo Werner shi ne ya nuna wata bajinta daga bangaren hagu har ma ya bugo kwallo cikin da'irar Paderborn amma an fitar da ita babu wata matsala.

    Hakika magoya bayan Chelsea za su mori dan wasan.

  19. Frankfurt 0-0 Mainz

    Frankfurt na taka kwallo mai kayatarwa, sai dai kuma Almamy Toure ya nemi raga amma kwallon ta yi sama sosai.

  20. An ci tarar Sancho saboda yin aski ba tare da takunkumin kare fuska ba

    Hukumar kwallon kafar Jamus ta ci tarar dan wasan Borussia Dortmund Jadon Sancho bayan an gan shi a hoto ya yi sabon aski ba tare da amfani da takunkumin fuska ba.

    Kazalika an ci tarar takwaransa dan wasa mai shekara 20 Manuel Akanji.

    Hukumar kwallon kafar ta ce a fili take cewa sun "keta dokar tsafta da ta kariya daga kamuwa daga cutuka masu yaduwa".

    Dortmund ta kare matakin da 'yan wasan suka dauka, tana mai cewa basu keta dokokin kiwon lafiya da na kariya na Bundesliga ba.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, Getty Images