Wannan shafi ne da ke dauke da labarin wasanni da ke gudanar a karshen mako don sanar da ku irin wainar da ake toyawa kai tsaye.
Rahoto kai-tsaye
A nan na kawo karshen shirin da fatan za ku tara a mako mai zuwa.
Wannan annobar ta cutar korona na zuwa karshe bayan da ake sa ran ci gaba da gasar Premier League daga 17 ga watannan da kuma ta Serie A duk dai cikin watan Yuni.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW ke muku fatan alheri.
Cristiano Ronaldo ya zama biloniya
Dan kwallon Portugal, Cristiano Ronaldo ya kasance dan wasan kwallon kafa na farko a tarihi da ya samu fiye da dala biliyan daya kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.
Dan wasan Juventus din ya samu dala miliyan 650 a buga kwallon kafa, sannan ya samu sauran kudin wajen tallar hajoji.
Ronaldo ya zama dan wasa na uku da ya kai wannan matakin, inda ya shiga rukuninsu dan wasan Golf, Tiger Woods da kuma dan dambe Floyd Mayweather.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Tottenham ta karbo bashin fam miliyan 175 daga bankin Ingila
Tottenham ta karbo bashin fam miliyan 175 daga bankin Ingila, don shawo kan matsalar tattalin arziki da ake fuskanta saboda cutar korona.
Tottenham ta yi kiyasin cewar za ta rasa fam miliyan 200 idan aka ci gaba da buga Premier ba 'yan kallo a filinta mai cin mutum 62,303, an kuma soke wasu wasannin na da ban.
Kungiyar ta cancanci karbar bashin a gwamnatance don shawo kan matsin tattalin arziki da ake fuskanta, kuma za ta biya kudin ruwa na kaso 0.5 cikin 100.
Tottenham wadda ke buga gasar Champions League a bana tana mataki na takwas a kan teburin Premier League.
Ranar 17 ga watan Yuni za a ci gaba da gasar Premier ta bana da kwantan wasa biyu tsakanin Aston Villa da Sheffield da na Manchester City da Arsenal.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
An ci kwallo - Leverkusen 1-4 Bayern
Robert Lewandowski ne ya ci wa Bayern Munich kwallo na hudu kuma na 30 a kakar Bundesliga ta bana.
Ya kuma ci kwallon da kai, bayan da Leon Goretzka ya bugo masa ita
A karon farko an sauya 'yan wasa biyar a tarihin Bundesliga
Ranar Asabar aka ci gaba da wasannin gasar Bundesliga karawar mako na 26 ba tare da 'yan kallo ba.
Hukumar gudanar da gasar Jamus ta yi hakan ne don kaucewa yada cutar korona, inda ta dauki matakai da dama, bayan gwajin 'yan kwallo.
An fara ne da wasa shida a ranar ta Asabar, kuma karawar da ta ja hankalin masu bin harkokin kwallon kafa ita ce tsakanin Borussia Dortmund da Shalke 04.