Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Borussia Dortmund ta doke Wolfsburg 2-0

Wannan shafi na kawo muku labaran wasanni da rahotanni kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. A nan muka kawo kaershen shirin da fatan kun ji dadin shirin za ku tara a wani wasan nan gaba.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tw ke fatan asha ruwa lafiya, a kuma yi bukukuwan karamar sallah lafiya.

    Allah ya kawo mana karshen wannan annobar ta cutar kotrona.

    Sai anjimanku.

  2. Ranar Lahadi: Karashen wasannin mako na 27

    • Schalke 04 da FC Augsburg
    • FSV Mainz 05 da RB Leipzig
    • FC Koln da Fortuna Dusseldorf
  3. Saura wasa daya ya rage da za a buga ranar Asabar

    Bayern Munich da Eintracht Frankfurt

  4. Wolfsburg 0-2 Borussia Dortmund

    An tashi wasa Dortmund ta hada maki uku a wasan mako na 27.

  5. Asisat: 'Yar wasan Barcelona ta yi tsokaci kan Ramadana

    Tauraruwar 'yar kwallon Najeriya kuma ta ƙungiyar mata ta Barcelona, Asisat Oshoala ta bayyana abin da take ji game da kasancewar yau Juma'a a matsayin ranar azumin Ramadana 29.

    Kamar yadda kuke gani, Oshoala ta wallafa a Twitter cewa: "Na 29....#Ramadan".

  6. Za a samu kungiyoyin da za su fadi da hawa gasar Ingila ta bana

    An amince cewar za a samu kungiyoyin da za su fadi da wadanda za su hau gasa uku da ke kasan ta Premier League da zarar an kammala sauran wasannin da suka rage na 2019-20.

    An kuma amince za a buga wasannin cike gurbi, amma kar su haura kungiyoyi hudu.

    Hukumar ta English Football League ta ce ta samu kaso 51 cikin 100 daga kungiyoyin da ke buga ko Championship ko League One ko kuma League Two da suka amince a soke wasannin bana.

  7. An bai wa Felix Klaus jan kati, Wolfsburg 0-2 Borussia Dortmund

    An bai wa Felix Klaus jan kati nan take bayan da ya taka Manuel Akanji.

  8. Wolfsburg 0-2 Borussia Dortmund

  9. Wolfsburg 0-2 Borussia Dortmund, Achraf Hakimi

  10. Borussia Monchengladbach 1-2 Bayer Leverkusen

    Kai Havertz ya kara cin kwallo na biyu a wasan.

    Havertz ya yi kan-kan-kan da Klaus Fischer wajen cin kwallo 34 a gasar Bundesliga kafin ya cika shekara 21.

    Daga baya Fischer ya ci kwallo 268 a gasar Bundesliga kuma shi ne na biyu a yawan zura kwallo a raga a tarihin gasar.

  11. Borussia Monchengladbach 0-1 Bayer Leverkusen

  12. Wolfsburg 0-1 Borussia Dortmund

    Jadon Sancho ya shiga wasa saura minti 25 a tashi daga karawar.

  13. Kada da ake kira Saturn wanda ke raye tun yakin duniya na biyu ya mutu

    Kadar nan da ta tsira a lokacin yakin duniya na biyu a Berlin da ake kira da Satun wadda ake cewa ta Adolf Hitler ce ta mutu a gidan namun daji a Moscow.

    An bai wa gidan namun dajin Berlin Saturn a 1936, kwanaki kadan da aka haife shi a Amurka, ya kuma tsere daga gidan namun dajin a 1943 a lokacin da aka yi wa wajen ruwan bama-bamai.

  14. Olivier Giroud zai ci gaba da taka leda a Chelsea

    Latsa nan don ci gaba da karanta labarinDan wasan Chelsea da tawagar kwallon kafar Faransa, Olivier Giroud ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a kungiyar zuwa karshen kakar badi.

    Giroud ya buga wasan Premier League biyar a watan Janairu, yana kuma wata shida da suka rage kwantiraginsa ya kare a Chelsea.

  15. Wolfsburg 0-1 Borussia Dortmund

    Dortmund ta yi canji inda tsohon dan wasan Liverpool Emre Can ya canji Mats Hummels.

  16. Wolfsburg 0-1 Borussia Dortmund

    an koma zagaye na biyu

  17. Labarai da dumi-dumi, Mario Gotze zai bar Borussia Dortmund a karshen kakar bana

    Mario Gotze zai bar Borussia Dortmund a karshen kakar bana in ji daraktan wasannin kungiyar Michael Zorc says.

  18. Wolfsburg 0-1 Borussia Dortmund

    An yi hutu

  19. , Sakwanninku a BBC Hausa Facebook