Wolfsburg 0-1 Borussia Dortmund
Dan wasan Portugal da ya fi cin kwallaye a Bunmdesliga fiye da Raphaël Guerreiro wanda ke da takwas a raga a bana shi ne Hugo Almeida wanda ya taka rawar gani Werder Bremen.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku labaran wasanni da rahotanni kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Mohammed Abdu
Dan wasan Portugal da ya fi cin kwallaye a Bunmdesliga fiye da Raphaël Guerreiro wanda ke da takwas a raga a bana shi ne Hugo Almeida wanda ya taka rawar gani Werder Bremen.
Kai Havertz ya ci wa Leverkusen kwallo a gidan Monchengladbach a gaban hotunan magoya bayan kungiyar dubu 13,000 da aka ajiye a kan kujerun 'yan kallo.
Paderborn 1-1 Hoffenheim,
Shi kuwa Leonardo Bittencourt ya ci wa Werder Bremen a gidan Freiburg.
Karon farko an yi wani abu a wasan inda Dortmund ta zura kwallo a raga ulian Brandt yana daga cikin wanda ya fara wasan sai ya bai wa Achraf Hakimi shi kuma ya ja ta gefe ya bai wa Thorgan Hazard..
Daga nan ne aka buga kwallon ciki sai Erling Haaland ya so yin wani abu amma hakan bai yuwuba, sai kawai Raphael Guerreirois ya cin ci kwallon ya kuma zura ta a raga.
Wannan wasa babu wani armashi ba hare-hare babu wani salo a fili babu wani abu na shakatawa a wasan.
Jadon Sancho baya cikin wasan nan kuma wasu za su iya tambayar dalilin da ya sa Dortmund ba ta saka shi a karawar ba.
Dan kwallon ya yi jinya ne bai dade da komawa fagen wasa ba, sannan ranar Talata Dortmunda za ta kara da Bayern Munich, saboda haka ba za ta yi ganganci da wuri haka ba.
Hukumar kwallon kafar Italiya ta tsayar da ranar 1 ga watan Satumba don ci gaba da gasar Serie A ta bana, sannan a karkare kakar 2019-20 ranar 20 ga watan Agusta.
Cikin watan Maris aka dakatar da dukkan wasanni a kasar, saboda bullar cutar korona, amma yanzu hukumar na fatan karkare gasar mai mataki uku, wato Serie A da B da kuma C.
Lokaci da na kara ja kuma kawo yanzu babu wadda ta buga kwallo ta nufi raga, an fi yin wasan daga tsakiyar fili ko kuma daga gefe.
Dortmund ta ci gaba da rike kwallo da kai hare-hare, sai dai Wolfsburg ta tsare gida da kyau musamman daga tsakiya ba a ratsa ta cikin sauki.
Manchester United ta ce bullar cutar korona ta jawo mata hasarar fam miliyan 28 - tana kuma fargabar hasarar za ta fi haka nan gaba.
United ta sanar da kasuwancin da ta yi na zango na uku ranar Alhamis 30 ga watan Maris.Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin
Erling Haaland na taka rawar gani sai dai har yanzu bai kai wani hari na azo a gani ba kawo yanzu.
Firai Ministan Spaniya, Pedro Sanchez ya ce za a ci gaba da gasar La Liga ta bana daga ranar 8 ga watan Yuni.
Tun cikin watan Maris aka dakatar da wasanni saboda bullar cutar korona.
Barcelona ce ta daya a kan teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid
Paderborn: Zingerle - Dräger, Hünemeier (c), Schonlau, Collins - Vasiliadis, Gjasula, Holtmann - Pröger, Srbeny, Antwi-Adjei
Masu jiran kar ta kwana: Huth, Strohdiek, Ritter, Sabiri, Jans, Evans, Mamba, Zolinski, Jastrzembski
Koci: Steffen Baumgart
Hoffenheim: Baumann - Posch, Bicakcic, Hübner (c) - Kaderabek, Grillitsch, Rudy, Zuber, Skov - Baumgartner, Bebou
Masu jiran kar ta kwana: Pentke, Nordtveit, Bruun Larsen, Geiger, Dabbur, Samassekou, Akpoguma, Ribeiro, Beier
Koci: Alfred Schreuder
Freiburg: Schwolow - Schmid, Gulde, Koch, Günter - Sallai, Haberer, Höfler, Grifo - Höler - Petersen
Masu jiran ko ta kwana: Flekken, Leinhart, Schlotterbeck, Abrashi, Frantz, Borrello, Heintz, Kwon, Keitel
Koci: Christian Streich
Bremen: Pavlenka - Gebre Selassie, Veljkovic, Moisander (c), Friedl - M. Eggestein, Vogt, Klaassen - Bittencourt, Sargent, Rashica
Masu jiran ko ta kwana: Kapino, Lang, Osako, Selke, Langkamp, Bartels, Groß, Woltemade, Bargrede
Koci: Florian Kohfeldt
Wolfsburg: Casteels - Mbabu, Pongracic, Brooks, Roussillon - Schlager, Arnold - Steffen, Mehmedi - Weghorst, Ginczek
Masu jiran kota kwana: Pervan, Brekalo, Klaus, Horn, Marmoush, Knoche, Tisserand, Victor, Justvan
Koci: Oliver Glasner
Dortmund: Bürki - Piszczek, Hummels, Akanji - Hakimi, Dahoud, Delaney, Guerreiro - Hazard, Haaland, Brandt
Masu jiran kota kwana: Hitz, Sancho, Götze, Balerdi, Morey, Can, Schmelzer, Reyna, Raschl
Koci: Lucien Favre
Chelsea za ta bar N'Golo Kante ya kauracewa atisaye saboda fargabar kamuwa da cutar korona - ko da kuwa hakan na nufin ba zai buga wasa ba har karshen kakar bana.
Dan wasan tsakiyar na Faransa, mai shekara 29, ya koma yin takaitaccen atisaye ranar Talata a filin wasan kungiyar da ke Cobham.
Sai dai tuni ya yanke shawarar yin atisaye a gida, matakin da Chelsea ta amince da shi.
Borussia Mönchengladbach: Sommer, Lainer, Ginter, Elvedi, Bensebaini - Strobl, Neuhaus - Hofmann, Embolo, Thuram - Plea
Masu jiran ko ta kwana: Sippel, Kramer, Herrmann, Raffael, Stindl, Traore, Wendt, Benes, Jantschke
Koci: Marco Rose
Leverkusen: Hradecky. Bender, Dragovic, Tapsoba - Weiser, Aranguiz, Demirbay, Sinkgraven - Bellarabi, Havertz, Diaby
Masu jiran ko ta kwana: Özcan, Tah, Paulinho, Bailey, Amiri, Alario, Baumgartlinger, Wendell, Wirtz
Koci: Peter Bosz