Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Borussia Dortmund ta doke Wolfsburg 2-0
Wannan shafi na kawo muku labaran wasanni da rahotanni kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu
Jama'a barkanku da kasancewa a cikin labarin wasanni kai tsaye da za a ci gaba da gasar Bundesliga karawar mako na 27.
Za kuma mu dinga kawo muku wainar da ake toyawa a fagen wasanni a fadin duniya a karshen mako.
Za ku iya bayar da gudunmawa a lokacin da ake gabatar da shirin kai tsaye a bbchausa facebook ko ta twitter a bbchausa.
Sunana Mohammed Abdu Mamman skeeper zan kasance da ku a cikin shirin.