Satar gida, Barcelona 0-0 Real Madrid
Nélson Semedo ya yi satar gida bayan sun yi taba in taba da Suárez
Muna kawo maku wasan La Liga tsakanin Barcelona da Real Madrid kai-tsaye.
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Nélson Semedo ya yi satar gida bayan sun yi taba in taba da Suárez
Barcelona ka iya zarce Madrid a yawan nasarorin Clasico a La Liga a karon farko a tarihi idan har ta ci wasan na yau.
A yanzu kowaccensu ta yi nasara sau 72.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Daga Messi har Suárez sun bata a wasan.
Real Madrid ta kai hari biyu na ciu a jere kwarara.
Har yanzu wadannan ba su samu aikin yi ba kwallo kawai suke jira a sanya a raga. Sai dai wasan na nuni da Madrid ce kan gaba a rike kwallo.

Asalin hoton, EPA
An bai wa Rakitic katin gargadi bayan doke Isco da ya yi, wanda raga ya nufa da kwallo mai kyau da kan iya zama hadari.
Varane ya yi wa Jordi Alba keta a cikin yadi na 18 na Barca bayan an bugo masa wata kwallo a sama - ya yi tsalle ya saka mata kai amma bai dake ta da kyau ba.
Shi ne katin farko a wasan.
Madrid ba za ta bar Barcelona ta sake ba, kai kace a gidan Madrid ake wasan, Pique ne ke ta kokarin hana kwallon shiga.
Madrid ta kai wani mummunan hari na-ci, kwallon ma ta tafi raga amma Piqué ya ciro ta.
Madrid ta matsa da kai kora. yayin da mai horas da kungiyar Zidane ke tsaye cak domin ganin sakamako mai kyau.
Kyakkywan taba kwallo daga Madrid. wasan da alamun zai yi zafi anan gaba.
Barcelona na neman Finareti,alkalin wasa ya yi burus.
Mummunan hari na farko da Benzema ya kai, wanda kuma hari ne na-ci.
Barcelona ta rike kwallon tana tabawa a gida. Tana ta kokarin samun damar kai hari cikin ragar Madrid.
Golan Madrid Thibaut Courtois ya hana kwallo 19 shiga raga cikin 21 wadanda duk hare-hare ne na ci,
Saboda haka sai Barcelona ta zage damtse kafin ta zira masa kwallo a yau.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Barcelona ta fara kai kora, sai dai babu wani hadari ga mai tsaron raga Courtois
Real Madrid
Zinedine Zidane bai yi rashin nasara ba a wasa 4 da ya jagoranci Madrid a filin wasa na Camp Nou (ya ci 2, ya yi canjaras 2), kuma a yau zai iya zama kocin da ya fi yawan wasanni ba tare da rashin nasarar ba a tarihi da wasa biyar.
Kyaftin din Real Madrid zai zama dan awasan da ya fi kowa yawan buga wasan na Clasico da wasa 43, inda zai wuce Manolo Sanchís da Francisco Gento da Xavi hernandez masu wasa 42 kowannensu.
Barcelona
Luis Suarez zai iya zama dan wasa na uku da ya ci kwallo sama da 10 a wasan Clasico a La Liga a tarihi bayan Lionel Messi (18) da Cesar Rodriguez (12).
Sai dai Messi bai ci kwallo ba kuma bai bayar an ci ba a wasan Classico uku na baya-bayan nan a kowacce gasa. Messi bai taba yin wasa hudu ba ba tare da ci ko bayarwa a ci ba.
Yayin da ake shirye-shiryen Kirsimeti, a Sifaniya kuwa shirye-shiryen wanda zai haye saman teburin gasar La Liga ake yi, kuma hakan za ta faru ne a daren nan.
Barcelona ce za ta karbi bakuncin wasan, wanda zai zama wasa na 90 a tarihi a filin wasa na Camp Nou a La Liga.
Wasa 20 kacal Madrid ta ci a filin wasa na Camp Nou cikin 89 da aka buga, yayin da Barca ta ci 50 kuma aka yi canjaras sau 19.
A wasan Clasico 10 na baya-bayan nan a Camp Nou wasa 2 Madrid ta ci, inda Barca ta ci 5 sannan aka yi canjaras 3.
Masu bibiyarmu barkanku da daren wasan El Clasico na 144 a La Ligar Spain.